Lafiya Uwar Jiki / Sirrika 7 Na Ganyen Bagaruwa, 'Ya'yanta Da Sassakenta Da Ba Kowa Ya Sani Ba:



 / Lafiya Uwar Jiki / Sirrika 7 Na Ganyen Bagaruwa, 'Ya'yanta Da Sassakenta Da Ba Kowa Ya Sani Ba:



A wannan makon shafinku mai farin jini zai ya yi nazari kan amfanin bagaruwa ga lafiyar dan adam. Bagaruwa ta shahara kwarai da gaske wajen magungunan wasu matsalolin lafiya da dama. Misali ana amfani da bagaruwa don magance matsalolin baki, ciki, gyaran jiki da sauran su.

A wani bincike da masana su ka gudanar kuma mujallar "Chinese Journal of Dental Research" ta wallafa a shekara ta 2012, ya nuna yadda ma su binciken su ka hada bagaruwa cikin wani man goge hakori, don ganin yadda bagaruwar ke tasiri wajen samar da fararen hakora.

Sakamakon binciken da masana su ka gudanar kan mutane 60 ya nuna cewa, hakoran mutanen da ke amfani da man goge baki mai hade da bagaruwa ya fi na mutanen da ke amfanin da man goge baki na yau da kullum fari da haske. 

Har-ila-yau sakamakon binciken ya nuna cewa, bagaruwar na da wasu sanadarai da ke iya maganin matsalolin lafiya da kan shafi bakin dan adam, saboda masanan sun gano mutanen da su ka yi amfani da man goge baki mai hade da bagaruwa sun samu wata kariya daga kamuwa daga cutukan hakora da dasashi fiye da wadanda su ka yi amfani da man goge hakora da aka saba da shi yau da kullum.

A iya cewa, ita bagaruwa dukkaninta magani ce, abin nufi, ganyen bagaruwa da 'ya'yanta da fire ko hudar bagaruwa da sassakenta da saiwarta duk magani ne, don kuwa ana amfani da su ta hanyoyi da dama kuma a samu waraka.

Yanzu ba tare da bata lokaci ba, ga sirrika guda bakwai na bagaruwa don amfanin mai karatu, da fatan a sha karatu lafiya, kuma Allah Ya amfanar da mu, amin.

1. Ana Amfani Da Bagaruwa Wajen Maganin Kuna
Sakamakon yadda mu ke amfani da wuta yau da kullum, musamman ma matanmu, idan har aka samu tsautsayi aka kone, to za a iya amfani da bagaruwa don samun waraka daga kunan. 
Yadda mutum zai yi amfani da bagaruwa don samun waraka daga konewa shine, ya samu 'ya'yan bagaruwa da su ka bushe, sai ya daka 'ya'yan bagaruwar ya ke zubawa a wajen da ya kone din. Idan kuma bai samu busassun 'ya'yan bagaruwar ba, duk da haka zai iya amfani da danyen 'ya'yan. Ya samu danyun 'ya'yan bagaruwar ya ke matsa ruwansu akan kunan, in sha Allahu zai samu waraka.

2. Ana Amfani Da Bagaruwa Don Samun Fararen Hakora Kuma Ma Su Haske.

Mu na kyautata zaton da mai karatu ya ga wannan kanun, hankalinsa zai koma kan sakamakon binciken masanan da mu ka kawo mu ku a sama, game da yadda bagaruwa ke samar da fararen hakora.

Don samun wannan fa'ida ta bagaruwa sai ka samun icen bagaruwa ka ke yin asawaki da shi, musamman ace ka daure ka ke yin aswaki da icen bagaruwar a kullum. Kuma zai fi kyau ka yi hakan sau biyu a kowacce rana, da dare kafin ka kwanta barci, sannan da safe bayan ka farka.

Hanya ta biyu da za a iya amfani da bagaruwa don samun fararen hakora ita ce, ka samu sassaken bagaruwa ka hada shi da jar kanwa ka jika, ka bar su su jika sosai, sai ka dinga kuskure bakinka da shi a kowacce rana, shi ma wannan an fi son ka yi hakan yayin da za ka kwanta da kuma bayan ka tashi daga barci.

3. Bagaruwa Na Samar Da Matsi Ga Mata
Matan da su ka amsa sunansu, ba sa yin sake da gyaran jikinsu don gamsar da mazajensu yayin ibadar aure. Mata za su iya amfani da bagaruwa don matse kansu. Yadda za su yi shine, su samu 'ya'yan bagaruwa da sassakenta sai su hada da Rihatul-hulbi su zuba cikin tukunya su dora kan wuta bayan sun zuba ruwa dai-dai misali, idan su ka tafasa sai su sauke sannan su tace su zuba shi cikin buta su dinga tsarki akai-akai. Idan maganar matsi ne, za ki bai wa kawarki labari, don kuwa wannan hadin bagaruwa na matse mace sosai.

4. Bagaruwa Na Maganin Matsalolin Ido
Ana amfani da bagaruwa don magance wasu daga cikin matsalolin lafiya da kan shafi ido, musamman mutane da ke fama da jan ido. Idan mutum na fama da jan ido sai ya samu ganyen bagaruwa ya tafasa shi, idan ya tafasu sai ya zuba a buta ya ke wanke idon da shi kullum da safe.

5. Bagaruwa Na Maganin Saurin Inzali Yayin Jima'i

Maza da dama na fama da wannan matsala ta saurin kawowa maniyyi kafin matansu su kawo, kuma hakan na yin tasiri wajen rage dankon soyayya. Saboda haka, duk wanda ke fama da wannan matsala ta saurin biyan bukata kafin Matarsa sai ya yi amfanin da 'ya'yan bagaruwa don maganin wannan matsala.

Yadda zai yi shine, ya samu 'ya'yan bagaruwa wadanda su ka bushe, ya daka su, ya ke zubawa a ruwa ya na sha, In Allah Ya nufa za a dace.

6. Bagaruwa Na Maganin Ciwon Sanyi:

Anan mu na nufin sanyi da ake dangantawa da jima'i. Akwai cutuka da ake dauka skamakon yin jima'i da mai wannan cutar. Kuma baya ga haka bincike ya tabbatar da cewa, ana iya daukar wadannan cututtuka a bandaki musamman wanda jama'a da yawa ke amfani da shi ko kuma bandaki marar tsafta.

Mutum zai iya amfani da bagaruwa don maganin sanyi. Don samun wannan fa'ida ta gabaruwa sai ayi amfani da ita kamar yadda mu ka yi bayani a lamba ta 3 dake sama. Wato a samu 'ya'yan bagaruwa da sassakenta a hada da Rihatul-hulbi a tafasa a ke tsarki da ruwan akai-akai, ya na maganin sanyi cikin yardar Ubangiji.

7. Bagaruwa Na Maganin Warin Gaba Ga Mata.
Kamar yadda mu ka ambata a lamba ta 3 da ke sama cewa, ana amfani da bagaruwa wajen samar da matsi ga mata, hakanan, mata za su iya amfani da bagaruwar don maganin warin gaba.

 Idan mace na fama da wannan matsala ta warin gaba, za ta yi amfani da bagaruwa don samun waraka, kuma za ta yi amfani da ita ne, kamar yadda bayani ya gabata a lamba ta 3 da ke sama. Allah Ya sa mu dace, amin.

SHARE THIS 



Post a Comment

0 Comments