Maganin Qarfin Azzakari Da Dadewa Ana Jima'i:






Rashin ƙarfi mazakuta, wani babban kalubale ne da maza ke fuskanta a wannnan zmani, ba tare da la’akari da shekarunsu ba. Akwai al'amura da yawa dake haifar da matsalar daurin azzakari ga maza da su ka hada da, yanayin kiwon lafiya, matsalolin zamantakewa, shan wasu nau'ikan magunguna, shan sigari, shan magunguna barkatai, shan barasa da sauran su.

Baya ga abubuwan da muka zana a sama dake haifar da raunin mazakuta, matsala a kwakwalwa, kamar damuwa, bacin rai, na haddasa raunin azzakari.

Ana iya cewa mutum ya hadu da wanan matsala ta raunin mazakuta idan yana daya daga cikin abubuwan nan uku.

1. Rashin sha'awar jima'i
2. Rashin mikewar azzakari
3. Rashin dadewar azzakarin a tsaye.

Hakika wani bincike ya gano cewa, samari da yawa na ziyartar likita ne saboda matsalar rashin karfin azzakari. Sau da yawa, maza masu fama da matsalar ciwon sukari, cututtukan zuciya, hawan jini, ko yawan kiba, na iya kamuwa da rashin karfin maza ba tare da sun sani ba.

Idan ba a dauki mataki da wuri ba, raunin mazakuta kan haifar da wasu matsalolin, kamar rashin gamsuwa yayin jima'i da rashin gamsar da iyali, jin kaskanci, damuwa, da kuma matsalolin zamantakewar aure. Hakanan, mai wannan matsala na iya fuskantar barazanar rashin samun haihuwa.

Yanza mu jero hanyoyin maganin matsalar raunin azzakari kamar haka:

1. Motsa Jiki:

"Akwai hanyoyi da waya da ake bi, don maganin raunin azzakari, amma motsa jiki na daya daga cikin mafiya shahara da saurin kawo fa'ida. Wani likita ya bayyana motsa jiki a matsayin hanyar mafi sauri da za a iya maganin raunin azzakari. Motsa jiki na sanya sassan jikin dan-adam su yi aikinsu yadda ya kamata, kuma ta haka ne, ya ke yaƙar matsalar raunin zakari.

Motsa jiki na inganta kewayawar jini a jikin mutum, wanda yake da matukar mahimmanci ga ƙarfin azzakari. Motsa jiki na inganta kewayawar jini ne ta hanyar haɓakar sanadarin 'nitric oxide' a cikin magudanar jini, wanda ya ce shine daidai yadda Viagra ke aiki. Motsa jiki mai na iya haɓaka kwayoyin halitta na 'testosterone', wani muhimmin sanadari na ƙarfin azzakari, kuma mai sanya namiji ya dade ya na jima'i.

2. Abinci Mai Gina Jiki.

Abincin da mutum ke ci na iya yin tasiri kai tsaye ga raunin azzakari. Cin abincin da ke da isasshen sanadaran gina jiki, kamar 'ya'yan itace, ganyayyaki,da kifi, kuma tare da ƙaranta cin jan nama da abincin gwangwani na maganin matsalar raunin mazakuta.

Cin lafiyayyen abinci mai gina jiki na taimakawa kwarai wajen kula da lafiyar jiki gaba daya, hakan kuma na taimakawa wajen samun karfi da kuzari a dukkan sassan jiki.

Hakanan, dole mu a guji cin abincin da ke kunshe da sandarin 'colostral' saboda ya na kara kiba, ita kuma kiba na kara hadarin kamuwa da cututtukan da kan shafi jijiyoyin jiki da ciwon suga da hawan jini, wadanda ke da alaka da rashin karfin azzakari.

3. Isashen Barci:

Wani bincike ya nuna cewa, rashin isasshen bacci na iya zama sanadi na raunin azzakari. Binciken ya ba da tabbatacciyar alaƙa tsakanin ƙwayoyin jima'i na 'testosterone' da bacci, lura da cewa kwayoyin jima'i na 'testosterone' na haɓaka ta hanyar isasshen bacci, kuma raguwarsa na haifar da raunin azzakari da saurin kawowa yayin jima'i.

Tsara lokacin barci da kuma samun isasshen barcin magani ne na rashin karfin mazakuta, kuma na iya taimakawa wajen dadewa ana jima'i.

4. Daina shan Sigari:

Ga maza da yawa, daina shan sigari na iya yi mu su maganin matsalar rashin ƙarfin azzakari, musamman lokacin da hakan ke da alaka da cutar da ta shafi jijiyoyin jiki, wanda ke faruwa sakamakon wahalar kewayawar jini ga azzakari saboda toshewar hanyoyin da jini ke kwarara. Shan taba sigari na iya haifar da matsewar hanyoyin jini kuma suna da tasiri ga karfin azzakari.

5. Daina Shan Barasa:

Wasu mutanen kan sha barasa da nufin maganin damuwa ko baqin ciki, sai dai abin da ba su sani ba shine, ta na iya haifar da raunin mazakuta na wucin gadi da na dogon lokaci.

Tsarin jijiyoyin jikin dan-adam ne ke da alhakin tunkudo sanadarin 'nitric oxide' cikin jiki. Shi wannan sanadarai ya na da mahimmanci wajen samar mikewar azzakari, kuma shan barasa yana lahani ga tsarin jijiyoyin jiki, inda hakan kan haifar da rashin karfin azzakari.

6. Shan Magunguna Barkatai:

Rashin karfin azzakari na iya faruwa sakamako shan magunguna ba bisa ka'ida ba. Magungunan da mutum kan sha yau da kullun saboda wasu cutukan ka iya haifar ma sa da matsalar raunin mazakuta. Magunguna kamar na hawan jini, na matsananciyar damuwa, magungunan ciwon zuciya, ko na ciwon suga da sauransu.

Saboda haka ne ya zama wajibi kar mutum ya sha magungunan kowacce irin cuta ba tare da iznin likita ba. Kuma idan ka na shan maganin da likitanka ya rubuta ma ka, sai ka ke tsammanin ya na da alaka da raunin mazakutarka, to, kar ka daina amfani da maganin a karon kanka, amma ka yi hakan a ƙarƙashin kulawar likita.

7. Tsirrai:

Binciken masana da yawa sun bayyana tasirin tsirrai da ganyayyaki wajen maganin raunin azzakari, amma ya na da matukar muhimmanci duk lokacin da mutum zai yi amfani da irin wadanan magunguna ya yi taka-tsantsan, kodayake, manazarta na ganin akasarinsu na da tasiri sosai kuma ba su da illa ga lafiya.
Misali daya da za mu kawo anan shine, wani hadi mai kyau da ake hada wa da, citta da tafarnuwa da albasa da kuma zuma.

Yadda za ayi shine, a wanke citta da albasa da kuma tafarnuwar, sai a markada a 'blender' sannan a zuba zuma a kansu, sai a jira tsawon minti 30 har sai sun jika, a tace a sha kafin a kwanta da iyali.

SHARE THIS 


Post a Comment

0 Comments