MU KASANCE A TARE DA JUNA:
"A duk inda kika je ki tabbatar da cewa ina biye da ke, ko da ban zo a zahiri ba to kuwa zan zo miki a cikin bacci, ke ma za ki bayyana a cikin mafarki na, mu kasance a tare da juna, cikin wani lambu mai cike da furanni mabambanta launi. Begenki shi ne abun yina a kullum. "
KO KIN SAN DA CEWA:
"A lokuta da yawa, kalmomi sukan gagari furtawa, domin bayyanar miki da adadin yadda sonki yake kara mamaye zuciya ta a kullum. Bana fatan zuwan ranar da zan gaza wajen nemo kalmomin da zan furta miki cewa INA SON KI. Hmm! Karda Ki Manta Da Ni a Rabon Naman Sallah. Barka Da Babbar Salla Masoyiya ta."
KE TA DABAN CE:
"A lokacin da na fara ganinki, sai da na rintse idanuwana domin fahimtar cewa, shin a zahiri nake ganin ki, ko kuma kawai kin gifta ne ta cikin tinani na. Lallai ke din ta daban ce, kina da wata baiwa wadda ba kowa ne zai gane hakan ba, daga ciki akwai ta zazzakar murya da tattausan murmushi. ina kaunarki"
INA SON ABUBUWA UKU:
"Ina son wasu abubuwa guda uku a rayuwata:- Rana da wata sai kuma mafi soyuwa daga cikinsu a gare ni shine ke. Ina son rana ne domin ta haskaka mini safiya, ina son wata domin ya haskaka min dare, ina sonki ne domin mu rayu tare har abada. Barka Da Babbar Sallah Masoyiya ta."
AMINCE MU RAYU TARE:
"Ke tauraruwa ce a cikin duniya, haka kuma ke duniya ce ga wani tauraro, zan so ki amince mu rayu a tare cikin shauki da ‘kaunar juna. Hmm! Zan kuma zo na kar6i nawa naman sallar. Barka Da Babbar Sallah. "
0 Comments