Amfanin Gwanda A Fatar Jiki



 Amfanin Gwanda A Fatar Jiki

Gwanda na daya daga cikin ’ya’yan itatuwa da ke dauke da nau’ukan sinadaren da ke kara wa mutum lafiya. Yawan cinsa na taimakawa hanjin ciki wajen nika abinci a sawwake sannan yana taimakawa wajen gyara fatar jiki domin yana dauke da sinadaren bitamin A da C. Wadannan sinadaren na sanya sulbi da sheki da kuma hasken fata a fuska ko a jiki. A yau na kawo muku hanyoyin da za abi domin amfani da gwanda a fatar jiki.

• Idan fatar mutum ta kasance tana da gautsi walau a fuska ko a jiki, yana da kyau a nika gwanda sannan a zuba cokali daya na zuma sannan a shafa a inda ake da matsala na tsawon minti talatin kafin a wanke.

• Domin magance kurajen fuska, yana da kyau a kwaba gwanda sannan a zuba zuma cokali daya da kuma ruwan lemun tsami kadan a ciki sannan a shafa a inda kurajen ya feso na tsawon minti ashirin sannan a wanke, yana da kyau a ci gaba da yin hakan kamar sau biyu a rana na tsawon wata uku.

• Sulbin fata; A nika gwanda da gurji da kuma ayaba sannan a shafa a fata sai a bari ya bushe na tsawon minti talatin a kullum kafin a shiga wanka. Yin hakan na taimakawa wajen samin sulbin fata.

• Idan ramukan fito da gumi na mutum na da girma, hakan yakan janyo yawan cututtukar fata don haka sai a samo gwanda da ruwan kwai banda gunduwar sai a kwaba a rika shafawa a inda kurajen ta fito. Yin hakan na rage girman ramukan fitar gumi.


• Maikon fata: A sami gwanda sannan a nika da lemun zaki sannan a rika shafawa a fuska na tsawon minti ashirin zuwa ashirin da biyar kafin a wanke domin rage gumin fuska.

• Samin hasken fuska; A nika ko a kwaba gwanda da ruwan lemun tsami sai a rika shafawa a fuska na tsawon minti goma zuwa sha biyar kafin a wanke. Haka za a rika yi har na tsawon kwana biyar kafin a fara ganin canji.

Post a Comment

0 Comments