SHAGULGULAN AURE DA TASIRINSU A TARBIYYANASSIN MAƘALAR DA AKA GABATAR A WAJEN TARON BITAR KWANAKI BIYU:



By Kabir Abubakar Asgar

- Shimfiɗa

Musulunci ya shar’anta bayyana farin ciki da annashuwa lokacin samuwar ƙaruwa irin ta aure. Saboda a cikin hakan akwai sanya farin ciki da jin daɗi ga masu ruwa da tsaki a cikin sha’anin. 

Sai dai kuma halastawar da Musulunci ya yi wa bikin aure ba sake take ba tsari ba. Musulunci ya lura da ƙa’idojin shari’a da zamantakewa da sanin ya kamata. Ba laifi kowace al’umma ta gudanar da sha’anin biki gwargwadon tanadin al’adarta matuƙar ba a keta haddin shari’a ba.

- Dalilan Halascin Bayyana Aure da Farin Ciki

Hadisin Ahmad da Ibn Majah da wasun su daga Aisha (Allah ya ƙara mata yarda) ta ce: Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ku bayyana aure”

Hadisin Ahmad da Nasa’iy daga Muhammad Ɗan Hadib (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (SAW) ya ce: “Bambamcin da ke tsakanin halas (watau aure) da haram (watau zina) shine dundufa da murya.

Hadisin Bukhari da Muslim daga Anas (Allah ya ƙara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (SAW) ya ce wa Abdurrahman Ɗan Auf sanda ya yi aure: “Ka yi walima ko da da akuya ne”.

Kiɗa a Lokacin Bikin Aure

Musulunci ya ba da damar a yi amfani da kayan kiɗa waɗanda ba sa nuna baɗala da rashin mutunci ko alfasha ko batsa da sakin baki.

Al-Imamut Tabarani ya ruwaito daga Amir Ɗan Sa’ad Al-Bajaliy ya ce na je wajen su Abu Mas’ud da Ubayyu Ɗan Ka’ab da Zaid Ɗan Thabit sai na tarar da wasu kwarkwarori suna buga musu dundufa suna kuma rera waƙoƙi. Sai na ce: “Kuna sahabban Manzon Allah (SAW) amma kuka bari ana kaɗe-kaɗe a gaban ku ba ku hana ba?” Sai suka ce: “an yi mana sassauci akan haka lokacin biki kamar yadda aka yi mana sassauci game da kuka ba tare da ihu ba lokacin da aka yi mana rasuwa”.

Hakanan kuma Aisha (Allah ya ƙara mata yarda) ta raka wata amarya mai suna Al-Fari’ah Bint As’ad zuwa gidan angonta mai suna Nubait Ɗan Jabir sai Annabi (SAW) ya ce mata: “Yake Aisha! Ina fatan dai kun tanadi waƙar da za ku rera in kun isa gidan amarya? Saboda kin san mutanen Madina suna da son shagali lokacin biki”. Sai Manzon Allah (SAW) ya koya mata wakar da za su rera wa wajen rakiyar amaryar.

- Ababen Lura a Wajen Shagalin Biki

Yana da muhimmanci a lura cewa, duk da yake sharia ta halasta shagalin biki, amma wajibi ne a kula da ƙa’idoji masu zuwa:

1. Kar a yi amfani da kiɗa irin na badala da fitsara ko rashin kunya

2. Bai dacewa a tsawaita dare wajen sha’anin saboda abin da ke cikin hakan na cutar da wasu

3. Haramcin cakudedeniya tsakanin maza da mata, a saboda haka, ba ya halasta ango ya shigo tsakiyar mata yana tika rawa shi da amaryarsa

4. Wajibi ne a guje wa duk wata al’ada ta kafirai ko fasikai ko mutanen banza

5. Ire-iren waɗannan shagulgula an halasta su ne ga mata da yara, kuma ana so ne a gudanar da su a wurare keɓantattu ba tare da halartar mazaje ba.

6. Ba laifi mata su yi waƙe-waƙe da raye-raye na al’ada ba tare da badala ba

7. Ɗauke-ɗauken hotuna na daga cikin ababen ƙyama waɗanda ake ƙarfafa batu akan a guje musu

8. Ba a son muryar wata ‘ya mace ta bayyana a matsayin mawaƙiya ko zabiya 

9. Dole ne a guje wa duk wani saɓon Allah, kamar shaye-shaye ko batsa da sakin baki da yasasshiyar magana

Idan sha’ani ya cika wadannan sharuɗɗan to shari’a za ta yadda da shi. In kuwa aka rasa su to shari’a tana ƙyamar wannan shagali da gwargwadon abin da ke cikin sa na saɓo da rashin tarbiyya.

- Tasirin Shagulgulan Aure a Tarbiyya 
 
Yana daga cikin ababen da suka zama ruwan dare gama duniya a bukukuwan mu a yau akwai yawaitar shagulgula da tarurruka tun daga waɗanda ake yi kafin ɗaurin aure (kamar su yawon gudu, kamun amarya, hotunan da ango da amarya suke dauka kafin aure waɗanda aka fi sani da 'pre-wedding pictures’ da sauransu). 

Haka nan kuma akwai waɗanda ake yi bayan ɗaurin aure akan yi tarurruka da sha’anoni kamar tarban amarya wato 'reception', da rakiyar ango da buɗar kai da sayen baki da makamantansu.

Waɗannan tarurruka da ake yi, kasancewar su al’adu ne ba addini ba, za a yi hukunci ne a kan su ta hanyar ɗaura su a kan ma’auni na shari’a. 

Daga nan a yi musu hukunci da gwargwadon dacewa ko rashin dacewar su da ma’aunin shari’a.

Ta fuskar tasirin da suke haifarwa kuwa a tarbiyya za a iya lissafa ababe masu zuwa a matsayin tasirin su:

1. Ɓarnatar da dukiya da kuɗaɗen da za a iya yin ababe masu amfani da su, wani lokacin ma sai an ci bashi ake yin su

2. Bayar da damar cakuɗeɗeniyar maza da mata ajanabai wanda hakan ya saɓa wa tanadin shari’a

3. Sakaci da hurumin hijabi (wato killace mata a gida) da karya alfarmarsu da yaɗa tsaraici

4. Koyi da al’adun kafirai da kuma raya su a cikin mutane

5. Ana yawaita wasa da sallah da jinkirta ta a lokacin bukukuwa

6. Akwai samari da ‘yan mata da ke amfani da ire-iren waɗannan bukukuwa su aikata masha’a

7. Baya ga saɓanin da malamai suka yi akan batun hoto, pre-wedding pictures suna ba wa samari da ‘yan mata damar wuce iyaka a alaƙar samartaka

8. Yaɗa pre-wedding pictures hanya ce ta yaɗa fasadi da ƙaranta kunya cikin mutane

9. Kafofin sada zumunta suna taimakawa wajen yaɗa hotunan pre-weddings zuwa ga dubban mutane

10. Bukukuwan suna haifar da gasa da alfahari tsakanin iyalai da gidaje mabambamta

11. Cire wa mata kunya da kawaici da fid da su zuwa duniyar cakuɗeɗeniya da maza

12. Walimar da mata suke yi tana daga cikin ababe marasa asali a cikin shari’a musamman in ana yin ta da tunanin cewa addini ne

-Nadewa  

Wajibi ne ga iyaye da mazaje su kula da tarbiyyar yara da matan dake ƙarƙashin su saboda amana ce Allah ya ɗaura musu. Haka nan kuma ya wajaba ga malamai da masu wa’azi su ci gama da tunatarwa da ilmantarwa don al’umma su kara fahimtar addini. Sai kuma hukumomi da shugabanni, waɗanda ke da rawa mafi girma da su taka wajen kafa dokokin da za su kiyaye mutumci da nagartar al’umma.

Allah Ubangiji ya sa mu dace.

Post a Comment

0 Comments