Matsalar amai ko tashin zuciya ga mata masu ciki matsaloli ne dake haifar da damuwa ga mata masu ciki. Juna 2 na daga cikin ababen dake sa yawan tashin zuciya, zubar da miyau dama aman musamman aman safe.
Dan magance wannan yanayin akwai dubaru 3 dana fito dasu wadanda ka iya magance matsalar a samu sauki.
1- Amfani da magunguna na prenatal vitamins magunguan da ake sha na mata masu ciki na matukar tsakaita amai da tashin zuciya.
2- Amfani da magungunan tsaida amai da tashin zuciya wadanda ake iya anfani dasu lokaci zuwa lokaci daga likita idan bukatan hakan ta taso.
3- Kaucewa sha ko anfani da duk abunda akasan yana tada zuciya ko sa amai kamar abinci, magani da sauransu.
HAR ILA YAU DAN TSAKAITA AMAI A GIDA Musamman mata masu ciki dake yawan aman safe.
A rika anfani da toast, cereal, crackers, ko sauran dry foods kafin tashi daga gado.
A Rika anfani da cheese, lean meat, ko kuma sauran high protein snacks kafin kwanciya dama shan fruits.
0 Comments