ZAMANTAKEWAR AURE GA MA'AURATA:




Me yasa muke ganin kyan wasu amma kuma bama ganin na wasu
Me ya sa wasu mutanen muke ganin kyawun su amma bama ganin kyan wasu? me yasa muke kamuwa da son wasu amma bama kamuwa da son wasu?

Yadda mutane suke tunani ba ɗaya bane, rashin wadatar zuci da muke da ita ba ɗaya bane kuma wannan shi ne dalilin daya sa abubuwan da muke ɗauka a matsayin kyau suka banbanta. Hakan ne yasa zaka ɗauki wani a matsayin kyakkyawa amma kuma wani bazai yi mashi kallon kyakkyawa ba.

A wasu lokutan kuma dalilin da yasa zaka ɗauki mutum a matsayin kyakkyawa amma kuma sauran mutane baza suyi mashi kallon kyakkyawa ba shi ne saboda zuciyar ka ta fahimci cewa wannan mutumin yayi kama da wani wanda ya taɓa inganta rayuwar ka ko wanda zai inganta rayuwar ka. Kuma dukkan hakan yana faruwa ne ba tare da mutum ya ankara ba. Misali.

Mutumin da yake ganin cewa mutane basu damu dashi ba yadda ya kamata ko kuma suna raina ƙarfin izzar shi da kuma yi mashi kallon ƙasƙanci, zai yi ƙoƙarin ganin ya faɗa soyayya ne kawai da mace wacce tayi suna da farin jini ko kuma kyakkyawa (domin ganin ya ɗauki hankalin jama'a)

Idan mutum ya shiga cikin damuwa saboda bashi da baiwar zaƙewa gurin yin magana, to akwai yuwuwar zai nemi yaga ya faɗa soyayya ne kawai da mace mai baki wacce take mutunta mutane. Kuma zai ga kyan wannan macen koda kuwa wasu suna ganin munin ta
Idan namiji baya iya kai zuciya nesa idan ya fusata kuma yana yawan yin nadama daga bisani akan abubuwan daya aikata cikin fushi, to akwai yuwuwar zai fi son macen data ƙware gurin shawo kan mazajen da suka fusata. Koda kuwa sauran mutane basu ga kyan wannan macen shi zai ga cewa kyakkyawa ce a idon shi.
Idan wani yana da siffofin ɗaya daga cikin mahaifanka ko ɗan uwanka da kake so, to zaka ga cewa kyakkyawa ne koda kuwa wasu suna ganin cewa shi munmuna ne.

Idan wani yana da siffofin wani abokin ka na ƙud da ƙud to zaka ga kyan shi koda kuwa wasu suna mai kallon munmuna ne.
Idan wani yana da siffofin wani wanda ka jima kana cutarwa a da can amma sai ka dawo kana yin nadama, to zaka ga kyan fuskar shi koda wasu suna yi mashi kallon munmuna ne.
Idan mutum baya ɗaukan kan shi a matsayin mai daraja da kima amma sai wani yazo yana mutunta shi, to akwai yuwuwar zai ga kyan fuskar shi koda sauran mutane suna mashi kallon muni.



© Copyright shamsuddeen inc all right reserved

Post a Comment

0 Comments