Alamun Tana Sonka Amma Tana Boyewa:
SHARE 🔔
#tsagayarmalamtonga
Ba duk mata bane suke iya bugun gaba su cewa namiji suna sonshi ba.
A dabi'a irin na mata duk irin son da take maka ba zata iya furta maka ba. Sai dai akwai wasu alamomin da mace idan tana sonka takan fito dasu a fili.
A darusan mu na baya mun kawo wasu daga cikinsu. Yanzu ma ga wasu alamomin da zaga gane mace tana sonka amma ta kasa furta maka.
1:Yawan Fara'a: Macen da take sonka taba iya boye farin cikinta a duk lokacin da kuka hadu.
Fara'a, murmushin sune kawai zaka ga suna bayyana a fuskanta. Sabanin mace idan bata ra'ayin ka.
2: Yawan Ambatarka: Mace idan tana sonka cikin kalamanta 10 dole sai ta ambaci sunanka koda kuwa misali zata bayar.
3: Kokarin Sanin Halin Da Kake Ciki: Duk irin yadda zaka boye rayuwarka macen da take sonka sai ta gano halin da kake ciki.
Bazata iya yin wuni gudaba ba tare da ta ji lafiyarka ba.
4: Dabi'un Ta: Duk yadda zata yi kokarin boyewa ta fatan baki, dabi'un mace mai sonka baya iya boyuwa musamman idan gaka gata.
Mace idan tana sonka kuna haduwa duk wanda zai lura sai ya fahimci akwai soyayya a tare da ita wajen yadda zata yi mu'amala da kai.
5: Yiwa Abokanta Zancenka: Mace idan tana sonka bata shakkar fadawa abokanta irin yadda take jinka a zuciyarta.
Irin wadannan mata akasari ta wajen kawayensu kake samun labarin soyayyar da suke maka.
6: Zaka Tayi Kokarin Dadada Maka: A duk inda ka hadu da mace mai sonka bazaku rabu ba sai ta tabbatar koda da kalmane ta dadada maka.
Ko da wasa kaga wani abu a tare da ita kana cewa ta baka zafa mika maka, sai dai idan daga baya ta maka bayanin nata ne ko kuma aikenta aka yi.
7: Kishi: Macen da take sonka koda wasa taga kana kula wasu matan sai ka ga fuskanta da alamun rashin jin dadi.
Macen dake sonka bata iya boye kishin da take yi akanka koda kuwa akan na kusa da ita ne.
8: Kwalliya: Macen dake sonka idan zaku hadu sai goma sai kaga tayi wani shigan da zata burgeka.
Macen datake sonka bata yarda ta hadu dakai har sai idan ta tabbatar taci kwalliyar da zaka yaba mata.
9: Rashin Mantuwa: Macen datake sonka bata manta duk wani magana da kukayi. Wasu hatta kalmar da kayi amfani da ita sai ta haddacesu.
Alamun gano mace tana sonka shine ta tabbatar maka bata manta wani bayani ko alkawarin da kuka yiwa juna ba.
10: Mace idan tana sonka duk wani kalmar da zaka furta mata farin ciki yake sakata.
Koda mara Fara'a ce kana mata Barkwanci zata tuntsire da dariya.
Wadannan wasu ne daga cikin dubannin alamomin da mace zata iya nuna maka tana sonka ba tare da ta furta maka kalmar so ba.
Maza sai a kula domin kada a yi sakaci da damar da aka samu.
0 Comments