Zaman aure tabbas abu ne mai matukar muhimmaci a rayuwar bil'adama wanda mutane masu banbancin jinsi kan hadu suyi domin taimakon juna da muka samuwar iyali.
To sai dai kamar ko wane irin yanayin na zamntakewa, ko da tsakanin harshe ne da hakori, kamar yadda Hausawa kan ce, akan samu sabani a tsakanin ma'auratan da a wasu lokutan ma ake rabuwa.
Duk da dai musabbabin rabuwar kan iya samun asali daga dukkan bangarorin, amma dai tun daga wurin yin auren babban abun da ake shawartar ma'auratan da shi shine hakuri.
wasu daga cikin hanyoyin da mace zata iya bi domin sace zuciyar mijin ta a zamantakewar aure:
1. Ki so iyayen sa da dangin sa
2. Ki guji yi masa binciken kwaikwaf
3. Ki daratta shi tare da bashi girma
4. Ki kula tare da tattala masa dukiyar sa
5. Ki taimaka masa lokacin da bashi da hali.
0 Comments