𝐌𝐄𝐍𝐄𝐍𝐄 𝐌𝐀𝐇𝐈𝐌𝐌𝐀𝐍𝐂𝐈𝐍 𝐌𝐀𝐂𝐄 𝐓𝐀 𝐇𝐀𝐈𝐇𝐔 𝐀 𝐀𝐒𝐈𝐁𝐈𝐓𝐈, 𝐒𝐇𝐈𝐍 𝐇𝐀𝐈𝐇𝐔𝐖𝐀𝐑 𝐆𝐈𝐃𝐀 𝐍𝐀𝐃𝐀 𝐖𝐀𝐓𝐀 𝐈𝐋𝐋𝐀𝐇 𝐍𝐄?:



🏥🏥🏥🏥🏥🏥🏥🏥🏥🏥🏥🏥🏥🏥

Mutane da yawa ayau sunfi damuwa da kudi akan lafiyarsu, har sai in lafiyar ta kucce asannan ne suke gane annabi ya faku kuma suke jin sun shirya biyan ko nawa ne inde zasu samu lafiyarsu ta dawo jikinsu. 

Duk sanda akace haihuwa a asibiti gani ake Mace ta tarkowa miji aiki, ammq fa ya kamata mugabe ayanzu aduniya komi ya canza hatta cuttuka yanzu anfi fama wannan tasa irin haihuwar da iyayen mu sukai abaya suka wanye lafiya wajibi ne ayau mu fahimci cewa bazafa ta yiwu ba inkuwa ba haka ba toh gara karkai aure kurum matukar baka shirya dawainiya ba.

Haihuwa har gobe nada cikin ababen da bamu dena rasa mata adalilinta ba, muna rasa mata da ayawa kafin da kuma bayan sun haihu adadi me yawa bana wasa ba.

𝐒𝐇𝐈𝐍 𝐌𝐄 𝐊𝐔𝐊𝐀 𝐅𝐀𝐇𝐈𝐌𝐓𝐀 𝐃𝐀 𝐇𝐀𝐈𝐇𝐔𝐖𝐀 𝐋𝐀𝐅𝐈𝐘𝐀

■ Abu na farko de nakeso kowa yasani shine: Ba’a cewa anhaihu lafiya har sai anyi kwana arba’in da haihuwar lami lafiya sannan. Domin abubuwa da yawa na biyo bayan haihuwa wanda duk wata matsala da zata sami Mace kasa da kwana 40 ka iya alaka da haihuwar.

■ Abu na biyu: ita Haihuwa ba yadda za ayi a hankalci cewa za’a baza ata6a samun matsala da ita ba.

■ Abu na uku; a asibiti ne kurum ake da ma’aikata kwararru wadanda sukasan matsalar haihuwa idan tafaru, ko inzata faru tun gabannin nakuda.

Wannan tasa idan aka Haihu ko aka fara Nakuda a Gida matsala tana iya faruwa yanke take bayan haihuwa... wacce ba wanda zai iya ya fahimceta har sai tayi qamari anga ta fara yiwa rai barazana sannan ace za'a nufi Asibiti yadda in anje asibitin ma a lokacin an makaro domin sakamakon kan zamo abu bamai dadin ji ba. 

𝐒𝐀𝐈𝐃𝐄 𝐇𝐀𝐑 𝐆𝐎𝐁𝐄

Mu a Al’adun mu idan mace bata Haihu agida ba ana ma ganin hakan kamar naqasa ce, ko gajiyawa... idan mafa haihuwar tazo da matsala kenan... Ballantana ace kurum Mace ce ta karfafi miji akan ya taimaka ya kaita ta haihu a asibiti ai gani ake ta jajubo masa wahala da asarar kudi.

Wanda wancan mugun tunanin zaisa tursasawa Mace taga tayi iya kokarinta ta haihu a gida... batare data yi la’akari da hatsarin da take sa kanta da kuma jaririnta gami da rayuwarta a ciki ba. 

Duk da irin wannan matsalolin na baiwa haihuwa mahimmanci ko daukarta abu me hatsari wasu lokuta kan taso daga mazajen ko kuma yan uwansa koda mijin nason yi inda zasuke hanashi suna masa kallon za'a sashi wani abune na asarar kudade😰 batare da ganin girman kyautar haihu da Allah ke shirin masa ba wacce ba'a saya akasuwa.

○☆○☆○☆

Hakika ba’a son nakuda ta wuce Awanni goma sha biyu wato rabin yini batare da anhaihu ba... kuma ya kamata a gane cewa, mai ciki zata iya samun ciwo wanda ita agunta nakuda ce, amma idan aka zo asibiti sai aga ba nakudar bace..., 

Shiyasa zakaji wasu suna cewa sun yi kwana hudu ko biyar suna nakuda, kuma sun haihu lafiya, ba nakuda kukai ba... kuma zama.aki daukar hakan da mahimmanci kan jawo bayan haihuwa wasu suke fusakantar larura ta yoyon fitsari.

𝐈𝐋𝐋𝐀𝐑 𝐃𝐎𝐆𝐔𝐖𝐀𝐑 𝐍𝐀𝐊𝐔𝐃𝐀 𝐁𝐀𝐓𝐀𝐑𝐄 𝐃𝐀 𝐙𝐔𝐖𝐀 𝐀𝐒𝐈𝐁𝐈𝐓𝐈 𝐁𝐀

Kamar yadda nace ba'a so nakuda ta wuce awa 12... To idan nakudar kuwa ta wuce awanni 12 matukar itan ce da gaske kuma ana jibge agida anata bankawa Mace jike-jike toh jaririn da uwar suna iya shiga wani Mugun hali 

𝐀𝐛𝐮𝐛𝐮𝐰𝐚𝐧 𝐝𝐚𝐤𝐞 𝐬𝐡𝐚𝐟𝐚𝐫 𝐣𝐚𝐫𝐢𝐫𝐢 𝐝𝐚𝐥𝐢𝐥𝐢𝐧 𝐡𝐚𝐤𝐚 𝐬𝐮𝐧𝐞:

▪︎ Irin wannan ne zai janyo kaga anhaifi jariri babu rai, ko kuma 
▪︎ Jaririn dakan fama cutar farfadiya arayuwa, 
▪︎ Ko aga yaro ya zama wani susu-su ko wawa wawa haka saboda matsin da kwakwalwarsa tasha 
▪︎Haifo yaro da ciwon zuciya
▪︎ Sannan idan wadancan basu sami yaro ba... toh zaima iya tashi dakiki.

𝐀𝐛𝐮𝐛𝐮𝐰𝐚𝐧 𝐝𝐚𝐤𝐞 𝐬𝐡𝐚𝐟𝐚𝐫 𝐮𝐰𝐚𝐫 𝐝𝐚𝐥𝐢𝐥𝐢𝐧 𝐡𝐚𝐤𝐚 𝐬𝐮𝐧𝐞:

■ A bangaren uwa wato me dauke da cikin mahaifarta (uterus) zata iya fashewa wato rupture idan tsohuwar haihuwa ce, ma'ana wacce tai haihuwa sama da uku abaya wanda hakan zai sa ta mutu dalilin zubar da jini.

■- Idan kuma haihuwar fari ce zata iya haduwa da larurar yoyon fitsari, wato ya zamto bata iya rike fitsari daga baya. ko

■- Ta hadu da larurar yoyon bayan-gida (encopresis) ya zama kashi na zubowa kai tsaye bata iya rikeshi ta dubura.

■- Ko kuma kin harbawar mahaifa ya zamto bayan ta haihu ta cigaba da zub da jini (uterine atony) wanda zai iya kaiwa ta rasa ranta, bayan ana murna ta haihu lafiya karshe akoma kuka kamar yadda muke gani.

■- Ko abunda ake kira uwa-bata-biya ba wato (uterine inversion) koma aga mabiyiyar ta zazzago manne hade da mahaifar ta tiďo ta bullutso ta farji wanda nan ma mace ka iya mutuwa dalilin zub da jini... galibi ma saide a garzaya da mace emergency operation ayanke mahaifar baki daya inba haka ba bau ta yadda za'a iya shawo kan zubar jinin wanda kuma ita da haihuwa shikenan... baya ga dumbin matsaloli da canji da jiki zaita samu rashin mahaifar.

𝐃𝐔𝐊 𝐒𝐀𝐍𝐃𝐀 𝐀𝐊𝐀𝐂𝐄 𝐍𝐀𝐊𝐔𝐃𝐀 𝐀 𝐆𝐈𝐃𝐀 𝐓𝐎 𝐃𝐀𝐘𝐀𝐍 𝐁𝐈𝐘𝐔 𝐍𝐄:

Idan mace tayi nakuda a gida cikin abu biyu ne; 

1- Tana iya haihuwa lafiya ba wata matsala saide bayan kwana biyu tadan fuskanci zazzabi da ciwon ciki... ko kuma ta haihu lafiya amma matsala ta taso daga baya musamman sepsis wanda in a asibiti ne ana lakanta bada magani... kuma wannan shikesa aga da yawa masu jego sun mutu kafin suna ko bayan suna alhalin lafiya suke.... kuma abune kalilan ya jawo mutuwarsu wanda da a asibiti ne da kila ba'a kai ga hakan ba.

2- Ko kuma ta haihu lafiya amma nan da nan abu ya rikice jini ya 6alle dole a taho asibiti gadan-gadan.
Ko kuma azo haihuwa abun ya gagara saboda da akwai matsala aboye da aka kasa agane da wuri, wanda ba lokacin da za’a zo asibiti kuma ta GALABAITA, sannan kuma a karshe ko arasa ta, ko arasa jaririn dake cikinta, ko arasa su duk gabadaya. 

𝐇𝐀𝐈𝐇𝐔𝐖𝐀 𝐁𝐀 𝐖𝐀𝐒𝐀 𝐁𝐀𝐂𝐄 𝐀𝐋'𝐔𝐌𝐌𝐀

Tafi dukkan wata matsala da zaka hararo girma, yanzun nan murna saita koma kuka😰 musamman 𝒔𝒕𝒂𝒈𝒆 3 𝒐𝒇 𝒍𝒂𝒃𝒐𝒓 wato bayan haihuwa wajen fitowar placenta shine stage mafi hatsari bama haihuwar ba.

Wannan tasa ko yaushe muketa ilmantar da mutane mahimmanci tura mata awo wato PRENATAL VISITS tun daga lokacin da ciki yakai watanni 4 ko 5 saboda su fara samun kulawar jami'an lafiya ta yadda inma akwai matsala za'a ganota da wuri a dau mataki yadda za'a tsara mata hanyar da zata bi ta haihu lafiya....

𝐓𝐎𝐇 𝐀𝐌𝐌𝐀 𝐅𝐀

To ammafa ayanzu matan na zuwa awo ba laifi, saide zuwa haihuwa asibitine sai yan kadan ke yin hakan. Ya kamata kowa yasani haihuwa ba baiwace data shafi masu kudi bafa kurum, inde Allah zaima wannan baiwar to wajibinka ne yin komi domin baiwa iyalinka kulawa koda kuwa suke nan abunda ya ragema... 

𝐃𝐎𝐍 𝐇𝐀𝐊𝐀 𝐍𝐀𝐊𝐄 𝐉𝐀𝐍 𝐇𝐀𝐍𝐊𝐀𝐋𝐈 𝐀 𝐖𝐀𝐍𝐍𝐀𝐍 𝐆𝐀𝐁𝐀𝐑

Musamman gamu mazaje domin mune da matsala tunda idan har mun tura Mace mun bata goyon baya toh ba abunda zai hanata zuwa... kama daga awo har haihuwar! inma muna kokonto zamu iya kaita da kanku asibitin wajen awo kuma muma likitoci muna maraba da mazajen muga kuna rako matanku domin wasu sakonnin ku mukafi so kuji dama.

Don haka magidanta ku daure ku taimaki iyalanku ku gane duniya fa ta canza... yanzu hatta cimarmu bame kyau bace irinta magabatan mu. Jikin mu ba irin na iyayen mu bane, shyasa in sunyi wani abun zamaninsu sun kwana lfy mu in mukai ayau toh aciki zamu kwana.

Matan mu na yanzu ko motsa jiki basayi sai anyi da gaske, gasu da ciye-ciye hadda na banza tun ma ba cin zaqi da maiko irinsu chocolates dinnan ba, batare da lissafi ko nazarin me zaije yazo ba. 

■- Inko kana turata awon amma bata bada hadin kai toh ka rakota ka hadata da jami'an lafiyar zasu saita ta. Kuma kaima ka nuna mata 6acin ranka afili kan hakan tare da fadamata illar da take jefa kanta.

■- Bawani likita da zai iya taimakonka game da haihuwa ta waya ko chat... abace da kurum dole sai gaba da gaba.

■- A game da haihuwa baka bukatar sai wani yace me ya dace kai, karka kuskura kake kallon kudinka matsayin priority sama da abunda za'a haifama, haihuwa baiwa ce sai baka da ita kasani.
 
■- Kamar yadda kake tanadin kayan haihuwa ko suna mu daure mu rika shirin kota kwana ta hanyar ware wasu yan kudade koda haihuwar zata zo mana da matsala. Tare da da ware kudaden da zamu kashe na kai iyalin mu asibiti su haihu mu dawo gida koda ba asami matsala ba.

A haihuwa da aure ake samun mai ambaton 𝐥𝐚'𝐢𝐥𝐚𝐡𝐚'𝐢𝐥𝐥𝐚𝐥𝐥𝐚𝐡𝐮 darajar da babu me samunta saikai da aka haifawa kaga ko tafi kudi. Inka kudurci bawa iyalinka kulawa da kyau Allah ma sai ya budamaka. Yafi kai sake ka rasata wajen haihuwa bayan watanni ko shekara ka dawo kana kici-kicin kuma samun kudi don yin wani auren... na tabbata kudin da zaka kashe a asbiti bai kai na qara aure ba.

A karshe wadannan abubuwa duk lamarin Allah ne akwai yanayin da ko a asibitin likitoci ba abunda zasu iya yi bayan sun nasu dukkan kokarin na ceto mutum kurum hakan ya zamo mahadin ajali.... toh amma de kaso 90% na mace macen mata masu ciki muna iya kaurace musu insha Allah in mun bada hadin kai.

Wannan shine Allah yasa agama haife haife lafiya. Ina fatan sakon ya isa.

[𝐈𝐛𝐫𝐚𝐡𝐢𝐦 𝐘. 𝐘𝐮𝐬𝐮𝐟]

Post a Comment

0 Comments