Duk Budurwar Tana Tsammanin Wadannan Daga Wajen Wanda Take So:


Duk Budurwar Tana Tsammanin Wadannan Daga Wajen Wanda Take So:

 
Akwai wasu kananan abubuwa da maza sukan rainasu a lokacin gudanar da soyayya ba tare da sanin suna da matukar tasiri a wajen mata ba.

Su irin wadannan abubuwan sunada matuka wahala mace ta furta maka da kanta tace tana son ka rika mata. Amma kuma da zaka rika mata su babu kamarka a birnin zuciyar ta.

Waɗannan a abubuwan sun hada da:
 
Sakonnin text:

Mata suna son masu soyaya dasu su yawaita tura musu sakonnin domin sanin halin da suke ciki.

Da safe mace na son ganin sakon masoyinta domin sanin yadda ta kwana kuma ta tashi. Haka da rana domin jin yadda ta wuni. Cikin dare kuwa ta samu sakon a kwana lafiya daga gareka.

Irin wadannan sakonnin sunada matukar tasiri a zukatan yan matan da suke soyaya.

Kira A Waya:
Yan mata suna son samarinsu na kiransu a waya domin furta musu kalamai na soyayya da kuma yadda kake kewar ta tare da nuna mata ta kula da kanta.

A kalla a kullum ka kirata sau uku. Kada kiran naka ya zama na bibiyan ta ne kana tambayanta inda take da abunda take yi dasu wa take a'a. Kirani na jaddada soyayarka a gareta da kuma nuna mata kulawarka.

Mata suna son hakan amma bazasu iya fadi ba.

Kyauta Na Bazata:

Duk buduwa na son taga mai sonta ya mata kyauta na musamman ba tare da ya sanar da ita ba.

Macen da saurayinta ke mata irin wannan kyauta zai zama babu wani namijin da zai iya takara dashi a wajen wacce yake nema da aure.

Shawara:

Duk budurwa tana son mai sonta ya rika bata shawara akan burinta na rayuwa. Hakan yana karfafa mata gwaiwar ta tare kuma da samun tabbacin ko bayan aure mai sonta ba zai dakele mata wannan burin nata ba.

Sai dai matsalar mata basa iga6 furtawa masu sonsu suna son hakan.

Fadamata Wani Sirrinka:

Mace mai sonka tana so akalla masoyinta ta fadamata wani sirrinsa guda daya wanda zai tabbatar mata da cewa babu wanda yasan wannan abun sai ita.

Ita mace tana matukar jin dadi taji an masoyinta ya sanar da ita sirri hakan nasa su kara tabbatar da soyayyar da yake mata da gaske ne, duk kuwa ba duk mata suke iya boye sirrin da aka fadamusu ba.
#tsangayarmallamtonga 
Waɗannan abubuwan suna cikin jerin wasu ababen da mata suke son masu soyaya dasu su musu amma su bazasu iya fitowa fili suce suna so a musu ba.

Post a Comment

0 Comments