Masoya Su Guji Yawa Juna Wadannan Abubuwan Kamar Haka:


Masoya Su Guji Yawa Juna Wadannan Abubuwan Kamar Haka:
 
Akwai wasu abubuwa da masoya suke yiwa junansu dake dakile ko ya kawo karshen soyayyar tasu gaba daya.

Irin wadannan abubuwan sau tari wasu masoyan suka dauke su ba a bakin komai ba, sai lokacin da guda daga cikin masoyan ya gaza ko ta gaza hakuri sai kuma rabuwa tazo bayan kila sun yi nisa a soyayyar tasu.

Ga wasu abubuwa da masoya ya kamata su kiyaye yiwa juna domin kaucewa samun matsala a soyayyar su.

 
1; Raini- Bai kamata raini ya shiga tsakanin masoya ba. A kullum masoya ana son ganin suna girmama junansun ne.

An fi samun raini a bangaren mata. Akasarin mata suna ganin duk namijin daya furta kalmar so garesu, to wannan mutumin ya zama abun rainawa a wajensu. Don haka duk wacce take son ganin mai sonta ya dauketa da mahimmanci, ya zamto babu zancen raini a tsakaninsu.

2: Karya- Babu karya tsakanin masoya na gaskiya. Da dadi babu dadi su rika kokarin fadawa junansu gaskiyar abubuwan da suka kamata guda ya sani ko ya tambaya.

Karya yana iya rusa soyayyar da aka jima ana raininsa a dan karamin lokaci.

Don haka duk masoyan da suke son ganin sun cimma burin soyayar su, babu karya tsakaninsu.

3: Yaudara- Ita ma wata Matsala ce dake kawo cikas a tsakanin masoya. Ana iya ganin masoya suna tare amma guda yana yaudaran guda. Ita kuwa yaudara daga ranar da mutum ya fahimci yi masa ake, daga wannan lokacin ya daina ganin girman mai masa  Don haka duk masoyan dake son tabbatar da soyayyarsu ya cimma ga ci, su guji yaudaran junansu.

4: Kullata- Ba a kullatan juna a tsakanin masoya.
Su masoya da zaran guda ya yiwa guda laifi kokari ake a fahimci juna kuma da zaran an kashe magana babu mai sake tadota wannan shi zai wadatar da masoyan har su samun cimma burinsu.

5: Zargi- Da zaran masoya sun zama masu zargen junansu, wannan soyayar babu inda zashi.

Zargi a soyayya shike girma ya wuce har bayan aure. Mafi sauki shine duk masoyan da basu aminta da juna ba. Hakura da junansu ya fi maimakon batawa junansu lokaci.

6: Yin Banza Da Bukatun Juna- Bukutu ba lalle bane sai na kudi. Duk da yake su mata sune suka fi bukatuwa na kudi a lokacin soyayya. Wanda bai kamata namijin da ta dogara da shi a matsayin wanda zai aureta yayi burus da su ba.

Ita ma macen akwai wasu bukatun saurayi na yi nayi kada kiyi na kamin aure da ya kamata idan kina son mutun bazaki yi watsi dasu ba.
Yin banza da bukatun juna na masoya zai iya kassara soyayyar su.

7: Kin Amsa Laifi- Wasu mutanen sunada girman kai wajen yarda da wani laifi da aka tabbatar sun yi ba tare da sunyi kokarin daurawa wani laifin da suka yi ba.

Duk masu soyayya na gaskiya dole ya kasance suna amsa laifin da suka yi domin samar da soyaya mai inganci. 

8: Matukar Dogaru-Wannan matsalar mata sunfi yinsa a lokacin gudanar da soyayya. Inda mace zata dogara kataf na bukatunta akan mai sonta da aure. Hakan kuskure ne babba.

Da zaran mutum ya dogara ga wani aka iya samun matsala a lokacin da shi wanda aka dogara dashi ya kasa samar da wannan bukatan a lokacin da ake so.

Kada masoya su dogara akan junansu akan bukatunsu na yau da kullum muddin suna son su cimma burinsu na aure.

9: Zafin Kishi- Shi kishi idan yayi yawa mutum yakan iya rasa abunda yake tsananin so saboda saboda kishi.

Don haka da zaran masoya sun zafafa a kishinsu, suna iya kawo karshen soyayyar su.

10: Rashin Baiwa Juna Lokaci- Duk soyayar da ba a baiwa Juna lokaci wannan soyayar ba zai taba yin inganci ba.

Masoya suna bukatar lokaci a Faggen soyayar su ta hakane suke samun damar shakuwa da juna kuma su katsai duk wani mai burin shiga tsakani.

Da fatan masoya zasu yi amfani da wadannan abubuwan domin inganta soyayyar su.

#tsagayarmalamtonga

Post a Comment

0 Comments