AMFANIN GWANDA!!!!
Gwanda tana da abubuwan da jiki yake buqata da dama, ga dai amfaninta ga fata nan mun fada, masamman ta wajen kiwon lafiya, yadda fatar za ta yi qarfi, lafiya da kyawun gani, gashin kai kuma ya yi santsi da qarfi, ba zai riqa kakkaba ba, namiji bai damu da sanqo kamar yadda mace ta dauke shi ba, don in ma bai da shi yana iya yin tal-kwabo ya fita da kan a haka, ita kuwa abin kunya ne koda kuwa a wajen gyaran gashi ne, a irin wannan matsayin Gwanda tana da rawar da take takawa ba 'yar qarama ba.
1) Hawan jini daya ne daga cikin cututtukan da suke gallabar dan adam, to Gwanda tana da Potassium mai dama, wanda shi kuma yakan taimamaka wajen daidaita jinin mai cutar, tare da barin qwaqwalwa a farke kowani lokaci.
2) Gwanda kan kyautata ganin mutum, in mutum zai iya cin yanka biyu a kullum, ganinsa zai iya zama haka ba tare da ya ragu don girman shekaru ba, wannan sabo da yawan sinadarin ne da ake zaton zai iya yin wannan aikin, bawai don ita Gwanda ce an san dole ta yi haka ba.
3) Gwanda kan taimaka wajen kyautata qwayoyin garkuwar jiki, don tana dauke da sinadarinnan na Beta Carotene wanda wannan yana daya daga cikin aikinsa.
4) Kumburi wanda ya bayyana da boyayye duk cututtuka ne da suke cutar da jikin dan adam, to Gwanda takan taimaka wajen hana kumburin kunne na dindindin ko sanyi ko zazzabin influenza.
5) Cutar zuciya ma kan yi illa, to Gwanda tana da sinadaran da suke taimakawa, tana da Nutrients mai yawa wadan da suke maganin rubabben Cholesterol, da haka sai ta yi maganin yuwuwar kamuwa da rashin bugawar zuciya, ko tsayuwar qwaqwalwa.
6) Sai kuma raunuka irin na jiki, Gwanda kan taimaka ta yadda rauni zai yi saurin hadewa ya warke, in aka yanka gwandar sai a shafe raunin da shi, a nan muna ba da shawarar cewa duk raunin da mutum zai yi, ya yi qoqarin samun likita don karbar allurar Tetanus, wannan kuma wata cuta ce mai kisa, wace take saurin shiga jikin dan adam da zarar ya yanka, ko ya soke ko kuma ya yi wani rauni, in har ba a yi maganinta da gaggawa ba to akwai yuwuwar za ta yi kisa, Gwanda ba ta da amfani a nan.
7) Wani lokaci akan sami qurarraji ko maruru, wadan da sukan yi ta damun mutum na tsawon lokaci, to a nan sai mutum ya sami gwandarsa ya nuqe ta, ya hada ta da kindurmo ya shafa a wurin da marurun yake gallabarsa har sai ya bushe, in Allah ya so za a ga bambanci cikin gaggawa.
8) Akwai kuma ciwon sukari, duk da cewa Gwanda tana da zaqi amma kuma tana taimakawa wajen sassauta matsalar, alal aqalla ba ta a cikin manyan 'ya'yan bishiyar da ake hana mai cutar ya ci ko ya sha.
9) Hanji masamman babban na qarshe wanda daga shi ba-haya yake fita waje, wanda ake kira a Turance Colon yakan kamu da cutar Cancer to Fibres din dake cikin Gwanda suna da qarfin da za su iya yin maganin wannan Cancer din kuma su ba hanjin kariya, banda wannan ita ma 'ya'yanta sukan taimaka wajen magance wasu matsalolin sabo da sinadaran dake cikinta, sai dai ita 'ya'yanta daci ne a su ba kamar sauran 'ya'yan bishiyar da muka ambato a baya ba, 'ya'yan suna dauke da Vitamins da sauran sinadaran da za su taimaka mata wajen ida nufi.
Ga wadan da suka yi shaye-shaye har ya wuce qima hantarsu ta lalace 'ya'yan Gwanda kan taimaka, in mutum yana shaye-shaye hantarsa kan tattare ne ta cure wuri guda, sai ta gaza yin aikinta kamar yadda ya dace, to 'ya'yan Gwanda kan janye cutar matuqar za a dena dibar barasar, sai mutum ya sami 'ya'yan gwanda busassu ya niqe su, ya riqa sha a cikin lemon tsami, zai riqa sha ne a kullum da tazarar lokaci kafin ya ci abinci, haka zai yi har zuwa wata guda cur, don gurbacewar ba ta fita lokaci daya kacal, da haka in sha Allahu sai za a ci nasara, sai dai in mutum ya koma dibar barasar wata qila ba zai jima a duniya ba.
Kamar dai yadda muke fadi ne a kullum, matsalolimmu shi ne in aka sami dan bishiya guda to cin qoshi za a masa, wanda hakan kuwa matsala ce ga jikin dan adam, babu ko shakka rashin cin wadannan albarkatun gonar jikkunammu sukan shiga wani yanayi wanda cuta qarama in ta cafki mutum sai ta kwantar da shi, to amma in aka ci sama da yadda jikin yake buqata nan ma wata matsalar ce ta masamman, sai mutum ya yi qoqarin daidaita abincinsa don kaucewa da na sani a cikin rayuwa, Allah ya ba kowa lafiya amin, sai mu tara gobe in sha Allah don jin matsalolin gwanda, kusan ta fi duk wata dan bishiya matsala
Duk da cewa Gwanda tana da dumbin amfanin da muka ambata a baya, sai dai ba ta rasa nata matsalolin na masamman, galibin wadannan matsalolin ba a iya magance su in ba an nisanci ci gaba da dibanta ba
1) Abu mafi sauqin fadi shi ne Gwanda ga mace mai ciki hatsari ce, don za ta iya haifar da barin cikin, tun ba yau ba a baya can ma matan da ba sa son ciki, ko don sabo da hanyar da ya zo, ko ba a buqatarsa sukan zubar da shi ta wajen yin amfani da Gwanda, i tabbas nunanniyar Gwanda ta fi zama daidai ga mace sama da danya, don danyar takan haifar da matsalolin mahaifa sabo da sinadarinnan nan na Latex, shi wannan sinadarin zai iya haifar da bari ko haihuwar da ba a shirya ba, ba ma wannan kadai ba zai yuwu dan a haifo shi da tawaya ko ma ya fito a mace.
2) In da za a lura tun farkon darasin muna kwadaitarwa ne da cewa a riqa taqaita kowani dan bishiya ne da ake son ci, don mutum bai san wanda sinadarin cikinsa in ya hadu da na jikinsa qila ya wahalar da shi ba, in aka lura wani zai ce maka in ya ci kaza dole kaza zai same shi, ba camfi ba ne, tsarin jikinsa din ne akwai wasu abubuwan da ba sa haduwa da dan bishiyar shi bai sani ba, Gwanda in aka sha ta da yawa za ta iya haifar da Carotene a cikin jini, samun Beta Carotene a Gwanda zai iya haifar da canjawar launin fatar.
3) Haka kuma za ta iya kawo matsala ga mutum a wajen numfashi, sabo da samuwar Enzyme a cikinta, 'yan matsalolin za su shafi: Matsala a wurin numfashi, munshari, numfashin ya riqa samun cisgiya wajen shiga ko wurin fita, Asthma da kuma mura, koda yake ana iya magance mura da lemon tsami, ko citta, hatta kindirmo yana iya magance mura, sabo da sinadarin Magnesium dake cikinsa, qila ma shi ya sa fulani duk da zaman jeji, da rashin cikakken kariya daga sanyi, amma ba su ne suka fi kowa kamuwa da muran ba.
4) Za ta iya haifar da tsakwankwanin qoda, domin Gwanda qwara daya tal tana da Vitamin C 60mg, wato sama da 300% na abin da malaman kiwon lafiya suke ba da shawara da shi a rana, shi kuwa Vitamin C yakan zama babbar garkuwa a jiki, ya ba da kariya daga cutar kansa, da hauhawar jini, ko ma jinin ya riqa gardama ta wurin nuna raguwa ko zamantuwa daidai, amma duk da haka yin overdose na Vitamin C zai iya zama Poising har ya qarisa zuwa tsakwankwanin qoda, dole mutum ya riqa sara yana duba bakin gatari.
5) Gwanda za ta iya wahalar da tumbi, wannan duk muna nufin ne in aka sha ta har ta wuce qima, wani in ya sa ta a gabansa sai ya ga iyakarta, tabbas tana haifar da matsala a tumbi, kamar radadin tumbi, kumburin ciki, tashin zuciya da koke-koken ciki na ba gaira ba dalili, su galibin irin wadannan 'ya'yan bishiyar akan dan ci su ne daidai gwargwado a tsakanin abinci guda biyu, ba lokacin cin abinci ko nan take bayansa ba, duk da ka ji matsala to lallai an wuce gona da iri a ciki.
6) Ba wai ciki ba hatta ga mai shayarwa, yana da matuqar amfani ta san halin da take ciki, don malamai sun sami sabani a ciki, a gabashin Asia likitoci sukan ba masu shayarwa shawarar shan Gwanda don samun nono ga yaro, a wasu qasashen kuma akan gargade su sabo da samun Enzymes a ciki, a taqaice wannan babu wata matsaya qwaqqwara dake nuna cewa a guje ta din, a nan muna ba da shawarar cewa a kusanci malaman lafiya don samun cikakkiyar shawara.
7) In ya kasance mutum yana fama da mummunar cuta kamar Asthma, ina ba da shawarar ya bi a hankali wajen dibar Gwanda, ni a ganina tunda akwai wasu 'ya'yan bishiyar ba ita ba gwara ma ya koma wata, wani lokacin akan sami wasu matsalolin ga wanda bai tafiya daidai da ita, kamar kumburi a baki, a fuska, qaiqayi a cancan cikin baki da maqogwaro, a qasan harshe da baki, jiri, ciwon kai, kururuwan ciki, matsalar numfashi, zafi wurin hadiya da radadin ciki.
8) Idan mutum ya zarce gona da iri wajen yin amfani da ganyen Gwanda ko 'ya'yanta ko ma ita kanta zai iya samun matsala wurin yin numfashi da qyar, wannan kam in har yanayin bai canza ba, to ba shakka an kama hanyar aukawa cikin matsala.
9) Ya zama dole ga wadan da suke fama da matsalolin zuciya sudan guji Gwanda, don za ta iya haifar musu da jinkiri wajen bugawar zuciya, ko tsarin bugawar kwata-kwata ya canza.
10) Wanda yake fama da zawo ya kamata ya guji gwanda, kamar yadda ya kamata ya nisanci sauran 'ya'yan bishiya.
11) Haka yaron da bai kai shekara daya ba bai dace mamansa ta tura masa gwanda ba, don kashinsa yana iya yin kauri ya sha wahala a ciki, ko ma ya yi fama da atini, don haka ina ba wa maishayarwa shawarar ganin likita kafin danta ya fara shan Gwanda.
Da wannan darasi na kawo qarshen 'ya'yan bishiya, mu hadu a ganyayyaki in sha Allah.
Zamu cigaba in sha Allah
0 Comments