Ba laifi a yi auran zamunci idan ya yi kyau zumunci yayi, idan ya ɓaci zumunci ya ɓaci.
Akwai misalin auran zumunci da auran kusanci, da yawa a musulunci.
Amma yana daga cikin abubuwan dake kawo matsala a rayuwar aure , shine hanyar da ake auren tunda farko.
Auren haɗi da sunan haɗa zumunci tsakanin dangi ko abokai ko wani dalili kamar aurar da yarinya ko yaro ga gidan ma wadata ko malamai domin samun iri ba tare da lura da soyayya ba, na daga cikin auren da ya shahara a ƙasar hausa. Duk da cewa a lokutan baya matsalolin irin waɗannan auruka basu fiya fitowa fili ba , sakamakon tarbiya hakuri da yanayin wayewa da zamantakewa irin ta wancan lokaci.
Amma a wannan zamani da yanani da tarbiyya suka canja , irin wannan auren na haɗi bai fiye haifar da ɗa mai ido ba. Akwai rahotanni na matsaloli kala kala , tsakanin wanda muka ji da wanda muka gani da ba zasu lissafu ba.
Irin wannan aure na haɗi , ya saɓa da koyarwar musulumci da manufofinsa na rayuwar aure da zamantakewa , kuma yana haifar da matsaloli da babu mai kewayewa da saninsu sai Allah.
Alal misali , akwai wani ɗalibi a ƙasar waje yake karatu. Sai ya bugo mini waya, har kuka yake yi, cewa an tilasta masa ya auri wata kuma shi ba ba ya son ta. Ita ma ba ta so amma iyayen sun ce dole sai an yi.
To ka ga wannan ba daidai ba ne.A matsayin ɗalibi da ya kai matakin Jami'a ya yi cuɗanya da mutane da kabilu dabam dabam , ya kamata alal a ƙalla a nemi shawarsa da cikin hikima .
In ba haka ba , a karshe sai ka zo a jefa ɗanka cikin matsala, ka sa ya riƙa jin haushin ka. Ya riƙa jin haushin matar, su riƙa yi muku mummunar addu’a suna fatan ku mutu, domin kun kawo musu cikas a rayuwa.
Ba laifi ka tallatawa ɗanka ‘yar abokin ka, ko ɗan wani mutumin kirki da kake ganin ya dace ɗanka ya aura. Sai ka tallata masa in ya gamsu ya aure ta. Amma kada ka takura masa kan ya aure ta saboda ƴar ku ce. Kada ku ce lallai sai kun haɗa zumunci a dangi ko tsakanin abokai koda kuwa ma'auratan ba sa so.
Amma ba laifi ba ne iyaye su yi kamfen. A samu wata rana da za ku je ziyar gidan da abokin, ita kuma a sa ta ci kwalliya Sannan a sa ta kawo muku ruwa. Daga haka zai iya cewa “kai wannan ‘yar ta ka ai mutuniyar kirki ce, inama ɗa na zai same ta.” Shi ma ya ziga tasa ka ziga na ka. Dai ku haɗa su da dabara. Idan kun basu dama kuka ga suna son juna shi kenan. Idan ɗaya ya gardame shike nan sai a nemar masa wata ita ma a nema mata wani.
Da haka ne malamai suka ce hanyar haɗa aure guda biyar ce:
2. Namiji ya ga matar da yake so da kansa. Wato kana binciken matar da za ka aura sai ka ga wata ta yi daidai da wacce kake buƙata. To sai ka je ka gabatar da kanka wurinta ko wurin iyayenta cewa kana so ko kana ciki. Sai ka tambaya cewa “za a bani dama in zo in gwada, Na gabatar da kai na. Idan an aminta da ni a a lamunce na aura.
3. Mace ta ga namijin da take so da kanta. Duk wannan bai fiye faruwa ba saboda yanayi da al'ada da kunya, amma ba laifi ba ne a musulunci.Mace zata iya gabatar da kanta ga mutumin kirki wanda ko bai gamsu da aurenta ba , to ba zai kunyata ta , ko ya yi amfani da soyayyar da take masa ya cutar da ita ba.
A irin wannan yanayi mace zata iya gabatar da kanta ta aika wani ko wata mai hankali. Ko ta hanyar wasiƙa ko saƙo ga wani cewa “ Suna wance ƴar gidan wane zanyi farin ciki da zaka yarda ka aure ni” ko wani lafazin da ya dace. Ta bayyanar da kanta cewa “
Za ta iya bayyana masa shekarunta da matakin Ilimi da take da shi. Budurwa ce ko Bazawara da sauransu na a mataki kaza nake da shi.” Duka wannan an samu ya faru hatta a zamanin sahabbai an yi.
4. Wani mutumin kirki ya gano ka ko ya gano ta, ya zo ya baka labari ko ya ba ta labari. Kamar yadda Khaulatu bintu Hakim ta zo ta bawa Manzon Allah (SAW) labarin Nana A’isha da kuma Sauda, cewa bayan rasuwar Khadija wacce shekarun ta 25 da Manzon Allah (SAW) lokacin bai yi aure ba bai kuma yi mata sa ɗaka ba. Wato ita Nana Khadija ba ta zauna da kishiya ko kuyanga ba.. To bayan ta rasu sai ya zamo babu kowa a gidan Manzon Allah (SAW) sai ‘ya’ya. Ba mace ko ɗaya, ba sa ɗaka, ba baiwa ba kuma kuyanga. To sai wannan mata KHaulatu bintu Hakim ta ce “ya rasulallah na gano maka bazawara da budurwa, ko ka auri duka biyun ko ka auri ɗaya. Bazawarar ta yi imani da kai kuma akwai mijinta sunan sa Sakaraanu, Allah ya yi masa rasuwa. Idan ka aureta ka ƙimanta ta domin ba za a walaƙanta ta a dangi a ce ta yi imanin banza ba. Gashi yanzu mijinta ya rasu ta tozarta ba. Ita kuma budurwar ‘yar abokin ka ce, wato Abubakar Siddiq. Idan ka aure ta zumuntar da ke tsakanin ku da shi za ta ƙara ƙarfi. Domin ga zumunta ta addini ga ta abota kuma ga ta surkuta ta shiga tsakani.” Manzon Allah ya ga waɗannan dalilai da KHaulatu ta gaya masa duka dalilai ne da ya kamata a duba su kuma daga bisani ya amince ya auri waɗannan matan guda biyu. Ka ga kenan wani yana iya zuwa ya gabatar da wani ko wata.
5- Mahaifi ko waliyyi da kansa yana iya zuwa ya samu wani mutumin kirki da ya gamsu da shi ya ce idan kana buƙatar auren ‘ya ta wance na baka. Kamar yadda Sayyidina Umar, lokacin da Nana Hafsa mijin ta ya rasu, ‘yar Sayyidina Umar ce. Sayyidina Umar da kansa ya fito ya samu Sayyidina Usumanu, ya ce masa akwai ‘ya ta, mijin ta ya rasu ta gama takaba, idan kana buƙatar aurenta na ba ka ita. Sayyidina Usumanu ya ce to shi a bashi lokaci tukunna ya yi nazari. Bayan ‘yan kwanaki da suka haɗu ya cewa sayyidina Umar ba ni da buƙatar yin aure yanzu. Ka ga kenan ya riga ya ba da uzurinsa. Da ya ji haka sai ya tinkari Sayyidina Abubakar, ya ce masa “ga ‘ya ta Hafsa ta gama takaba bayan rasuwar mijinta. Idan kana buƙatar aure na baka ita.” Sai ya yi shiru bai ce eh na karɓa ba, bai ce a’a ban karɓa ba.
Sai bayan ‘yan kwanaki kaɗan sai Manzon Allah ya turo ya ce yana so zai auri Hafsa. Bayan ya aureta sai suka haɗu da Sayyidina Abubakar da Sayyidina Umar. Sai Sayyidina Abubakar ya ke so ya ba Sayyidina Umar hanzari da uzuri a bisa rashin amsa masa buƙatar da ya kawo na ya auri ‘yar sa da eh ko a’a. Ya ce “abin da ya sa ka ga kamar na yi maka shiru ban ce maka eh ba ko a’a lokacin da ka bijiro mini da maganar ‘yar ka ba.” Sai ya ce “gaskiya ne kuma ban ji daɗi ba, gara Sayyidina Usumanu shi ya ce mini ba ya buƙata amma kai sai ka yi tsit.” To shi ne ya ce “dalilin da ya sa na yi tsit, a lokacin da ka kira ni kake tambaya ta game da auren, ni kuma mun yi Magana da Manzon Allah (SAW) ya ce mini yana so zai auri ‘yarka Hafsat, to shi yasa ka ji na yi shiru. Idan Annabi (SAW) ya aure ta, to ka gashi kenan buƙata ta biya. Idan bai aure ta ba to, ni sai aure ta. To kuma bai kamata in gaya maka sirrin Manzon Allah (SAW) ba kafin ya tabbata.” To ka ji a nan uba zai iya zuwa ya bijirar da ‘yar sa ga wani. Kuma duka waɗannan abubuwa da muka faɗa babu wani ƙasƙanci a ciki.
6. Ana iya samun mai dalilin aure ya haɗa. Akwai masu dalilin aure maza da mata dake haɗa aure. Wasu ma sana'rsu kenan kuma sun sami alheri da arziki mai yawa sababinta. Duk da akwai gyare-gyare a cikin abubuwan da suke yi amma dai akwai amfani mai yawa a ciki , domin da yawa wani bai san yadda zai samu matar ba. Wata matar ba ta san yadda za ta haɗu da mijin ba. Ko kuma idonsu bai kai ga wanda suke so ba. Daga abin da ya kamata dai dillalai su dinga yi akwai karɓar hotunan maza kamar yadda suke karɓar na mata a inda ya dace.
Domin yadda kai ya kamata a kawo maka hoton macen ka gani, ya kamata kuma mazan da kuke neman aure kowa ya je ya tsalla wanka ya ɗau hoto ya cakare hula, shi ma ya bayar da nasa hoton. Shima a kai wa matan da suke neman auren idan ta gani ta ce wane ya zo.
Sannan ya kamata su dinga la'akari da waɗanda ba aure ne a gabansu ba. Ta yadda za su tabbatar cewa duk wanda suka ba shi hoton wata yarinya to lallai maganar aure ce; ba maganar wasa a ciki.
La'akari da tarbiyya mutuntakar mai neman aure na daga jigon abin da ya kamata masu dalili su dinga la'akari da shi.
Su dinga yin na su binciken tun kafin su haɗa wani da wata. Domin sau tari akan haɗa wani wata ƙarshe ya yi ƙoƙarin lalata ko biyan bukatarsa da ita. Wannan yana faruwa da yawa.
Misali akwai wacce aka ce wai ta kawo fasfo ɗinta za a fita waje tukunna. Ta ce “mu je waje mu yi me to, me za mu yi a waje ba tare da an yi aure ba?” Ka ga irin waɗannan duka sai an taka musu birki a cikin wannan harka ta haɗa aure.
Kada a maimakon haɗa aure a ɓige da haɗa zina. Kai ko mutumin da aka san cutar da mata ne ko mai yawan auri saki ne bai kamata a dinga haɗa shi da ƴaƴan mutane ba.
7. Daga abin da zai iya shiga haɗin aure. Akwai haɗi ta ɓangaren hukuma. Hukuma tana iya haɗa aure kamar yadda mai dalili yake haɗawa.
8. Daga hanyoyin dabara na haɗa aure akwai haɗin dabara. Misali za ka ga wasu iyayen sun tura ‘ya’yan su cikin dangi, ko idan an yi baƙi sai a sa yaran su kawo ruwa ko su kawo musu abinci. A nan wani yana iya sanin akwai yara a gidan nan da suransu. Idan wani yana buƙata sai yayi magana. Wani lokacin akan aiki yarinya wajen dangi ko ta je wani biki da ko za tab haɗu da wani wanda ba lalle ya ganta ba idan ta zauna a gida.
Wasu kuma sukan ce “to ai malam kuna cewa mu ‘yan mata ko zaurawa mu riƙa sanya hijabi muna rufe jikinmu muna lulluɓi da zai rufe jikinmu gabaki ɗaya . kuma ba za a gane ko a banbanta mu da matan aure da waɗanda ba matan aure ba. Har wata ta taɓa bada shawara duk da ba mu yarda da shawararta ba, cewa me yasa ba za a bambanta hijabi ba ya zama matan aure a yi musu wata kala, zawarawa ma a yi musu wata kala, ‘yan mata a yi musu wata kala. Yadda duk wacce ka gani da shiga iri kaza to budurwa ce. Idan ka ga wata da shiga iri kaza to bazawara ce. Idan ka ga wata da shiga iri kaza to matar aure ce. Saboda haka mun duba wannan mun ga yana da illa shi ya sa ba mu gamsu da wannan shawara ba.
Dalili, zai rika nunawa mutane irin rayuwar da al’umma ke ciki. Ta yiwu wataran aka ga dandazom mata sun taso duk da hijabi irin na zawarawa, ka ga kawai kallon su za a riƙa yi cewa ga dandazon zawarawa nan. Ko kuma a zo taro ga mata da yawa a cakuɗ sai a ga kalar hijabin da ke nuna matan aure ya fi yawa ko wanda ke nuna zaurawa ya fi yawa ko kuma wanda ke nuna ‘yan mata ya fi yawa. Sai muka ga dai babu hikima a cikin wannan shawara, shi ya sa ba a ɗauke ta ba, ba a yi aiki da ita ba.
Saboda haka aka ga shawara ce da ba za ta haifar da maslaha ba.
Gara dai a ci gaba da bin hanyoyin da ake yi na nunawa juna ma’aurata
A wasu ƙasashen akwai ƙungiyoyi da aka kafa da cibiyoyi, da gwamnati ta amince da su, aikinsu kawai haɗa aure.
Akwai kuma kwararrun ma’aikata masu amana waɗanda mace za ta zo ta gabatar da kanta a yi mata tambyoyi a tanbaye ta rayuwarta da komai a tabbatar ta cancanci aure, su kuma su ɗau ragamar haɗa ta da wanda ya dace da ita . Kamar yadda maza su ma suke zuwa..
Waxannan cibiyoyi su zasu haɗa kowa da wanda ya dace , su yi magana a gabansu su tabbatar kuma su shaidawa iyayen cewa waɗannan ma’auratan sun cancanta su yi aure.
Malaman addini su ma wata mahaɗa ce babba dake haɗa aure , ko samawa mata mijin aure.
Duka dai akwai buƙatar kula da tarbiyya da kiyaye ƙa'dojin shari'a. Kiyaye sirri jigo ne da zai taimaka ƙwarai da gaske. Dalili kuwa shi ne akwai mata da maza da yawa dake tsoron a dinga yaɗa su cewa an kai hotonsu wurin dillalai.
0 Comments