🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎
Yar uwa ki jiƙa abu kaza da kaza kisha domin ki fitar da zaƙin dake mararki kafin naƙudar haihuwa, ko kuwa wane karɓi wannan maganin ka kaiwa iyalinka kace ta jiƙa ta rika sha maganin zaƙi ne.
Wadannan sune irin maganganun da zakaji suna zagawa musamman tsakanin Mata in sun hadu da mai juna biyu. Toh amma fa
::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
Mu alikitance bamu san wani abu wai shi zaƙi a marar Mace ba ballantana fitarsa ajikin Mace gabatowar haihuwa.
Duk da irin wannan al'ada ta jima amma duk da haka mun shigo wani zamani yanzu da gurbatattun labarai da bayanai marasa sahihanci na ilimi suka yawaita kuma ke kai komo tsakanin al'umma cikin kafafen sadarwa iri-iri.
Komi mutane sukaji ba duk ke tsayawa sui nazari da binkice ba akan;
▪︎Shin kaza din nan da akace yama dace dani kuwa?
▪︎Sannan dadin abun aka fada amma menene illar daka iya biyo baya incase?
▪︎Shin hakan ma batun yake a ilmance ko kuwa?
Wannan tasa zarar haihuwa ta gabatowa Mace kowa sai kaga shawara yake bata akan komi ma, Musamman ma atsakaninsu Mata..., Eh munsan kuna yine bisa kyakkyawar manufa da son kuga ta haihu lafiya.... amma fa ba duk yan adam bane zubin halittarsu tare da komi yai daidai dana juna ba.
Ba mamaki wata kukaji tayi irin haka ta wanye lafiya, amma mu tuna fa idan wani yai abu ya kwana lafiya tofa wani in yayi wahala zai sha.
::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
Babu wani abu da sunan zaƙi jikin mai juna biyu, in akace zaƙi ajika tofa mu ko yaushe a likitance abunda muka shina; ana batu ne na ciwon suga ajikin mutum, wato yawaitar sinadarin glucose acikin jini.
Shi ko ciwon suga yayin goyon ciki "gestational diabetes" sunansa, kuma muddin aka ganosa ba'a wata-wata ake dora Mace kan shawarwarin abinci ko magunguna wasu lokutan allura domin bata kariya daga hatsarin suga daka iya tasowa! wanda cikin irin wannan hatsarin akwai mutuwar jariri aciki, mutuwar macen wajen haihuwa, zubewar ciki, ko sanya jariri yai girma fiye da kima aciki ta yadda bazai iya haifuwa ta farji ba saide ai aiki acirosa, ko kuwa sai anqara fadin farjin Mace kafin kan jariri ya iya wucewa.
Wasu kan dauka kowanne katoton jariri lafiya ce tasa, Amma inaa wani girman bana ka'ida bane larura ce, galibi alamace ta larurar suga yayin goyon ciki a uwar musamman a macen da bata rika zuwa awo ba, ko kuwa bata sami duk gwaje-gwajen da suka dace ba, kurum an auna arziki ne. Duk jaririn da nauyinsa ya wuce 3.5kilogram lafiyar mahaifiyarsa abin tuntu6a ce a yayin goyon cikinsa.
Ita kuwa wannan sugar ajini take bazata ta6a fita ta farji koh ta hanyar fitar da wani ruwa ba.
::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
Don haka abunda muka sani na ruwa ajikin Mace dake fara leaking gabatowar haihuwa shine ruwan da ake kira AMNIOTIC FLUIDS wanda kuma wannan ruwane da jariri kan fara taruwa tun daga sanda ciki yai sati 4 inda ake fara iya ganinsa a scanning daga sati 8 na juna biyu.
Wannan ruwan amniotic cikinsa jariri ke rayuwa, yana kuma samuwa ne daga abunda Macen kesha na abinci da kuma fitsarin jaririn. Eh' jariri na fitsari tun aciki wanda shine wannan amniotic din ke taruwa kuma akarshe shine zai shanye abinsa yayin kishirwa da kansa sannan ya qara fitsarar dashi, haka zaita recycling din abinsa duk bayan awa 3, saboda mabiyiya (placenta) dinsa na tace masa shi.
Akullum sai jariri yai fitsari kwatankwacin Moɗa biyu wato 500milliliter.
Wannan ruwan har ila yau da taimakonsa; Jariri ke motsi da juyi aciki, shike taimakawa huhun jariri samuwa, shike sa ciki girma, shike samarwa da jariri kyakkyawan yanayi wato tempreture, saukin naƙuda tare da samuwar cikakkiyar halittarsa ta dan adam ajika ya zamto ba'a haifesa da tawaya ba irin; karamin kokon kai, guntulallen hannu, yamutsatsiyar fata, kayan ciki awaje, dade sauran ababen gudu masu illah.
::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
Toh menene ma yasa ake kiran ruwan da sunan zaƙi ne?
Watakila sakamakon kalar ruwan amniotic din ne da takan canza ya zamo yayi kalar kasa-kasa kamar dafaffen ruwan sikari me kauri shiyasa mutane ke kiransa da ruwan zaƙi tunda yai kalar dafaffiyar sugar amma ba zaƙin ne dashi ba suffarsa ce kurum kamar abun zaƙi a ido. Hasali ma inda mutum zai dandanasa zaiji kamar ďanďanon kori yake.
Ruwa ne da a farkon ciki kalarsa haskene dashi kamar ruwan sha, saide yayin da ciki ya tsufa yakan canza launi sannan yawansa ya fara raguwa ta yadda yake fara fita ayayin da ciki ya gama cika watannin isa haihuwa wato sati na 37, 38, 39, ko 40.
Wannan ruwan yana fara fita alamace ta bakin mahaifar Mace na shirin soma budewa (cervix dilatation) wato naƙuda, wanda hakan ke nuni data shirya cikinta zai fara murdawa (contraction) domin juye lodin dake cikin mahaifarta na tsawon watanni (jariri).
Abun tsoro shine ace wannan ruwan ya soma fita alhalin ciki bai gama cika watanninsa ba koma ace sam ba kusa da watannin haihuwa mace take ba, ko kuwa ace ba haihuwar bace ta gaske, shine ma muke kiran irin wannan mummunan yanayi da premature membrane rupture wanda hakan na nuna za'a haifo bakwaini ko kuwa wanda de bai gama cika halitta ko watannin haihuwa ba. Infact yaron ma na iya mutuwa tun aciki, sannan hakan zai iya barinki da infection me tsanani da zai iya keta mahaifarki yai miki illa ko bayan haihuwa, jo nan gaba zaman wani cikin yai wahala.
::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
Don haka anan nake jan hankalin Matan mu game da wannan kuskuren na shaye-shayen abubuwa da sunan wannan ruwan ya fashe ya rika fita tun kafin lokacin haihuwa bisa tunaninsu na cewa zaƙi ne kuma abune da ya dace afitar don kar ya jawo matsala wajen haihuwa da su daina. Gaskiya karatun ba haka yake ba yadda kuke tunani ko ake doraku akai.
In wannan abun ya fashe alhalin ba nakuda bace ta toh wannan ke iya sa yaro ya maqale wajen haihuwa saide aiwa Mace aiki, kota haihu a wuyace, koma ta haihu jini ya 6alle tazo ita ta rasa ranta, ko yaron ya haďu da infection kwana 1 ko biyu ko ďan sama da haka da haihuwa jariri ya mutu, ko kuwa a haifo yaro ya taso awani dolo-dolo ko shasha saboda wahalar naquda.
Ya dace ai hankali asan cewa yanzu kullum kara wayewa al'ummar duniya keyi, ko a likitance duk minti guda sai wani sabon abu ya 6ullo, wannan tasa hatta bayanai wadu zakuga suna canzawa.
Kuma kema da hankalinki tunda kike zuwa awo wato "antenatal care" kin ta6ajin cewa angano wai kina zaqi a mara? baki ta6a jin ma'aikatan lafiya sunce miki ga wani magani da zaki sha ba saboda ki fitar da zaƙi gabannin haihuwa don gudun matsala... toh ko wannan bai isa ku gane ba.
Inma al'adace aka gada suma kusani cikin duhu suka rikayi, iya iliminsu kenan, sannan rayuwarsu ta bambanta da tamu,
Daga cikin al'ada yau ina al'adar zubar da colostrum wato ruwan nono na farko me ruwan rawaya-rawaya ko zallar madara me kauri da Mace ke fara samarwa bayan haihuwa....! Ko kunsan da iyayen mu matsesa ake azubar ace ai illah ne dashi ba'a baiwa jariri, inma Mace ta kasa matsoshi babbane zaisa baki ya zuƙe mata shi har sai sun tabbatar sun zubar dashi.
Amma bayan binkicen masana akan hakan sai gashi angano ai wannan ruwan nonon da ake zubarwa na farkon yafi duk wani abu da jariri zaici ko yasha inganci, yafi kowanne ruwan nono inganci tare da habbaka lafiyar jariri da basa kariya daga cuttuka. Yau bagashi sai tarihi ba, wasu ma basusan anrika hakan ba abaya.
Kusani wannan ruwan bazai ta zama har abada ba, shi akaran kansa da lokacin haihuwa yazo zai huje ya soma fita wanda hakan shi zaisa bakin mahaifa tauhi ya bude yai santsi yadda jariri zai fita cikin aminc.
:::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
Wannan shine sakon, ku dena shan komi, inkuma anqi toh Allah raba bawa da wahala.
0 Comments