Kinyi Dace Saurayi Idan Kika Samu Mai Miki Wadannan Abubuwan:
SHARE 🔔
#tsagayarmalamtonga
Ba duk 'yan mata ko mata suke dacen samari ba. Sai dai wacce tayi sa'ar samun saurayin da zai aureta mai mata wadannan abubuwan tabbas tayi dacen masoyi.
1: Mai Kiyaye Mutuncinki: Duk namijin da zai kiyaye mutunciki, baya neman muzantaki ta kowani yanayi. Kinyi dacen masoyi.
2: Yana Sauraronki: Alamun dacen masoyi shine ki samu wanda zai baki lokacin. Yana sauraranki, yana baki dama daya dace dake.
3: Baya Zarginki: Duk masoyin da baida da zargi, alamu ne na dacen samun mijin aure na gari.
4: Yana Girmamaki: Duk macen da ta samun namiji mai sonta yana girmamata, wannan tayi dacen mijin da zai aureta.
5: Yana Goyon Bayan Kudurorinki: Idan mai sonki Yana goyon bayan burinki da kudurorinki tabbas bakida matsala bayan kunyi aure.
6: Yana Alfahari Dake: Idan kin samu namiji mai alfahari dake a gaban mutane da bayansu, alamu me na kin yi dace manemi.
7: Yana Yaba Ki: Idan masoyinki yana yaba abubuwan alherin da kika masa, yana nuna godiyansa. Alamu ne na kinyi sa'a manemi.
8: Yana Son Ganin Farin Cikinki: Alamu ne na dacen mijin da zai aureki idan kika samu mai son aurenki da yake burin ganin ki cikin farin ciki ako yaushe.
9: Yana Nuna Miki Soyayya: Baya kunyar nunawa duniya yana sonki komai muninki, ko nakasarki.
Macen da mai sonta da aure yake nuna mata soyayya na zahiri, babu shakka ko bayan sunyi aure akwai alamun zata yi dace miji.
10: Yana Damuwa Da Lafiyarki Da Damuwarki: Duk mai sonki na gaskiya bai samun sukunin a duk lokacin da kike cikin wani yanayi na rashin lafiya ko jin dadi.
Da zaran kin fahimci wanda yace yana sonki bai damu da damuwarki ba. Ki hakura da aurensa.
Wadannan wasu daga cikin alamomin mace tayi dacen samun mijin aure na gari.
Da fatan Allah Ya baiwa mata masu burin yin aure mazan da suka dace dasu na gari.
0 Comments