By Jaafar Jaafar -
RUBUTAWA:
Bello Galadanchi
Babu shakka mata dake zaman aure na fuskantar kalubale masu matukar yawa, wadanda ba kowa ne yake fahimta ba. Banda zaman aure da kula da iyali, akwai rashin tabbas na karancin kudaden shiga wadanda zata iya amfani da su wajen taimako, da kyautatawa, da kuma zaman ko-ta-kwana. Babu shakka akwai matan dake da hali, ko suke da maza masu hali. Sai dai fahimtar yadda ake juya nera da kwabo na da matukar muhimmanci wajen takalar kalubalen rayuwa, darajar kudi da kuma nuna irin baiwa da zuciyar da Allah Ya baiwa mata. Saboda haka wannan rubutu zai mayar da hankali ne akan sana’o’in da mata masu karamin karfi dake zaman aure zasu iya yi domin samun arziki da rayuwa mai amfani.
Kafin mu fara lissafo sana’o’i, to ya kamata mu fahimci cewa idan zaki fara sana’a, to ki tabbatar kin amsa wadannan tambayoyin:
1. Wace matsala zaki warware wa jama’a?
2. Ta yaya sana’arki zata rage wa jama’a bata lokaci?
3. Ta yaya harkar ki zata kawo wa jama’a rahusa?
4. Ta yaya zaki banbanta sana’arki da sauran masu yin irinta?
Wadannan tambayoyin sune gimshikin duk wata sabuwar sana’a dake son yin nasara. Idan sana’a baza ta warware wata matsala da ta addabi jama’a ba, to kar ki kuskura ki fara. Ruyuwar nan a cike take da matsaloli da kalubale iri-iri. Duk inda kika duba zaki gani, akwai abubuwa iri-iri dake ciwa jama’a tuwo a kwarya. Mafi akasarin lokaci, mutane suna kashe kudi ne domin warware matsala. Idan har zaki warware wa jama’a matsala, to da gudu zasu dauki kudi su kawo miki.
Sai dai kuma mafi yawancin lokuta, akwai hanyoyin da ake amfani da su wajen warware wadannan matsaloli. Kasancewar mun san wadannan hanyoyi, sai kwakwalwar mu ta toshe, ta yi tunanin cewa baza a iya samo wata sabuwar hanya ba. Wannan ba dai-dai bane. Anan ne nake so ki dan yi tunani, ki kirkiri hanyoyin warware matsala cikin hanzari kuma cikin farashi mai rahusa. Idan kika yi haka, to jama’a zasu yi watsi da daya hanyar da suka saba da ita, domin yin amfani da naki. Wato a duniya babu abunda yake da daraja kamar lokaci. Lokaci ya fi kudi daraja, kuma sai da lokaci ake samun kudi. Idan har zaki rage wa jama’a bata lokaci, to babu shakka zaki samu kudi.
Ba dole sai kin kirkiro sabuwar sana’a ba, a’a, zaki iya duba sana’ar da ake yi kullum, akwai akasi a yadda ake yinta, ko akwai matsala da kusan kowa yake fama da shi bisa yadda ake gudanar da wannan sana’a. Ke kuma idan kika tashi, to sai ki kirkiri hanyar warware wannan matsala tare da rage wa kwastomomi bata lokaci da kashe kudi.
Ga misali. Hajiyata tana da tela da take kaiwa dinki. Telan ya kware, amma kwanaki bakwai yake dauka kafin ya kamalla. Sai dai kuma bayan kwanakin bakwan, telan yakan yi jinkirin kwanaki biyu zuwa uku, sannan ga tsada. Dinkin riga daya na kamawa dubu shida zuwa goma. To idan ke mace ce mai sha’awar dinki, ga dama ta samu. Matsalolin anan sune daukan dogon lokaci, rashin cika alkawari, tsada, da kuma zirga-zirgan zuwa wajen tela. Sai ki kirkiri tsarin da zai warware duk wadannan matsaloli.
– RAGE WA’ADI: Zaki iya tantance kwanaki nawa yake daukar ki gama riga mai wahala, sai ki tsara yadda zaki rage wannan lokaci. Zaki iya dauko matasa ‘yan mata ki rarraba musu bangarori masu sauki na dinkin, ke kuma ki mayar da hankali akan masu wahala.
– KWANTAR DA HANKALI: Zaki iya rubuta takardar alkawari ki saka hannu akai, sannan ki baiwa kwostomarki itama ta saka hannu don ki kwantar mata da hankali. Akan takardar, zaki iya saka sharruda kamar “idan baki kammala dinkin a cikin wa’adin da kika yi alkawari ba, to kar ta biya rabin kudin dinkin”.
– RAHUSA: Idan kuma zaki iya rage kudin dinkin, shima hakan zai kawo miki kwastomomi, sannan zaki iya kara abubuwa da yawa wadanda wasu telolin basa yi. Bai sai kwastoma ta zo wajenki ba, ki ringa zuwa wajenta talla, ki nuna mata sabbanin dinkuna. Ya zamanto kina da “LOKUTAN GARABASA”, inda zaki bada rahusa ta yin amfani da hikima iri-iri kamar “idan kika kawo dinkin atamfofi guda hudu, to na biyar din kyauta ne”, ko kuma a kowane wata, akwai irin dinkin da kike rage kudinsa da kaso hamsin cikin dari. Zaki iya amfani da garabasa wajen tallata sana’arki. Kamar “idan kika saka hotunan kayana da shagona akan shafinki na facebook da WhatsApp, to zan rage nera dubu a dinkinki na gaba.
– TALLA: Idan kina da hali, ki nemi ‘yan wasan Hausa ku tsadance, su saka dinkinki a dauke su a hoto a gidan hoto. Idan ma zaki iya, ku tsadance a dauke su akan bidiyo suna yabon ki, da irin dadin da suka ji wajen aiki dake. Ke kuma ki watsa ta Facebook, da WhatsApp da Instagram. Da gudu zaki ga mata suna rububin zuwa wajenki.
– KAFOFIN ZAMANI: Har yanzu jama’a basu ankara ba da yadda ake amfani da wadannan shafukan sada zumunta wajen bunkasa sana’a. A wannan zamani, mutane sun gaji da talla. Kowa talla yake, kuma a ko ina. Yanzu mutane sun fi mayar da hankali akan mai tallar, ba kayan da yake sayarwa ba. Idan kina da kirki, ban dariya, murmushi mai kwantar da hankali, nutsuwa da rikon amana, to jama’a zasu bada labarinki. Yi tunani mana, sau nawa kika taba ganin wani yace “wai-wai, ashe wannan tsiren yana da dadi haka?”, amma zaki ga jama’a suna rubuta kalamai kamar haka “yanzunnan na rabu da Aminu Maishayi Taraba. Mutumin arziki ne”. Duk wanda ya karanta wannan, zai ji yana begen haduwa da Aminu, sannan yasa a fasa masa kwai da indomie. Kina gani dai Aminu aka tallata ba shayinsa ba, amma harkarsa ce ta samu cigaba. Saboda haka zaki iya amfani da kafofin sadarwa na zamani wajen tallata sana’arki, ta samun mutane su fadi abubuwan alhari dangane da yadda kike rike sana’arki.
Bugu da kari, ya zamanto kina da shafi inda kika tattara duk masu hulda dake. Amma shi wannan shafi ya zama waje ne na gaisawa da tattauna batutuwa na rayuwa, ba talla ko zancen kasuwancin ki ba. Hakan zai sa kwastomomin ki su shaku dake, su kara fahimtar ki, sannan su zama suna gaya wa jama’a labarinki. Wannan shine zai jawo hankulan mutane. Idan daya daga cikin kwastomominki ta samu karuwa, ki bayyana a shafinki, kuma ki yi kira ga jama’a su taya ta murna da Allah Ya raya. In har kina da hali, ki sayo ‘yan riguna ki aika, ki ce wasu daga cikin kwastomomin ne suka bayar a baki. Kar ki so kiga yadda zata ji dadi, ta kara darajanta ki. Game da kafofin zamani, zamu yi rubutu na musamman akai.
– KYAUTATAWA: Daya daga cikin abubuwan da masu sana’a basu fahimta ba a Najeriya shine kyautatawa. Hankalinsu yana kan samun riba. Albishirinki, mance da batun riba na shekara daya. Duk ribar da kika samu, yi amfani da ita ki bunkasa sana’arki ta yadda zaki cigaba da warware wa kwastomominki matsaloli. Idan da kina kammala dinkin riga a cikin kwanaki uku, kuma suna biyan dubu biyar, to idan kika tara riba, a maimakon ki fara tunanin siyan mota ko wayar hannu, a’a, sai ki fara tunanin yadda zaki yi amfani da wadannan kudade wajen kammala dinki a cikin kwanaki biyu, ko ma kwana daya, da kuma yadda zaki rage farashin dinkin zuwa dubu uku, ko dubu biyu da dari biyar. Hakan zai iya yiwuwa ta dauko yara mata ko amare kina koya musu dinki, karawa shagon ki girma, ko mallake wani dan karamin shagon dinki da ma’aikatansa dake cikin matsala. Wani abu da zaki iya yi wanda ban cika ganin shaguna suna yi ba shine kyauta. Idan kika sayi takalma, da mayafai, to duk lokacin da wata kwastoma tayi miki cinikin misali dubu biyar, ko goma, to sai ki bata takalmi ko mayafi kyauta. Wannan ya zama al-adar sana’arki. Kar ki damu da samun riba, ki baiwa kwastoma komai ta yin amfani da hikima. Abunda kike yi shine tallata kanki da kasuwancinki ta hanya mai jan hankali, kuma ba kowa ne yake hakan ba. A cikin ‘yan shekaru zaki tara mutane da yawa.
To jama’a, idan kuka dubi wadannan bayanai, za’a iya daukar hikimomin dake cikinsu a saka a kowace sana’a. Babban abun shine ki warware matsala, ki rage wa kwastoma kudin da take kashewa da bata lokaci, sannan ki jawo hankalin wasu kwastomomin ta hanyoyin da ba kowa ne yake bi ba.
To yanzu ga lissafin sana’o’i da matar aure mai zaman gida zata iya farawa ba tare da jari ba.
1. HAJIYA GOOGLE: Wannan sana’ace ta taimakawa mutane samun abunda suke nema. Misali shine akwai wanda yake so ya sayi mota Honda Accord 2002, kuma yana so ya kashe dubu dari shida, ke kuma sai ki aika sakonni a shafukan Facebook da WhatsApp da Instagram, ki nemi wanda yake da wannan mota kuma yake sha’awar sayarwa. Idan kuka tsadance, to shi kuma sai a nuna mishi mota. Idan tayi, sai ya biya kudinta, ke kuma a yanka miki kwamashonki. Idan kina sha’awar wannan, to ya zamo kina cikin shafuka iri-iri akan Facebook da WeChat. Sai ki rubuta sanarwa kamar haka “Assalamu alaikum. Idan akwai wanda yake son sayar da Honda Accord 2002, ya iya aiko mun da hotunan ta.”
2. KOYAWA MATA DABARUN ZAMAN AURE: Babu shakka akwai matsala a wannan zamani, inda ‘yan mata da yawa da samari basu fahimci zaman aure ba. Akwai abubuwa da yawa kamar rashin tsafta, iya kwalliya, iya girki, iya magana, ladabi da biyayya, da fahimtar yadda namiji ko mace ke tunani. Bisa la’akari da yadda aure yake saurin tarwatsewa a wannan zamani, koyar da zaman aure zai iya zama sana’a mai kyau idan malamar ta tsara shi sosai yadda zai ja hankalin jama’a, kuma ya kayatar da su. Banda darrusa, za’a iya tsara wasannin kwaikwayo, kallon fina-finei ana fashin baki akan abubuwan da suka dace, da wanda basu dace ba, gasar girki, gasar kwalliya da kuma “Certificate” a karshe. Wannan zai harzuka amare kuma jama’a zasu yi marmarin shiga wannan makaranta ko don su ga irin wainar da ake toyawa.
3. RUBUTA KASIDU DA WAKE-WAKEN SIYASA: Ba kece zaki rera wakokin ba, amma zaki iya rubuta su, sannan ki sayarwa mawaka, ko wasu ‘yan siyasan dake kaunar wanda kika rubuta wakar akan shi. Misali shine Mallam Bello babban dan siyasa ne. Mallam Aminu yana kaunar Mallam Bello. Idan kika rubuta waka akan Mallam Bello, to zaki iya tallatawa Mallam Aminu, ko wani mawaki ya rera ta don ki sayar wa Mallam Aminu ko Mallam Bello. Idan zaki rubuta wakokin da kalmominsu sunyi fice, ba kamar wadanda muke ji kullum ba, to kuwa zaki samu kasuwa. Idan zaki iya baiwa mutane dariya da farin ciki da wakokinki, to ‘yan siyasa zasu yi ta aiko sakonni.
4. FRUIT SALAD: Wannan sana’a ce mai sauki, kuma ba kowa ne yake yin ta ba. Ki fara da makota, da ‘yan uwa. Kina aika musu, suna sha. Ki share makonni kina yi, idan har akwai dadi, to zaki ga jama’a sun fara kwankwasa kofa. Sirrin shine ki zuba lemo irinsu 5 Alive da Tang a ciki. Dan adam yana son zaki.
5. HADA DARASI: Idan kin kammala karatu, to zaki iya zama mai hadawa malamai darasi. Idan kina da na’ura mai kwakwalwa, to sai ki yi amfani da ita wajen kasafta lokacin darasi da abubuwan da za’a koya. Idan kin iya wannan aiki, to zaki iya daukar malamai suna koyarwa a kofar gidanki, ke kuma kina neman dalibai a WhatsApp da Facebook. Ki biya malamin albashi, ki yanki naki rabon. Idan kin tara kudi, to sai kiyi hayar waje, ki nemi rijista, ki yi hayar manager ya zama principal.
6. MAI NEMAN ASALI: Akwai jama’a dake so su san asalin iyayensu da kakanninsu. Idan kina da wannan baiwa, to ki mayar da ita sana’a.
7. RUBUTA TATSUNIYOYIN YARA: Me zai hana ki rubuta tatsuniyoyin yara? Ai babu wahala, ki tantance yara ‘yan shekaru nawa zaki rubutawa, me iyaye suke kokarin koya musu a wadannan shekaru, sannan ta yaya zaki yi amfani da hikima wajen rubuta labari mai dauke da wannan batu?
8. MALAMAR QUR’ANI: Zaki iya zama malamar mata. Ba dole sai yarinya mace taje wajen malami na miji ya koya mata karatun Qur’ani ba. Ki bude makaranta a cikin gidanki, kuma dalibai su ringa biya awa-awa. Zai iya kasancewa su dauki karatun da za’a share sa’o’i 30 domin kammala izifi biyar. Za’a ringa zuwa makarantarki sau biyu a mako, kuma karatun sa’o’i biyu za’a ringa yi. Zaki iya karbar dari 2 duk sa’a daya, saboda haka dari 4 kennan kowace ranar karatu. N800 a mako, N6,000 na sa’o’i 30. Idan kina da dalibai biyar, kinga zaki tashi da N30,000 kennan. Shin akwai abunda yafi samun kudi da lada a lokaci guda?
9. KULA DA ‘YA’YAN MUTANE: Idan kina da gida mai tsafta, to zaki iya kafa sana’ar kula da yara idan iyayensu basa nan, ko suna bukatar hutu. Mata masu aure sau da dama suna fuskantar kalubale daga kananan yara, wani lokacin har bacci ma gagararsu yake. Idan kin iya muamalla da yara, to wannan sana’arki ce. Itama awa awa za’a ringa biyan ki.
10. MARUBUCIYAR JAWABAN SIYASA
11. GWANJO
12. KULA DA TSOFAFFI
13. DINKIN HULA
14. HADA TAKALMI
15. RUBUTA LABARAN SOYAYYA
16. KWALLIYAR MATA
17. HADA AURE: Idan kin san mutane da yawa da halayensu, musamman zawarawa da maza masu neman aure, to zaki iya hada su, su kuma su biya ki.
GARGADI: BABU BASHI! BABU BAYAR DA BASHI!!! BABU BASHI!!!!!!!! MASOYINKA BAYA KARBAR BASHI A HANNUNKA!!!! MASOYINKA NA SO KA CIGABA, SABODA HAKA SHINE MUTUM NA FARKO DA ZAI BIYA KA DON KA BUNKASA SANA’ARKA. BABU BABU BABU BABU BASHI!!!! GWAMMA AN BARKI DA KAYANKI, DA KI BADA BASHI.
0 Comments