Menene Cryptocurrency?



Menene Cryptocurrency?

Jama’a da yawa suna tambaya akan Kasuwancin Cryptocurrency da kuma yadda ake sarrafashi, kasancewar bai jima da shigowa wannan zamanin ba.

Cryptocurrency a taƙaice kasuwanci ne na canjin kuɗaɗe a yanar gizo ba tare da shigowar wata hukuma ko banki ba, wato canjin kuɗaɗe ne da ake yi kaitsaye tsakanin mai siyarwa da mai siya.

Misali yadda ake canja kuɗaɗen daga Dollar zuwa Naira ($ => ₦) ko zuwa kuɗaɗen wasu ƙasashe daban, haka ake canja waɗannan kuɗaɗe na intanet zuwa wani kuɗi.

Saboda yawaitar hatsaniya da sauran dalilai, a yanzu ba a buƙatar sai mutum ya je banki kafin ya iya biyan kuɗi a yanar gizo ko ya tura zuwa wata ƙasa, cikin hanyoyin da ake bi na zamani akwai wannan hanyar wacce ta zama ruwan dare a wannan zamanin. Kuɗaɗen intanet za su ba wa mutum damar musayar kuɗaɗe a yanar gizo ba tare da shigowar wata hukuma cikin lamarin ba.

Rashin shigowar hukuma cikin lamarin ba shi ke nuna cewa ba ingantacce ba ne, haƙiƙa an jima ana wannan harkar kuma yawan damfara yana raguwa ta dalilinsa.

Cryptocurrency kaitsaye shine kuɗaɗen Intanet, haka zalika Cryptobusiness kuma shine kasuwancin kuɗaɗen a yanar gizo.

Yadda tsarin yake
Ana siyan waɗannan kuɗaɗe na intanet domin siyar da su ga wasu a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso. Saboda yadda waɗannan kuɗaɗe suke tashi, misali yadda (Dollar, $) take tashi a yanzu, siyanta zai iya zama riba ga mutum – ta yadda za a siya a yau, kashegari kuma a siyar musamman idan ta ƙara kuɗi. Haka harkar kasuwancin cryptocurrency yake a yanar gizo.

Ire-iren Cryptocurrency
Kuɗaɗen intanet na wannan harkar ta cryptobusiness suna da dama, a cikin mafiya shahara sun hada da:

Kuɗaɗe Adadin Kuɗin Lantarki Farashin Kuɗi a Naira
Bitcoin BTC 0.00005383 ₦1,000
Litecoin LTC 0.012274 ₦1,000
Ethereum ETH 0.001682 ₦1,000
Bitcoin Cash BCH 0.00459 ₦1,000
Ripple XRP 6.10 ₦1,000
…da sauransu.

Abinda ake fara yi da farko shi ne, a matsayin mutum na ɗan-koyo sai ya duba wanda ya kamata ya fara siya a cikinsu. Sannan kowanne akwai tsarin yadda ake amfani da shi da kuma yadda ake kasuwancinsa.

Idan aka ɗauki Bitcoin musamman yadda yake tashe kullum a kasuwa, zai fi sauƙin harka sai dai yana da tsada. A yanzu haka Bitcoin 1 ya kai N30,670,562. Ana lissafinsa da 0.1 zuwa sama. Sannan ana buɗe masa asusu da ake kira wallet a shafukan da ake harkar. Haka suma sauran kuɗaɗen Intanet kamar su Ethereum, Litecoin da sauransu…

Post a Comment

0 Comments