MAGUN-GUNA DA MANZON ALLAH (SAW) YA AMBATA:




🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

HABBATUS-SAUDA:

Daga Nana A'isha (RA) ta ce: "Manzon Allah (SAW) ya ce: wannan Habbatus-Sauda waraka ce daga dukkan cuta sai dai mutuwa.

FA'IDOJINTA:

Idan aka damqata aka dama da zuma aka sha da ruwa mai zafi tana narkar da tsakuwar ciki.

Tana bubbugar da fitsari da haila da nono, idan aka sha zuwa kwana biyu.

Tana maganin kuturta.

Tana amfani wajen rage majina.

Ana dandaqata a zuba a wani qyalle a shaqa don maganin ciwon kai nan take, da mura.

Shan ta da ruwa yana da amfani ga mai numfashij da qyar.

Don haka tana matuqar taimakawa mai Asma.

 
ARRAIHAN/XOXXOYA:

Raihan tsiro ne mai qamshi, ana shuka shi a kudancin Asiya da Iran da wani vangare na Africa da tsakiyar America.

Allah (S.W.T) yana cewa:
"فأما إن كان من المقربين* فروح وريحان وجنة نعيم"
Amma wanda ya kasance daga cikin makusanta hutu da bishiyar Raihan da Aljanna sun tabbata a gare shi".

Manzon Allah (SAW) ya ce: "Wanda aka bashi Raihan kada ya juyar dashi domin bashi da wahala wajen xuka yana da daxin qamshi.
Ana kiran Raihan da Xoxxoya ko Kafi Amarya qamshi.

FA'IDARSA:

Idan aka shefe jiki dashi yana yanke warin qashi yana samarwa da jiki qamshi mai daxi.

Yana tafiyar da ciwuwwuka na kai, da hana zubewar gashi.

Yana amfani wajen turo jini cikin qirji da huhu.
Yana buxe hanyoyin jinni da taimakawa zuciya wajen aiki.

Yana maganin Hawan Jini.

ALAMUN HAWAN JINI

Yawan ciwon kai.
Kasa yin barci.
Faxuwar gaba.
Wani lokaci kaji hannunka kamar ba a jikinka yake ba (Minjirya).
Vacin rai haka kawai.
Mai fama da waxannan larurori zai iya yin amfani da wani magani mai suna (Tasiri) domin akwai sinadaran raihan a cikinsa.



HULBA:

Hulba tsirone da ake shuka shi a qasashen Turawa da Asiya da Africa da wasunta.

An ruwaito Hadisi daga Mu'azu xan Jabalin ya ce:

 Manzon Allah (SAW) ya ce: "Da al'uma sun san abin da ke cikin Hulba, da sun sayeta koda da awonta ne na Dinare". Ma'ana gwargwadon abin da aka auna maka sai ka auna zinare gwargwadon hakan ka biya da shi.

FA'IDAR HULBA:

Ana dafata tare da dabino da zuma aci sau biyu a rana domin warware majinar qirji data uwar hanji da kuma wahalar yin numfashi da cututtukan da suka shafi huhu.

Idan aka shafa hulba aka wanke gashi mai duddunqulewa to zai ware ya yi tsayi.

MATSALAR MAHAIFA: Idan mace ta dafa hulba ta zauna a cikin ruwan da aka dafa to duk ciwon da take ji a mahaifa zai wuce.

KUMBURI: Ana shafata a kan kumburi kuma ya sace Insha Allah.

MASU SHAYARWA DA MASU HAIHUWA:

 Hulba tana taimakawa masu shayarwa da masu haihuwa kuma tana vuvvugo da nono. Ana shanta bayan an dafa kuma ana cinta koriya ba tare da an dafata ba.

Ana haxa garin Hulba da zuma ko ruwa a shafa a qurji ko kuma kunburi za'a samu waraka Insha Allah.

Hulba na taimakawa mai ciwon suga domin tana xauke da sinadarin dake daidaita suga a jikin mutum.

ALAMOMIN SUGA:

Yawan jin qishirwa.
Yawan jin fitsari.
Yawan gumi.
Qin warkewar gyambo.
Ramewa.
Yawan kasala da ciwon jiki.



SHA'IR
An ruwaito Hadisi daga Nana A'isha (RA) ta ce: "Manzon Allah (SAW) ya kasance idan zazzavi ya kama iyalansa sai a daka sha'ir tare da ruwa ko nono sai ya sasu su sha sai ya ce: "Yana xauke zuciya mai baqin ciki, yana farantawa ga zuciya mara lafiya kamar yadda ruwa yake faranta fuskar xayanku".

FA'IDOJIN SHA'IR:

Yana vuvvugo da fitsari ga wanda ya kasa yinsa.
Yana tsarkake uwar hanji.
Yana tafiyar da qishirwa.
Yana kashe zafin jiki.
Yana maganin Tayfod da Maleriya.

ALAMUN TAYFOD DA MALERIYA
Yawan ciwon kai.
Zazzavi mai naci.
Ciwon ciki.
Kasala da ramewa.


INABI:

Inabi xan itaciya ne mai daxin xanxano kuma yana xaya daga cikin kayan marmarin sarakuna.

Ana shuka shi a Asiya da Africa. An ruwaito Hadisi daga Ibn Abbas ya ce: "Na ga Manzon Allah (SAW) yana cin Inabi".

FA'IDARSA:

Ana cinsa xanye da busasshe da kore da nunanne. Yana daga cikin mafifitan kayan marmari mafi amfani. Abinci ne daga nau'o'in abinci. mahaxine daga mahaxai, magani ne daga magunguna abin sha ne daga abubuwan sha.

Yana maganin kumburin ciki.
Yana maganin ciwon hanta.
Yana maganin ciwon qoda.

ALAMUN CIWON QODA DA HANTA:

Ido yai kore shar.
Nauyin qirji.
Ciwon ciki ta varin qodar.
Cushewar ciki.
Yawan kasala.
Yawan son bacci.

Kumburin jiki da kasa fitsari wasu lokutan.
Sinadarin Zuma, Da Kankana Dake Cikin Maganin Tasiri Yana Saurin Warkar Da Ciwon Hanta Da Qoda.


ZAITUN:

Zaitun bishiyace koriya a qoda yaushe kuma mai albarka. Allah (SWT) ya yi bayani a cikin Qur'ani inda yake cewa:

"يوقد من شجرة مباركة زيتونة، لا شرقية ولا غربية، يكاد زيتها يضيء ولو لم تمسسه نار".

Manzo (SAW) yana cewa: "Ku dinga cin zaitun, ku dinga yin mai da shi domin shi daga Bishiya mai albarka yake".

FA'IDOJINSA:

Yana maganin ciwon ciki.
Yana tausasa fata.
Yana qara gashi da qarfafashi.
Yana hana fitowar furfura.
Yana qarfafa da dashi da haqora. Ana dafa gayan zaitun da ma'u Kal ka sha murfi xaya yana qone Basir.

Idan aka dafashi da zuma (ganyen) aka kurkure baki yana ciki kogon haqori".
Yana maganin ciwon kai.
Yana qarfafa haqora idan aka kurkurashi.
Ana shayi da garin don maganin cututtukan dake cikin haihu. Image result for olive oil

DABINO (AJWA):

Yana daga cikin kayan marmari kuma abinci ne, maganine, abin sha ne mai zaqi.

FA'IDARSA:

Yana qarfafa hanta.
Yana tafiyar da warin maqogwaro.
Cinsa a hankali yana kashe tsutsar ciki.
Manzon Allah (SAW) ya ce: "Yana maganin Sihiri da tsafi wanda ya karya da qwaya bakwai sihiri, ko kambun baka ba zai same shi ba".
Hakanan yana maganin Aljani (Namijin dare).
Da aljani mai hana aure.

ALAMOMIN NAMIJIN DARE DA ALJANI MAI HANA AURE:

Yawan mafarkin saduwa.
Yawan ciwon kai da mara.
Yawan lalacewar maganar aure.
Faxuwar gaba haka kawai.
Yawan baki ba mace a wani lokaci ko tai fari wani lokaci.
Yawan rama ko qiba a wasu lokuta.
Aljani mai taurin kai ko cuta mai wahalar magani a gwada yin amfani da magani mai suna (TASIRI) a sha mamaki. Image result for dates fruit

ALHENNA/LALLE:

Daga Abu Huraira (RA) ya ce: "Manzon Allah (SAW) ya kasance idan ciwon kai ya same shi saboda wahayi da yake sauka a gareshi sai ya lulluve kansa da lalle.

FA'IDOJIN LALLE:

Yana amfani wajen qonewar wuta.
Yana amfani wajen kumburi da ciwuka.
Idan aka sa a kan farce yana qara mta kyau.
Yana tsiro da gashi, yana qara masa kyau da qarfi.
Yana kau da cututtukan fata.
Yana buxe toshewar jijiya idan aka xora a gurin.
Hadashi da mai a ringa shafawa yana rage qiba.
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀


Post a Comment

0 Comments