🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
SHARE 🚀
Da sunan Allah mai yawan Rahmah mai yawan jin kai, Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga shugaba, farin jakada, Annabi Muhammad Sallallāhu alayhi wa Sallam da Ahalin gidan sa zababbu da sahabban sa masu girma baki daya.
ZAITUN DA MAN ZAITUN
Hakika zaitun itaciya ce mai albarka da kuma bada cikakkiyar lafiya a jikin dan Adam, kamar yadda muka sani cewa zaitun abune mai daraja, kamar yadda muka samu bayanin ta a cikin
Littafin Allah mai Tsarki (Al-Qur'ani),
haka kuma kamar yadda aka samu daga hadisan Manzon Allah Sallallāhu alayhi wa Sallam.
An samu daga sayyadina Umar Allah ya kara masa yarda yana cewa: Manzon Allah Sallallāhu alayhi wa Sallam yace: "Kuyi abinci da man zaitun kuma Ku shafa shi a jikin ku, domin hakika shi yana daga cikin bishiya mai albarka.
Tirmizhy ne ya ruwaito shi.
KADAN DAGA CIKIN AIKIN DA ZAITUN YAKE YI GA LAFIYA SUN HADA DA:
́
1. KARFIN MAZAKUTA
Duk mutumin da ya samu kan shi a wannan hali, to ya samu garin habbatussauda ya dinga zubawa a cikin ruwan danyan kwai sannan a Soya shi da man zaitun ya dinga ci. Kullum, in shaaAllah zai samu karfin mazakuta sosai. Kada a gaji duk wani magani da aka gani a gwada za a dace in shaaAllah.
2. CIWON CIKI
Duk mutumin da yake ciwon ciki sai ya samu man zaitun kamar cikin cokali ya hada da garin habbatussauda ya cakuda ya sha safe da yamma. A samu kamar sati daya ana sha in shaaAllah.
3. CIWON KAI
Duk mutumin da yake ciwon Kai to sai ya samu man zaitun yana shafawa a kan sa yana kuma shan cokali daya da safe da Rana da dare in shaaAllah za a samu lafiya.
4. CIWON HAKORI
Duk mutumin da yake ciwon hakori sai ya samo ganyen Zaitun da "yayan habbatussauda a saka su a cikin garwashi sai a bude baki hayakin ya dinga shiga, in shaaAllah.
5. CIWON HANTA
Duk mutumin da ya kamu da wannan ciwo sai ya dinga shan man zaitun cikin cokali daya da safe daya da Rana daya da dare.
6. CIWON DADASHI
Duk mutumin da yake ciwon dasashi sai ya samu man zaitun ya dinga wanke bakin sa da shi.
7. TARIN FUKA
Duk Wanda yake tarin fuka to sai ya dinga shan man zaitun cokali daya kullum.
8. CIWON SUKARI (DIABETES)
Duk mutumin da ya kamu da ciwon sikari to sai ya samu man zaitun da tsamiya yana hadawa yana sha kafin ya kwanta bacci in shaaAllah zai warke.
9. CIWON ASMA (ATHMA)
Duk mutumin da wannan ciwon ya kama shi ,to sai ya samu ganyen zaitun ko "yayan sa ya dinga turara wa.
10. CIWON KODA
Duk mutumin da yake ciwon koda, to sai ya dinga shan man zaitun cikin cokali uku a Rana in shaaAllah.
11. CIWON BAYA
Duk mutumin da yake ciwon baya, to sai ya samu man zaitun da garin habbatussauda a kwaba ya dinga shafawa a bayan in shaaAllah.
12. CIWON RAMA
Duk mutumin da yaga yana ramewa, to ya dinga shan man zaitun kullum cokali uku in shaaAllah zai yi kiba.
Karin bayani:
Amma a rage yawan tunani da bacin rai.
13. ZAZZABI MAI ZAFI
Duk mutumin daya kamu da zazzabi mai zafi to sai ya dinga shan man zaitun cokali daya sannan yana karanta Āyatul Kursiyyu sau 7 yana tofawa a cikin ta yana shafe jikin sa da ita in shaaAllah.
14. KYAWUN FUSKA
Duk mutumin da yake so fuskar sa tayi kyau, tayi fari Wanda ba zai cutar da shi ba, to ya dinga shafa man zaitun da na habbatussauda in zai kwanta bacci bayan ya tashi da safe sai ya wanke da sabulun salo zai yi mamakin yadda fuskar sa za ta koma.
15. ZUBEWAR GASHI
Duk macen da gashin ta baya futowa sosai ko in ya futo sai ya zube, to sai ta samu ruwan zafi ta wanke kan ta da shi sannan bayan ya dan bushe sai ta zuba man zaitun a hannun ta, sai ta shafe kan na ta da shi gaba daya kullum.
16. KARANCIN JINI
Duk mutumin da yake da karancin jini a jikin sa to sai ya dinga shan man zaitun cokali biyu a Rana.
17. BAYAN GIDA MAI KARFI (WATO BASUR)
Duk mutumin da yake shan wahala in yazo zai yi bayan gida, wani ma sai Yayi kuka saboda wahala, to sai ya samu man zaitun da garin habbatussauda ya kwaba sai ya turashi a cikin duburar sa in shaaAllah bayan gidan sa zai rika fita da laushi b wahala.
18. CIWON MARA GA MATA
Duk matar da take haila tana fama da ciwon Mara saboda fitar jini in tana so ta samu saukin wannan ciwon, sai ta samu man zaitun tana hadawa da ruwan tsamiya tana sha, in shaaAllah duk lokacin da za tayi haila ba zai Mata ciwo ba.
19. SANYIN KASHI
Duk mutumin da kashin sa yayi sanyi baya iya motsa shi, to sai ya samu man zaitun da man habbatussauda ya dinga sha yana kuma shafawa a wajan in shaaAllah.
20. KYAWUN FATA DA LAUSHINTA
Duk mutumin da yake so fatar sa tayi laushi da kyau, to sai ya sami man ya dinga shafe jikin sa da shi bayan Yayi wanka da ruwan dumi, zai yi mamaki yadda fatar sa za ta koma da izinin Allah.
21. KURAJEN KARZUWA (QAZUWA)
Duk mutumin da yake da karzuwa ko wasu kuraje ko sabon miki, to sai ya samu ganyan zaitun ya kirba shi ya hada da garin habbatussauda yana shafawa a wajan har ya warke.
22. CIWON KUNNE
Duk mutumin da yake ciwon kunne, to sai ya Bari in zai kwanta bacci sai a dinga hada man zaitun da na habbatussauda yana digawa a kunnen sa a toshe da auduga in shaaAllah.
23. CUTAR KYASFI
Duk mutumin da yake da KYASFI a jikin sa, to sai ya samu ganyen zaitun busasshe, ya daka shi yayi laushi sai ya hada shi da man zaitun ya cakuda, ya dinga shafawa a wajen lokacin da zai kwanta bacci, sai ya wanke in ya farka daga barci.
24. SHAFAR ALJANU
Duk mutumin da yake so ya rabu da aljanu, to ya dinga amfani da man zaitun saboda aljanu basa son shi, shi da habbatussauda.
Dan haka yana da kyau mutum ya lazimci amfani da su a ko wane lokaci, in da hali ma ya mai da su man sa na shafawa da kuma zubawa a abinci ko abin sha, amma yana da kyau kafin a Fara shafawa a karanta Āyoyin rukyah da kuam Azhkārai wadanda suka tabbata a Sunnah.
25. CIWON KARKARE (DAN KANKARE)
Duk mutumin da ciwon karkare ya same shi, to sai ya samu man zaitun, sannan a samu lalle a kwaba, sai a zuba man zaitun din a cikin lallen a gauraya, sannan a karanta (ĀYATUL KURSIYYU) sau 7 a tofa a ciki sannan sai a tofa a jikin wannan karkare in shaaAllah.
26. CIWAN NONO
Duk matar da take fama da ciwan nono saboda rashin zubar sa, to ana hada man zaitun da garin sa, a barbada a kan nonon saboda samun damar zuba, dan kofofin su bude.
27. MOTSA SHA'AWA
Man zaitun yana motsa sha'awa in an shafa shi a lokacin da za ayi mu'amalar aure ga masu aure in shaaAllah.
28. CIWON SAIFA
Duk mutumin da yake ciwon saifa, sai ya hada man zaitun da garin habbatussauda da kuma Zuma farar saka ya rika sha, in shaaAllah.
29. TSUTSAR CIKI
Duk mutumin da yake fama da tsutsar ciki, to sai a samu man zaitun da garin habbatussauda da zuma ya kwaba su ya riak sha, wannan tsutsar zata mutu da yardar Allah.
30. CUTAR HANJI (ULCER)
Duk mutumin da yake da gyanbon ciki, to sai ya samu garin habbatussauda kamar cokali daya sannan ya samu garin (khumasari)da ganyan zaitun mai laushi ya jika su ya dinga sha har sai ya warke.
31. FITSARIN KWANCE
Duk yaron da yake fitsarin kwance, to sai a samu garin zaitun da kuma garin habbatussauda a zuba a nono a rika bashi yana sha zai daina in shaaAllah.
32. MUTUWAR JIKI (YAWAN KASALA)
Duk mutumin da jikin sa yake yawan mutuwa to sai ya dauwama yana shan zuma da garin habbatussauda da na zaitun zai ji karfin jikin sa in shaaAllah.
33. YAWAN ZABBABI
Duk mutumin da yake yawan yin zazzabi, to sai ya samu garin habbatussauda da na zaitun kamar cikin ludayi ya kwaba da ruwan zafi, da kuma zuma maras hadi ya dinga sha in shaaAllah zai warke.
34. CUWON GABOBI
Duk mutumin da gabobin sa suke masa ciwo to sai ya samu garin habbatussauda da na Zaitun da zuma ya dinga sha, sannan kuma ya zuba garin habbatussauda a cikin man zaitun ya dinga shafawa a gabobin.
35. KWARKWATA
duk matar da take fama da matsalar kwarkwata kuma har take son rabuwa da ita, to ta samu man zaitun da garin habbatussauda ta kwaba sannan sai ta bari sai Rana ta take sai ta zuba wannan man a kan ta ta bar shi yayi kamar minti (20) sannan sai ta wanke in shaaAllah za tayi ban kwana da kwarkwata kuma za taga a in mamaki..
36. CIWON TARI
Duk mutumin da ya kamu da ko wane irin Tari to sai ya samu garin habbatussauda da man zaitun da yar'citta da tsamiya da zuma, sai ya hada su guri daya ya cakuda ya dinga ci in shaaAllah.
37. MAJINAR KIRJI
Duk mutumin da yake fama da yawan majinar kirji to sai ya samu man zaitun da garin habbatussauda ya hada ya dinga sha kullum sau biyu (2) safe da yamma.
Copyright BY: Sirrin rike miji
FACEBOOK GROUP: sirrin rike miji
EMAIL: sirrinrikemiji@gmail.com
FACEBOOK PAGE LIKE: sirrin rike miji
WhatsApp: ☏+2348037538596
0 Comments