Illolin da madigo ke haifarwa ga mace:



Illolin da madigo ke haifarwa ga mace:


Madigo: na nufin saduwa ta hanyar gogayya tsakanin macce da mace ta amfani da tsiraicinsu ko cikon halittun matancinsu don jin dadi ko kau da sha’awar junansu. Wasu kuma sun bayyana Madigo da cewa, hanya ce ta biya wa kai bukata da mata ke yi a tsakaninsu da mata ‘yan uwansu.

Hakika wannan halayya ta fi zina muni ga al’umma. Halayya ce da ko dabbobi ba sa yin ta.

 Wannan babbar masifa ce da ta shigo wa al’umma, take kuma habaka da ruruwa cikin al’ummar musulmi. A yanzu dai bincike ya nuna cewa a kan samu ‘yan mata daga shekaru goma zuwa sama da haka na aukawa cikin wannan harkar. 

Za a iya jefa madigo a nau’in cututtukan ruhi wanda shaidan ke fesa wa ‘yan Adam gubarsa. Kamar yadda wata ta gabatar da takardar ta a taron ?ara wa juna ilmi kan matsalolin al’umma musamman madigo ?in. Ta nuna cewa:

“Neman jinsi ya faro ne tun daga zamanin Annabi Lut (a.s) wanda ya zo a tarihi cewa Shaidan ne ya zo a siffar ‘yan Adam ya nuna wa mutanen Annabi Lut (a.s) yadda za su rika neman junansu. Shi ya sa zuwan Musulunci ma ya kawo ma hukuncin masu aikata wannan cewa kisa ne ta hanyar jefo su daga dogon gini”.

Hakika a shekarun baya ba za mu ce babu wannan abu ba, amma ko da akwai to ba a jin hirarsa sosai sai yanzu ne yake ?ara habaka. Amma yanzu me ya jawo abin ya taso ya habaka har yana neman samun gindin zama a kasashenmu?

Dalilai da suke haddasa yawaitar madigo

Da farko akwai kaucewa koyarwa ta addini da ya umarci iyaye da su aurar da yaransu da wuri yayin da suka kai minzalin balaga. Amma maimakon haka sai a dauka cewan hakan ?auyanci ne, don haka a bar yara mata su yi karatu mai zurfi. Wanda kuwa a wurin karatun wasu ke ha?uwa da wannan bala’in yanayin da ake barinsu suke cakudawa da wasu masu halin.

Shiga cikin taron kawaye inda masu irin halin suke na taimakawa. A irin haka wasu har gida za su rika biyo ta, uwa ta saki baki ai kawayen ‘yarta ce don haka sai a shigo a shige daki. A irin wannan ne za ka ga ita ma ta zama gwana in ba a yi sa’a ba har kannenta ta ba ta.

Auren mace mai irin wannan hali. Misali mutum ya auro amarya bai san tana harkar ba kuma yana ‘yan mata da suka girma. A irin haka matar kan ja ra’ayi wasu daga cikin yaran don sa su cikin wannan harkar musamman ma idan suna taya amaryar kwana in ba girkinta ba ne sai a zaci shakuwa ce mai karfi a tsakaninsu amma abin da take koyawa yarinyar kenan. Daga nan yarinyar ita ma ta ?ware har ta koya wa wasu ita ma.

Haka kuma makarantar, kwana takan taimaka wajen samun irin wa?anda suka samu irin wannan mummunar ?abi'a, da zarar ta samu masu irin halin shikenan sai abin ya ci gaba da ya?uwa.

 Musamman in an samu sakacin hukumomin makarantu. Idan hukumomin makarantun kwana za su kafa kwararan matakai na tsaro a dakunan kwanan dalibai. Sannan ya zama wani maudu’i guda mai zaman kan sa da lokaci zuwa lokaci za su rika tunatar da dalibai a kansa da illolinsa. Sannan in suka kama ma su yi su zartar da hukunci to da abin ya yi sauki kwarai.

Bayyanar kafofin sadarwa ta internet: wannan ma hanya ce mai saukin yaduwar wannan masifar. Misali idan aka dubi ‘dandalin Facebook’ akwai kawai sai ka ga guruf-guruf sun fi ?ari na ‘Lesbian’ ‘yan madigo, wadanda kawai wannan abu ake a ciki. Kuma abin takaici cikin kaso 100 ?ashi 90 Hausawa ne ‘ya’yan Musulmai suna maganganunsu na batsa, har da tura hotunan da bidiyo na wannan bala’in domin kara dulmiyar da Musulmi kuma suna ajiye lamba, in da mai bukatarsu.

Samuwar fina-finan batsa: Yahudawa sun karfafa abin ta hanyar jefo mana mugayen fina-finai na batsa ta hanyar kasa-kasai ko tauraron ‘yan adam. Tun suna Turawa kyauta har yau abin ya zama da kudi ake saya ta Intanet saboda raja’ar da mutane suka yi kansa. Irin wannan fina-finan zallar abin da suke nunawa shi ne salo-salo na yadda jinsi daya za su biya bukatarsu da juna cikin sauki. Hikimar Yahudawa ta turo wannan balai ?aya ne da na Shaidan, shi ne su dulmiyar da mutane ga sabon Ubangiji.

Wadannan suna cikin abubuwan da suka taimaka ?warai wajen yaduwar wannan cuta ta Madigo. Duk da cewa Shaidan la’anannen Allah shi ya kawo mana tallar wannan masifa to amma fa a zamanin nan yan’uwansa Yahudawa sun taimaka.

Matsalolin da madigo ke haifar wa masu yin ta:

 1. Yana haifar da mugun ciwon mara

Duk yadda masu madigo suka kai ga dabara da kwarewa ba za su taba kancewa kaman suna tare da namiji ba. Hakan kuma yana nufin wannan ruwan yana taruwa ne a mararsu a hankali kuma yana daskarewa har ya taru ya zame masu ciwo mai tsanani mara jin magani.

 2. Yana haifar da cuta tun daga farji har izuwa mahaifa

Wadda wannan cutar kuma tana iya hana haihuwa kwata-kwata, baya ga gusar masu da sha’awa na maza.

 3. Yana haifar da ciwon nan na hanji

Wannan cutar na hanji ita ke haifar da gudawa ba tsayawa sai dai ga mutum na tsiyayewa.

 4. Yana sanya ciwon ruhi

Ciwon ruhi ba ciwone da ake sha masa magani ko allura ba. Ciwo ne da yake kekashe zuciya ya sanya imani ya fita daga cikinta ya zamo dan Adam ya fita daga haddin mutane yana kuma iya aikata abin da dabbobi ma ba za su iya aikatawa ba.

 5. Yana haifar da cutar mantuwa

Mutum ba zai iya ri?e abu a ?wa?walwarsa ba, misali za ka yi abu yanzu da shi amma zuwa anjima zai manta, sannan kuma yana rage kaifin basira.

Yana rage masu sha’awan mazan aurensu:

Yana taimakawa wajen yaduwar cutar sida (Kanjamau):

Yana kashe masu sha’awa gaba daya.

Yana kashe aure.

Yana kashe zuciyar masu yin sa
Allah ya ?are mu da sharrin wannan bala’in. 


Post a Comment

0 Comments