Tasirin Yabo A Zamantakewar Aure:




  
Yabo
Daga Walida Ahamad Suleja,

Hakika son yabo da jinjina yana cikin dabi’ar dan’adam. An halicce shi tun usuli da son wannan dabi’iar. Hakika yabo yana taka muhimmiyar rawa a dukkanin zamantakewar mutane.A sakamako yabo wasu ragwayen mutane sun zamanto masu kokari da kyautata aiki. A sakamakon yabo masu yanke tsammani sun zamanto masu karfin gwiwar cim ma muradansu. A sakamakon yabo wadanda aka kusan cin su da yaki sun zamanto masu juriya da dagewa.

A gefe guda kuma,da zaran mun kalli tsarin koyo da koyarwa zamu ga yana bayar da gudummowa mai karfin gaske ga Dalibai a makarantunsu. A yayin da aka zo zangon karatu na karshe, wadanda suka samu daraja ta farko ana faranta zukatansu da kyatattun kyaututtuka domin su kara kwazo. Haka wadanda ba sa dagewa a kan darasin su sukan zamanto masu dagewa da karsashi da sa ran yin nasara a dukkanin darussan su.


A cikin alkur’ani mai girma za mu ga a wurare daban-daban Allah ya yabi Annabawansa da Salihan bayi wadanda suka shiryatar da al’umma su ka kaisu tundun tsira.

Yabo wani abu ne da mafiya yawan mutani su na son a yabe su a yayin da suka yi wata bajinta ta rayuwa.

sai dai kuma a kan samu mutanin da yabo bai dame su ba,da a yi da kar ayi duk daya ne a wajen su.Sannan akwai mutanin da su basu, damuwa idan an yabe su,amma dai su na so a yaba musu din,hakan kuwa bai rasa nasaba da yadda ruhinsu ya ginu a kan iklasi da yin komai saboda Allah.

Wannan kuwa haka yake a cikin mutane, da ke ba muna magana ne akan asalin shi yabo din ba,ballantana mu yi dogon sharhi akan shi,sai dai mun dan taba wadannan bayanai ne domin a kara fahimtar yabo din.

Yanzu za mu shiga cikin asalin abunda muke so mu yi magana a kan shi

Wato TASIRIN YABO A ZAMAN TAKEWAR AURE.

Mu mata akwai mu da son nuna burgewa da bajinta, to idan mun nuna hakan muna da son a yaba mana musamman idan muna ganin mun yi abun burgewa ko da kuwa, bamu burge din ba to muna da son muji yabo daga bakuna mazajenmu.

Hakan abu ne mai kyau da ya kamata ma aurata su kula dashi. Duk lokacin da matarka ta yi wani abun burgewa kamata ya yi ka yaba mata, hakan zai sa ta kara jin dadi da kaunarka a zuciyar ta, kuma tasan cewa har yanzu soyayyar nan bata gushe ba ta na nan kaima kana kaunarta. Soyayyarka za ta kara yi ma ta tasiri,zai yi wahala ta mance da wannan yabon ko shekara nawa ne.

Misali mace ta na da son idan tayi kwalliya mijinta ya yaba ko kitso ko sabon dinki, kai hatta ma da girki.A yayin da miji ya debi girki har ya yi santi,a nan ya kamata ya bayyana yabonsa ga matarsa wacce ta dafa abincin ko ta kula da dafawar.

Ko da kuwa ta yi kuskure wani abu ya zarce a cikin girkin kamar yaji,gishiri akwai bukatar a yaba sannan daga baya sai a yi gyara cikin nutsuwa.

Da farko mai gida sai ya ce lallai yau girkin na musamnan ne, da ma ba kullum ake kwana a gado ba, kuma ba wadda zai ce ba ya kuskure, daga baya sai ka nuna mata kuskuren ta, insha Allahu za ta dauki wannan magana ta ka, kai ma sai ka kara kima da daraja a a idon ta.

Akasarinmu Hausawa ba mu dauki matarmu dan ta yi mana abun burgewa, mu yaba mata ba wanda hakan ya yi dalilin mutuwar aure da yawan gaske a kasar Hausa.

Alhali yabo yana daga cikin wani jigo na Soyayya.

Akwai Matar da ta taba cemin, ita ta na da yawan son juya fasalin dakinta ta jujjuya kujeru da sauran kayayyakin dakin nata,ta ce,duk sadda na juya mijin nawa ko ya gani ba ya cewa komai, kuma dan shi nake yi, ya gani ya ji dadi.


idan ya ga na gyara din zai yi ta kallon dakin kawai ne ba tattare ra ya yaba ba wanda ni kuma bana jin dadin hakan.

Amma ko irin yace yau kin sha aiki, ba zai ce mani ko uffan ba.

Ko a jikin shi wai an naushi kakkausa!

Ta ci gaba da cewa

hakan da ya ke yi na ko in kula, sai jikinna ya yi sanyi a kan haka, rabon da na sake juya dakina na dade.

Nake ce ma ta, tun da abu mai kyau ne kuma ba cewa ya yi ba ya so ba,

kuma ya na nuna jin dadin shi to, ki daure ki ci gaba da yi.Ko bai bara ba, ladanki na wurin Allah.

Mazajenmu masu girma ya kamata i dan muka nuna bajinta, a rika yaba mana, duk da wasu mazan su na ganin shi a kawai wani abu ne can daban wadda ba dole ne ba.

Haka ne ba dole ne idan matarka ta yi abun burgewa ka yabe ta ba.

amma dai yin hakan ya na da amfani.

Wasu mazan kuwa Matar gida ce ba za su yabe ta ba, sai matan waje hakan kuma bai dace ba.

Matar gida ita tafi cantanta, ayaba mata ba ta waje ba ko wacce ake so a auro.Koba komai, shima wani nau’i ne na soyayya, kuma mu fatanmu a ko da yaushe a rika inganta abubuwan da zasu rika kawo mana zaman lafiya a zaman takewarmu ta aure.

 

Kuma kema uwargida a rika nuna wa maigida ya burge da kuma yabon shi, ko dan abu ya sayo ya kawo gida, ko kaya ya saka sabo, ke har ma da tsohon kaya ki rika nuna mishi ya na burgeki kuma ya na kokari.

 

Dan abu kadan da muke renawa a zaman aure sai ya jawo matsalar da zata haifar da rabuwar aure gaba daya.

Wani abu kuma da nike son tunasar da mu a nan shi ne,shi yabo yana barin tasiri mai girman gaske a zuciyar masoya,don haka ya zamanto wajibi mu rika aiwatar da shi domin samun inganci da dorewar zamantakewar aure.Allah ya sa mu amfana,sai mun hadu sati mai zuwa insha Allahu.

Post a Comment

0 Comments