@~~~~~--______--~~~~~~@
Saukar Jini yai kasa wannan shima wani yanayi ne da wasu mutanen Kän tsinci kansu kamar yadda ake samun hawan jini (High Blood Pressure) to shi kuma ana kiransa (Low Blood Pressure) wato karsashin dake cikin jini in yayi kasa. Ana gane cewa karsashin jini yayi kasane a yayin da ya kasance ya nuna casa'in bisa sittin na karfin bugawar jini cikin babbar jijiyar dake daukarsa zuwa Zuciya (artery) a ma'aunin karfin jini (90/60 mmHg) da ake kira *Spygromanometer* a turance.
SHIN SAUKAR JINI KA IYA SA NAKE FAMA DA CIWON KAI
Ciwon kai baya daya daga cikin fitattun alamun saukar Jini ajika Saidai yanayin matsi da jiki ya sami kansa ka iya sa arika jin wasu alamu dake da alaka da kai kamarsu; Jiri, jin nauyi, ganin duhu-duhu, da rashin son haske ko yaushe.
Acewar wata kungiyar lafiya ta (Health lines) ta kara da cewa mai Larurar kanyi fama da tashin Zuciya, damuwa, yaushin fata, da rashin sukuni.
ABUBUWAN DAKE KAWO SAUKAR JINI!!!
Ba abubuwa ne dako da yaushe zaka iya cewa sunyi fice wajan kawo hakan ba saidai akan alakanta su da shi;-
- Juna Biyu (pregnancy) duba da yadda aka tabbatar da ba abunda ke zuke jini ajikin mai juna biyu kamar jaririn dake cikin.
- Sauyin sinadaran halitta dake jika wato walau su Karu ko sui kasa abisa yadda da suke. Musamman sinadaran sarrafa abinci ajika.
- Ciwon suga. Ko
- Idan ya zamto kuma sikarin dake jiki yayi kasa.
- Yawan magungunan da ake ganin koba da umarnin likita ba kowa yasan aikin su irinsu (vitamin A, C, Paracetamol, Procold) ds.
- Idan ya kasance mutum yana Kän shan magunguna da likita ya dora shi irin na hawan jini, na rashin bacci, tsarin iyali, ko na kuturta.
- Matsalar tsukewar jijiyoyin jini.
- Larurar data shafi bugawar Zuciya.
- Toshewar hanyar jini acikin Zuciya.
- Sai Ciwon Hanta.
ALAMOMIN LARURAR!!!
A wasu mutanen saukar jinin kai tsaye kanyi nuni da cewa akwai wata matsala tattare da jiki a karkashin kasa da ba'a San da ita ba, musamman kuma inya hado da wadannan alamun;-
°- Ganin Jiri.
°- Ganin duhu-duhu.
°- Rashin Samun nutsuwa.
°- Ganin daya a biyu.
°- Jin tashin Zuciya akai-akai.
°- Matsanancin jin sanyi.
°- Dashewar fata.
°- Jan numfashi da sauri-da-sauri amma kuma yana fita kadan.
°- Yawan Kasala ko Laulayi.
SHIN SAUKAR JINI NASA JIN GAJIYA??
A ainishin hypotension kadai baisa gajiya ko kasala amma idan ya zamto akwai matsaloli da suka sa kwayoyin cuta suka shiga ciki, ko karancin ruwa ajika (dehydration) ko ciwon da ya shafi Zuciya to akan rika jin kasala da rashin karfi da kuma zazzabi tabbas. Idan ko haka ta fara faruwa to lalle mutum a asibitin ma yana bukatar sashin kulawa ta musamman (ICU).
ME ZAISA NA GANE JINI NA YA SAUKA???
Yakan bambamta daga jiki zuwa jiki amma de matukar na'urar awo ta nuna jininka (90/60) mmHg ko kasa da wadannan numba Tofa lallai karsashin jinin ka yayi kasa.
MENENE MAFITA???
Mafita shine zarar aka ga haka Toh jami'in lafiya zai kara binkice Sannan ya sama ruwa mai dauke da sinadarin gishiri (sodium) domin taimakama jikinka ya dawo normal tare kuma da yan magunguna ko allurai da jikin zai bukata.
ALLAH YA SA MUI YININ JUMA'A LFY AMEEN!!!
*{Ibrahim Y. Yusuf}*
Don neman Karin bayani akan hypotension zaku iya bin Wannan link http://www.zocdoc.com
0 Comments