yadda ake kasuwancin social media:




By sadeek sadboi
 

Yadda zaka zama dan social media ko kasuwanci a social media.

Kasuwancin social media abu ne mai karfi sosai kuma yana dacewa da ko wane irin kasuwanci kakeso kayi domin samun customers.domin daman chan customers dinka suna harkalla tare da wasu kamfanoni a cikin ita social media din.amma idan baka fitowa fili ka tallata hajarka a irin su facebook ,twitter,instagram,pinterest da sauransu toh gaskiya a zamanance kana rasa babar dama.

Kasuwanci mai inganci a cikin social media yana iya kawo babbar nasara a rayuwa da kuma shi kanshi kasuwancinka din.domin yana bunkasa kasuwanci sosai idan har kana yinshi yanda yakamata.

Menene kasuwancin social media:

Social media marketing yana nufin wani irin kasuwanci ne wanda ake yinshi a internet wanda ake kirkirar rubuce rubucen bayanai da kuma rarraba su a cikin social media domin cinma burin kasuwanci da sauransu.kasuwancin social media ya kunshi abubuwa kamar posting din hotuna ,bayanai da sabuntawa tare da bidiyoyi da kuma sauran abubuwa dake jawo hankalin mabiya ko customomi.

Mun kirkiri wannan tutorial din ne domin mu temaka wajen baku introduction din kasuwancin social media a matsayinka na dan koyo.mun hado shawarwari da kuma training wanda ya kamata domin bunkasa kasuwancinka.

Tare da wadannan shawarwari ne zaka iya gina plan dinka na kasuwancin social media.

Ka fara a zabar plan
Kafin ka fara shiga cikin tsarin tun farko ya kamata ace ka tsara irin nasarar da kakeso ka samu.

Domin fara kasuwancin babu tsari yakan iya baka matsala amma akwai wasu tambayoyin da zaka tambayi kanka kafin farawa.

-wane irin buri kakeso ka cinmawa a cikin kasuwancin social media.

–su waye customers din da kake targeting

–ina customers dinka suke kuma taya suke amfani da social media.

–wane irin sako zaka turawa mabiyanka.

Yadda social media zata temakeka don ci gaban kasuwancin ka.

Kasuwanci social media zai temakeka da abubuwa kamar haka.

-karin yawan jamaa a website

-gina zantuttuka

–tallar sabuwar haja

-samar da ilimin sanin sabuwar haja

-karfafa zantuttuka tsakaninka da mabiyanka.

Iya yawan adadin mabiyan da ka samu a social media ,iya yawan adadin yawan nasarar kasuwancin da zaka iya ci kenan.

Shawarwari game da zama dan social media
-social media content planning:kamar yanda nayi bayani a baya,yin plan kafin faraway yanada vamfani sosai .kayi keyword research kafin ka fara domin ta hakane zaka iya sanin wane abu ne customers dinka suke bukata.

-great social media content: content yana nufin duk wani abu da zaka saka ko ka dora a social media flatform dinka, kuma hakan shine babban jari ga bloggers da kuma yan social media.ka tabbata ka bayar da bayanai masu inganci kuma karinga posting akai akai .ka bada bayanai wanda ya kunshi abinda mabiyanka suke bukata.abubuwan da zaku dora a social media sun kunshi irinsu bidiyoyi,hotuna da sauransu da makamantansu.

-a consistent brand image:amfani da social media domin kasuwanci yana sa ka amsa sunanka a matsayin dan kasuwa na social media kuma da nuna banbanci tsakanin sauran kamfanoni.a yayinda ko wannensu yanada irin nasa sunan da kuma irin services din da suke badawa.

Social media for content promotion; hakan yana nufin social media wata babbar tasha ce wadda zaka iya rarraba watau sharing din bayanan ka wanda kake sabuntawa daga blog zuwa masu karantawa.da zarar ka gina babbar kafa a social media toh zaka iya posting din duk wasu sabbin abubuwanm da kayi posting a blog dinka ko kuma abubuwa sabbi da suka samu.domin tabbatawa da makaranta sun karanta.

-sharing curated links: a yayin da kake amfani da social media yakamata ace kazamanto unique vta hanyar rarraba link.domin ta hakan ne zaka samu manyan followers da kuma fans,ta hakane mabiyanka zasu rinse samun bayanai daga gareka masu amfani.

Tracking competitors: bibiyar abokanan kasuwancinka yanada kyau sosai domin zasu baka damar samun bayanai irinsu keword reaserch da kuma Karin ilimi wajen sanini makamar aiki.sannan kana iya binciki wane irin tsari ne suke bi domin suyi aiki toh kai ma kana iya gwadawa ko zai iya yi maka aikin kaima.

Yadda zaka zabi social media platform domin kasuwanci
Ta hakane zakusan wasu yan abubuwa game da hanyoyin da zakusan ta yanda ake zabar irin social media din daya dace kuyi amfani das hi kuma da yanda ake amfani dashi.

Amfani da facebok

Facebook yana daya daga cikin manyan platform a duniya a yayinda yake bukatar strategies.step din farko anso ka bude facebook fan page domin bunkasa kasuwanci.domin facebook kamar waje ne wanda zakaje kayi relaxing kuma kayi chat da abokananka.domin ta facebook fan page zaka iya samun miliyoyin likes domin bunkasa blog post.

Amfani da google+
Google+ shine yake biyo facebook a wajen mabiya a duniya.sai dai google plus ba kowa yake yiwa aiki ba amma kuma wasu suna jin dadinsa. Saboda tare da google plus kana iya sharing din vidseos, links,audio da sauransu.kuma hakan ne zai baka damar samun followersa da dama.

Amfani da pinterest
Pinterest yana daya daga ciklin platforms masu tasowa a social media a yayin da kowa zai iya amfani dashi domin gina customers page dinsa domin ci gaban kasuwanci.pinterest yana barin yan kasuwa domin bu baje hajarsu a kansa.sannan kafin ka fara a pinterest yakamata kasan audience din da zakayi targerting domin yawancin masu yinshi mata ne.

Amfani da youtube

Youtube shine na farko wajen saka da rarraba bidiyoyi sannan kuma tool ne a social media mai karfin gaske.domin yawancin yan kasuwa suna amfani dashi domin bunkasa kasuwa.saboda mutane da yawa suna hada video da kansu wanda ya kunshi kalar kasuwancinsu.sannan yawancin videos na how-to suna da damar samun ranking a google search.

Amfani da twiter

Twitter platform ne wanda zai iya bari ka saka duk abinda kakeso bangaren abinda kakeso kayi promoting.tweets masu yawa zasu saka ka ka bunkasa abinda kakeso ka cimmawa domin ta twitter zaka iya saka labaran sabbin abubuwan da suka fita da ragin kaya da dai sauransu.sannan kana iya saita twitter ads domin kabiyasu su dinga yi maka talla da kansu kamar yadda suma facebook sukeyi.

please share and comment.

Post a Comment

0 Comments