YIN LALATA KAFIN AURE
Akwai wani abu da yake yaɗuwa YANZU a duniyar samari da ƴan mata ko bazawari da bazawara, na yin sharholiya da iskanci, da lalata tsakanin su kafin a yi aure, sai bayan an gama sheƙe aya wani lokacin har an yi ciki an zubar sai kuma kaga wai yanzu za a yi aure, to yaya aure zai yi ƙima yayi daraja bayan an gama shantakewa a waje? Yaya za a sami aminci da yarda da Amana tsakanin ma'auratan da suka yi sharholiya tsakanin juna kafin aure ? Yaya zargi ba zai yi yawa ba? Tunda kowa yasan abokin zaman sa fasiƙi ne kuma shima sheda ne akan haka?
Ida kika kuskura kika bari wani yasan mutunci a waje to tabbas ba zai ƙara ganin ki da ƙima ba har abada, kuma duk sanda kika fita unguwa sai ya zarge ki, domin yasan ki a waje baki da sauran mutunci a idon sa.
Kada ki kuskura wani ya kawo miki hannu zai taɓa ki kafin aure ko amince.
Kada ki kuskura wani ya gayyace ki wani gida ko shago ko bishi.
Kada ki kuskura wani ya baki abinci ko abin sha a wani guri ki karɓa ki ciki, domin ya iya kasancewa ya saka miki wani abu da zai bugar da ke ya ci lalata miki rayuwa.
AURE BAYAN ANYI LALATA.
Shin idan an yi zina za a iya aure daga baya.?
Asali abin da musulunci ya koyar duk wanda zai aure to ya nemi auren kamammiya mai tarbiyya ƴar gidan mutunci.
Haka mace ita ma ta auri kamamme mai tarbiyya ɗan gidan mutunci.
Musulunci ya hana aurar lalatattun mutane waɗanda suke cikin ganiyar lalata , kamar mazinata , masu neman maza , da yan madigo, ƴan ƙwaya da sauransu fasiƙai da fasiƙancinsu yake a fili sananne
Allah cewa ya yi : " Ku aure su da izinin waliyyansu a halin kasantuwarsu kamammu ba lalatattu ba ko masu riƙar abokin baɗala a ɓoye ba (ƴan dadiro) " Nisa'i
A wata ayar cikin Suratun Nur Allah ya bayyana cewa ya haramta aurar mazinaci da maznaciya kamar yadda ya haramta aurar mushrikai.
Ma'anar waɗannan ayoyi ita ce kada mutum kamamme ya je ya auri lalatacciya tana tsaka da lalatarta ba tare da tuba ta gyara halinta ta daina aikata lalatar ba.
Amma idan ta tuba ta gyara ta zama mutuniyar kirki to babu wani dalili da zai hana a aure ta matsawar akwai son juna da fahimtar juna.
Sai dai wani abu dake faruwa na matsala shi ne , aurar irin waɗannan mata dake aikata irin waɗannan laifuka da suka shafi mutuntaka , yakan zama matsala da abin gori koda kuwa sun tuba.
Wannan babbar matsala dake ciwa mutane da yawa tuwo a kwano. A musulunci ba a gori ko suka akan laifin da mutum ya tuba daga aikata shi.
Allah ya faɗa a cikin Suratul Furƙan cewa waɗanda suka tuba da shirka da zina da kisan kai , sannan suka zamo mutanen kirki , to haƙiƙa waɗannan zai musanya munanan ayyukansu izuwa kyawawa.
A taƙaice dai , duk macen da ta tuba ta gyara halayenta babu laifi a aure ta. Kuma goranta mata akan abin da wuce ba koyarwar musulunci ba ne.
Domin sau tari mu kan samu tambaya akan halaccin auren mazinaci ko mazinaciya .
Akan samu wasu sun tuba kuma su na son yin aure amma kowa sai ya ƙyama ce su. Ko kuma waliyyan ango ko amarya su hana yin auren. Wanda daga ƙarshe idan aka yi rashin sa a , su koma aikata baɗalarsu tunda kowa ya guje du.
Don haka sharuɗan da ake so cika wajen mazinaciya su ne guda biyu kamar haka :
1- A samu inganntaccen tuba na zaran bunu wanda babu alamar komawa daga gareta sannan a samu nadama.
2- A yi mata istibra’i da sikanin(scanning)- domin a tabbatar da cewa bata da ciki kuma zina da ta ke yi bai sa ta ɗauko cutar ƙanjamau ko wasu cututtuka da ke iya yaɗuwa ta hanyar jima’i wanda za ta iya sawa mijin ta da ta aura ba.
Idan an tabbatar da lafiyarta kuma bata da juna biyu sannan ta tuba, to mutum yana iya aurenta in yana buƙata.
Hana shima namijin a kiyayi auran mazinaci, sai an tsananta bincike,
0 Comments