Wasu Dabi'u Da Halayen Da Zaka Mamaye Zuciyar Matarka Dasu:
Idan kana tunanin zaka iya cusawa matarka kaunar ka da kudi ko tarin dukiya to fa har yanzu da sauran ka a fahimtar halaye da dabi'u irin na mata.
Wasu mazan suka shiga rudun rashin sanin wasu hanyoyin da zasu bi domin ganin sun dauwamar da soyayarsu a zukatan matan da suke aure.
Musamman bayan sun auresu.
Ga wasu dabi'u da halaye masu sauki mazaje zasu iya mallakar zukatan matan su dasu har bayan ransu.
1: Tayata aiyukan cikin gida: nan take zaka mamaye zuciyar matarka cikin sauki muddin kana taya ta kananan aiyuka na cikin gida wanda akasarin maza dauka suke wadannan aiyukan tamkar wajibi ne.
2: Rakata Ganin Likita: Mata suna son ganin mazan su na musu rakiya a lokacin da suke da wata matsalar da zasu ga likita musamman a lokacin da mace take da juna biyu.
3: Daƙin Haihuwa: Duk mace na alfahari da mijin dake rakata daƙin haihuwa koda kuwa baza a barshi ta haihu a gaban sa ba.
4: Kaita Cin Abinci: Har bayan ranka mace bazata manta da kai ba idan kana ware wasu lokutan da kake hutar da ita girki ka kaita gidan cin abinci da maƙulashe taci tayi tsara ba.
5: Yawon Bude Ido: Basai ka kaita Dubai ko Amurka ba. A Kasar ka, yankin da kake ko jihar ku koma garin ku baza a rasa wasu wurare da zaka dauki matarka kuje yawon bude ido ba.
Kada ka maida matarka tamkar wata fursina a gidanka. Da unguwa sai tafiyan gaisuwar mutuwa amma baka da lokacin kaida ita ku fita yawon shan iska ba.
6: Ciyar Da Ita: Mace na son tana zaune mijinta na ciyar da ita. Hakan yakan kara soyayya ga ma'aurata har bayan ransu.
7: Yabawa Gitkinta Da Kwalliyar Ta: Muddin zaka rika yaba kwalliyar matarka da kuma girkin ta a kullum soyayyar ka zai rika tasiri ne a zuciyar ta.
8: Nasiha: Mata na son a musu gyara cikin nasiha amma ba cikin fada ko fushi ba. Duk mai gidan da zai rika yiwa Matarsa gyara cikin wannan yanayin dole ne yayi tasiri a zuciyar ta.
9: Ziyaran Iyayenta: Ba lallle sai ta sani ba. Duk mace mai tarbiya takan ji dadi a duk lokacin da Mijinta ya ziyarci na kusa da ita musamman ma iyayen ta. Wannan dabiar na sauri baka damar mallakar zuciyar mace.
10: Gamsar Da Ita: Muddin zaka kayi wadannan abubuwan guda tara da muka ambata a sama. Yana da matukar wahala ka iya mamaye zuciyar matarka ba tare da ka iya gamsar da ita a jima'ince ba. Don haka gamsar da mace shine abu na farko a kan hanyar ka na kokarin mamaye zuciyar ta har bayan ranka.
#tsangayamalam
0 Comments