Ko Kin San Illar Saka Takalmi Mai Tsini (Coge) Ga Lafiyarki?:






Takalmi
Daga Muhammad Zahraddeen,

Takalmi mai tsini wanda wasu suka fi sani da coge yana da tsayi hawa-hawa kamar inci daya, inci biyu da inci uku, da sauransu. Ana auna tsayin cogen ne ta hanyar auna tsayin tsinin cogen daga kasan tsinin zuwa tushensa da ke matakar dunduniya.

Tafin sawu da yatsun kafa wadanda ke dauke da tarin gabobi da aka yi musu shiri na musamman domin tsaiwa, takawa ko tafiya cikin sauki. Daga cikin aikin wannan jerin gwanon gabobi da ke tafin sawu ya hada da shanye jijjiga ko girgiza da ke faruwa yayin tsaiwa, tafiya ko gudu sakamakon saukar nauyin jiki a kan kasa.


A takaice dai, jerin gabobin tafin sawu an yi musu kira ne ta “shock absorber” kamar yadda ababen hawa ke dauke da ita domin shanye jijjiga yayin tafiya.

Saboda haka, a lokacin da aka sa coge wannan “shock absorber” za ta dame, don haka ba za ta yi aikinta na shanye jijjiga yadda ya kamata ba.

Haka nan, sa coge na tattare da hadura da ka iya afkuwa nan take ko bayan wani lokaci kamar:

(1) Targade (2) Gurdewa (3) Gocewar kashi (4) Karaya (5) Ciwon yatsun kafa (6) Ciwon idon sawu (7) Ciwon kasan tafin sawu, da sauransu.

Bayan nan, kasancewar matsalolin sa coge ba su takaita iya kafa kadai ba, akwai matsalolin da sa coge mai tsayi yau da gobe fiye da kima kan kawo kamar:

(1) ciwon gwiwa (2) Ciwon baya (3) Daurewar dambubu (Gungun tsokokin bayan sangalalin / kwauri), da sauransu. Wadannan matsaloli suna faruwa ne sakamakon jirkicewar tsarin zaman kashi da tsoka a jikin mutum tun daga tafin sawu har zuwa gadon baya a duk lokacin da aka sa coge yayin tafiya.

Domin haka, ya kamata mata masu sha’awar sa coge da su:

(a) Zabi mafi karancin ko matsakaicin tsayi da tsini, saboda da hadarin sa coge na karuwa ne da karuwar tsayinsa ko tsininsa. A shawarce, an son kada tsayin cogen ya wuce inci uku.

(b) Sannan a guji sa cogen da zai matse yatsun kafa sosai, don haka a zabi mai yalwataccen wurin zira yatsun kafa domin jini ya ci gaba da gudana.

(c) Bugu da kari, ba a son wuce fiye da awanni biyu zuwa uku sanye da coge ana takawa, domin wuce awanni uku sanye da coge na iya gayyato wadancan matsaloli da muka ambata a sama, musamman ma tun da fa’idar sa coge ba ta wuce son karin tsayi ko kuma kwalisa kawai ba.

Daga karshe, idan kina da korafin ciwon tafin sawu ko yatsun kafa, tuntubi likitan fisiyo (physiotherapist) a yau domin duba ki ko kuma neman shawarwari game da irin takalmin da za a sa don wanyewa lafiya.



Post a Comment

0 Comments