'Abincin wani, gubar wani'.




Kowane ɗan adam yana da yanayin jikinsa da yadda Allah ya halicce shi. Abin da wani zai ci ya karɓe shi, wani kuma zai iya zama guba gare shi.

Abincin da mutum zai ci ya danganta da yanayin jikinsa. Wasu kan iya yin rashin lafiya, wasu ma mutuwa za su yi sakamakon hada wasu nau'ukan abinci.

Wani zai iya cin abu ya mike ba wata matsala, wani kuma guba ne gare shi. Mutum zai iya samun wata matsala da ba ya da ita sakamakon hada wasu nau'ukan abinci.

Ko wane irin nau'in abinci yana da amfaninsa, kuma hada wani da ke da amfani iri ɗaya ko daban-daban zai iya haddasa matsala ga mutum.


Ga mutanen da ke son hada nau'ukan abinci domin rage kiba da ƙarin kuzari ko mazakuta yana da kyau a fara tuntuɓar masana abinci.

Masaniya kan lafiyar abinci a Najeriya Habiba Haruna ta yi wa BBC bayani kan na'ukan abinci shida da idan an haɗa suke iya zama guba ga wani.

Kifi da madara:

Kifi da madara suna da sinadarai masu gina jiki kuma hade su wuri daya ba zai karɓi wasu ba - zai iya zama matsala.

Wani yanayin jikinsa ba zai so sanadari iri daya ba kuma nau'i daban-daban idan suka hadu za su iya zama matsala.

Wani zai iya zama guba gare shi ya dinga yin amai wani kuma zai haddasa masa gudawa saboda hade nau'in abu biyu masu amfani iri daya a jiki.

Madara da ayaba:

Haɗa madara da ayaba yakan iya zama guba ga wasu duk da cewa wasu za su hada su ci su kwana lafiya.

Ayaba tana da sinadarin potassium, idan mutum yana da ƙarancinsa kuma ya hada da madara ba zai samu matsala.

Amma wasu idan suka haɗa da madara da ayaba yana haifar masu da matsala kamar ƙaiƙayin wuya, wasu kuraje ko borin jini a jiki ko samiha.

Wasu zai janyo masu kasala.

Lemun tsami da madara:

Madara da lemun tsami ba su shiri domin nan take madara za ta tsinke idan aka haɗa da lemun tsami.

Idan mutum ya hada lemon tsami da madara ya sha zai iya zaman masa guba. Zai iya sa wasu zafin zuciya.

Gyaɗa da man zaitun:


Gyaɗa na da amfani sosai ga jikin ɗan adam kuma akan yi amfani da ita a fannoni da dama.

Gyaɗa na da sinadarin protein mai gina jiki da kuma sinadarin carbonhydrate mai kara kuzari.

Gyaɗa na cikin abubuwan da ke narkar da abinci, musamman masu son rage kiba suna amfani da gida a abinci.

Man zaitun kuma duk da yana da amfani musamman maganin cutuka da dama amma kuma hadawa da gyaɗa yana haifar da wani yanayi ga waɗanda ba su son man zaitun.

Shan magani da lemun zaƙi mai gas

Shan magani da wani nau'in kayan zaƙi mai gas kan iya haifar da mummunan illa ga mutum.

Masaniyar ta ce wani lokaci shan magani da Fanta ko Coca-Cola zai iya kashe mutum saboda gas.

Ta ce duk wani lemun zaƙi mai gas ba a son a hada da magani a sha.

Ɗanyen nama da ɗanyen ƙwai:

Haɗa ɗanyen nama da ɗanyen kwai zai iya haddasa matsala ga jikin wasu ƴan adam.

Yakan iya zama guba ga wasu, wasu na iya yin amai da gudawa saboda bai dace da yanayinsu ba.

Ɗanyen nama zai iya haifar da illa idan har ba a bi hanyoyin sarrafa shi ba domin rage karfin sinadaran da yake ɗauke da su.

Masaniyar ta ce ɗanyen kwai ba ya da wani amfani a jikin ɗan adam, domin yadda aka sha haka zai tsaya a jiki ba tare da wani amfani ba sai idan an dafa ko an soya ba. "Ba a aman ɗanyen ƙwai," in ji Ƙwararriya masaniya kan lafiyar abinci a Najeriya Habiba Harun

1px transparent line:

Masaniyar ta ce ba mutane shawara su ci abin da suka san zai masu amfani kuma ba zai haifar masu da matsala ba.

Kokarin gwada wani abu sabo zai iya amfani ga wasu amma kuma zai iya zama illa ga wasu.

Yadda ake da zabi da dama na nau'ukan abinci haka kuma yanayin mutane ya bambanta. Dole mutum sai ya yi taka-tsantsan da nau'ukan abincin da zai haɗa ya ci.

Post a Comment

0 Comments