Yadda za ki magance warin baki...:


:

dan kina goge haqorinki sau biyu a rana zai yi haske kamar hakaA wannan makon na kawo miki bayanin yadda za ki lura da hakorinki, wato- cire dattin hakori da kuma kara wa hakorinki fari da kuma lafiya.   
 
Ana so ki rika wanke bakinki da man goge baki ko aswaki akalla sau biyu duk rana, hakan zai sanya hakorinki ya yi haske.

Idan kina da dattin hakori sai ki nemi man goge baki kamar daya daga cikin wadannan: Colgate da Rembrandt da 3D Crest da Listerine da Akuafresh da sauransu, sannan kina goge hakorinki da shi.

Za ki iya amfani da bakar soda (Baking Soda) wajen goge hakorinki sau biyu a mako. Kadan ake so ki rika diba idan za ki yi amfani da sodar.

Sannan bayan haka ana bukatar ki kuskure bakinki sosai bayan kin kammala amfani da sodar. Kada don kina amfani da wadannan sinadaran sai kuma ki daina goge bakinki kamar yadda ya kamata.

Ki rika amfani da kororon da ake shan jus ko lemon kwalba wajen shan jus ko lemon kwalba, hakan zai kara wa hakorinki fari da haske. Ya kamata ki rage yawan shan kofi da kuma shayin da ba a hada da madara da sauran kayan hadi ba, domin rashin yin hakan zai kara wa hakorinki datti. Ki guji shan abu mai tsananin sanyi ko zafi, hakan zai taimaka miki wajen kara hasken hakorinki. Ki guji yawaita shan abu mai siga domin kauce wa rubewar hakori. Ki rika amfani da tsinken sakace hakori bayan kin ci abinci, musamman idan kin ci nama ko kifi da dai sauransu. Rashin yin hakan zai sanya sauran abinci ya taru a matse-matsin hakorinki, wanda kuma zai iya janyo wa hakorinki rubewa ko kuma ya yi duhu, ko ya haifar miki da warin baki. 

gyaran hakora.

tabbas yana daya daga cikin burin 'ya mace musamman 'yar kwalisa wato ace tana da fararen hakora,sau da dama rashin kula dayin brush akai akai shine yake jawowa aga hakoran mutum sunyi yellow.

To amma idan har kina kula dasu yar uwa to ba abinda zai sa hakoranki su canza launi daga farare zuwa wata kalan daban ga kadan daga cikin abinda yake lalata mana hakora: -yawan shan kayan zaki da suka hada da sweet,chocolate dss -rashin yin brush bayan shan drinks mai kala misali kamar zobo -rashin wanke baki bayan cin abinci Wadannan sune kadan daga cikin abubuwan da suke jawo dakushewan hakori amma yar uwa zaki iya bin hanya mafi sauki wajen magance hakan. 

idan har hakoranki sun kasance ba farare ki ringa amfani da 

-lemon tsami yar uwa yadda zakiyi zaki yanka lemon tsami ki matse ruwan sai ki kuskure bakinki dashi zaki iya amfani da hannunki ko brush wajen cuccuda hakoran .

-amfani da aswak domin yana taka muhimmiyar rawa wajen sa hasken hakora 

-ga wanda bashida wadatar maclean zai iya amfani da gawayi ya dakashi sai ya dansa gishiri kadan ya wanke bakin 

-kuskure baki da ruwa bayan cin abinci ko abin sha 

-inda hali yin brush akalla sau 2 zuwa 3 a rana 

-Yin brush kafin kwanciya bacci Ina fatan wadannan abubuwa dana lissafo zasu taimaka wajen gyaran hakoranmu. 

 *Hadin amare is now available ga masu bukata.*

 *Yadda muke hadin.*

*Farko maganin*

 *1-infection.*

 *2-Gyaran jiki.*

  *3-Matsalar jinnu.*

*Idan an gama Sai*

*4-Mu fara hadin ni'ima.*

*5-Matsi ga masu bukata.*

*Muna maraba da masu zuwa in Sha Allah.*

*kaduna State.*

Copyright BY: Sirrin rike miji
FACEBOOK GROUP: sirrin rike miji
EMAIL: sirrinrikemiji@gmail.com
FACEBOOK PAGE LIKE: sirrin rike miji
WhatsApp: ☏+2348037538596

Post a Comment

0 Comments