A wannan Darasin zamu fahimci wadansu matakai ko kuma gabobi da Coin ko Token yake bi har ya shiga kasuwa, wadannan matakai kusan Mataki na farko dana biyu wato Presale da ICO dukkanin su kusan babbar manufar itace a samu kuɗin da za'a dauki nauyin wannan project din har a samu damar dorashi cikin Exchange Application da Kuma Decentralized Application, Wanda da shiga wadannan Manhajojin to zai zama budadde ga kasuwar duniya gaba daya, za'a iya saye da sayarwar shi daga ko'ina, domin su dama wadannan Manhajojin babban Amfanin su kenan ga project din.
Jerin wadannan matakan sune:
Pre-sale »»» ICO »»» Lunching »»» Listing.
Kowanne Mataki anan yana zaman kansa, kuma ya nada tasiri akan akan wannan project din wajen karbuwan sa ko kuma akasin haka a kasuwa, samun matsala a daya daga cikin wadannan matakan na iya shigar da rudani akan wannan project haka kuma kammaluwar su cikin nasara nada alaka da Nasarar da wannan project din zai samu.
MATAKI NA FARKO: PRE-SALE.
MENENE Pre-sale?
Ma'anar Presale na nufin hanyar da ake siyar da Coin ko Tokens kafin a shiga ICO Nashi – Ita sayarwar anayin ta ne ya danganta ga tsarin masu gudanar da Tokens/Coins din, maslan:
✴ Akwai masu yin Presale din su Public wato kai tsaye zasu Tallatawa kowa dukkanin mai ra'ayin saye sai yaje ya siya.
✴ Akwai kuma wadanda zasu zabi wasu daga cikin mutanen da suka san zasu saya sai su basu damar sayen shi a farashin da suka saka masu
✴ Sai kuma wadanda Privately Kawai zasu sayar da shi a Presale, wannan sune idan suka sayar dashi Privately to Wanda ya Siya ya zama kamar Agent ne na Tokens din.
Saboda haka, su masu Coin ko Tokens din Sune zasu zabi irin tsarin da zasu dauka kuma su saka farashin da suka ga ya dace. Domin shi Pre-sale kusan taimakekeniya ce tsakanin masu Coin ko Tokens da Kuma wadanda suka saya, domin idan aka samu Project din ya samu nasara a kasuwa to dukkanin su zasu sami Riba tunda dama a Pre-sale ana Sayarwa ne a farashi dan kadan.
To idan Developers na Coin ko Token suka zabi irin tsarin da zasu bi wajen fara Presale Nashi abun da ya rage sai tsara kuma yawan adadin kwanaki ko watannin da zasu dauka ana wannan Presale Nashi, shima anan zabi ne nasu masu Coin ko Token din su zabi iyaka tsawon lokacin da zasu dauka suna hakan. Kar ku manta shi Pre-sale anayin sa ne domin janyo hankalin masu saye (investors) kenan Tareda basu tazara na lokacin gudanar da wannan Presale din.
Tsarin jadawalin Presale ana kasashi ne Kash-Kashi, ma'ana tazara na lokaci acikin tsawon lokacin da za'a dauka. Misali.
✴ Wanda za'a dauki Wata daya ana Presale Nashi sai ace to za'a yi Presale na Sati dai-dai wato kashi hudu kenan.
✴ wanda Za'a yi wata Uku kuma ana Presale Nashi sai a raba shi wata-wata, kenan za'a yi wata daya bayan daya, sau uku ke nan.
To haka tsarin yake tafiya, rabawar bawai wani abu nace, illa dabarun gudanar da kasuwa na baiwa mutum dama, Tareda janyo hankalin masu saye su kuma shiga ciki.
MATAKI NA BIYU: Initial Coin Offering (ICO)
MENENE Initial Coin Offering (ICO)?
Ma'anar ICO na nufin lokacin da aka kammala fitar da Coin ko Tokens Zuwa kasuwa ma'ana dukkanin wasu bayanai na wannan Coin ko Tokens din sun gama kammala, kamar irinsu Whitepaper da kuma bayanin yanda kasuwar wannan Coin ko Tokens din zata kasance idan ya shiga kasuwa na adadin sa da kuma yawan wanda aka samar duk zasu kasance a cikin Whitepaper.
To Kafin Coin ko Token ya Shiga wannan matakin na ICO sai an kammala Presale nashi wanda ko wanne mataki ana samun banbanci na farashin wannan Coin ko Token din. Maslan idan an sayar da shi a ₦5 a Presale to da zaran ya shiga ICO zai iya komawa ₦20, wanda shima.damace ga mutum da kuma su masu Coin ko Token din domin Indai ya zama successfull a ICO to zai baiwa wadanda suka saya Riba mai kyau.
Kamar Yanda nayi bayani a sama idan Coin ko Token ya Shiga ICO to ya Shirya tafiya ko kuma shiga kasuwar Crypto be gaba-daya wato kafin ya shiga sai ya tabbatar da fitar da bayanan wannan Coin ko Token din cikin wannan Whitepaper din tasa, wadannan Bayanan sune mutum yake fara nema idan zai sayi Token ko Coin a Kasuwa ire-iren bayanan sune:
✴ Adadin yawan Coins ko Tokens din da suka Samar gaba-daya
✴ Hanyar da zasu bi wajen saye da sayarwar shi ga masu sayen - wato inda za'a yi Kasuwancin sa.
✴ Use case na shi wannan Token ko Coin din, Wanda akansa ne Dukkanin ingancin sa ko akasin haka zai bayyana.
Kuma idan Coin ko Token ya Shiga ICO to Yana baiwa wanda ya mallakeshi damar Exchanging dinsa zuwa wani abun. Misali idan yana Classic Coin $CLC to zaka iya sayen Little Rabbit $LTRT dashi.
Sabod haka waɗanda Presale ya wuce su, to idan sukai Sa'a suka shiga ICO da wuri na shi wannan kalar Coin ko Token din to idan akayi lunching Nashi yana tashi ne sosai ma'ana farashin sa yana hawa ya wuce ma wanda yake a ICO, Wanda Wannan shine yake basu damar samun gwaggwabar riba. Kuma wannan kusan itace manufar da ake sayen Coin ko Token din da yake a ICO.
MATAKI NA UKU: LUNCHING
MENENE Lunching?
Ma'anar Lunching na nufin gabatarwa, to amma shin akwai wata gabatarwar da Coin ko Token take da bukata bayan waccan ta farko da ake fara yi wanda acikin ta ake kaddamar da Presale Nashi? Amsar tana rabuwa kashi biyu. Ma'ana Eh. Da kuma A'a. Masu Eh. Itace Ana kara yin Lunching na Coin ko Token idan za'a shigar da shi cikin sabuwar Exchanger Application ma'ana shi wannan Lunching din Kawai anayin sa ne domin fadawa jama'a cewa Coin ko Token kaza ya kara samun wani Tagomashi na tafiyar da Kasuwar sa.
MATAKI NA HUDU: LISTING.
MENENE Listing na Coin ko Token?
Listing na nufin Saka Coin a cikin Exchanging Application (ma'ana Manhajojin da ake Exchange). To duk idan Coin Tsallake wadancan matakan, matakin da zai ta cigaba shiga kuma zai rika daga darajar sa a kasuwa shine Listing Nashi a Exchanger, ma'ana ace an fara saka shi acikin Exchanger Application.
Listing na Coin Acikin Exchanger shine babban abinda yake daga darajar sa cikin kwana ɗaya (nai maka ta Sakkwatawa). Domin shigar Coin cikin Exchanger nada Cikin abubuwan da ake la'akari da su domin tabbatar da ingancin wannan Coin din, sannan kuma shine zai baka tabbacin cewa Mutanen da suke rike da wannan Coin din sunada kuɗin da zasu jibincin lamurran sa. Maslan:
Shaharar Exchange Application a duniya idan Coin ya Shiga cikin to itama zata shahara, idan mun fahimci hakan, Manhajar Binance kowa ya santa saboda haka idan akace yau Coin dinka zai shige ta ko kuma ya shige ta, to zai samu Tagomashi mai yawan gaske na sabbin masu sayen wannan Coin din da kuma karuwar masu sayen sa domin kuwa ita manhajar Binance ta tanada yawan mutane da suke amfani da ita. Sannan kuma wani abu da zai Dada Tabbatar maka da cewa idan kaga coins kaza a Exchange Application irinkaza kasan Masu shi sun shirya masa, hallau idan muka dauki Binance, kafin ace Coin dinka ya shige ta sai ka biya Donation Fee (Wato Listing fee) wannan Kuɗin wasu na cewa Sai an bada 40 Bitcoin wasu kuma sunce 50 Bitcoin ake bayarwa, amma kafin su saka Stack sai da suka karbi 400 Bitcoin, wasu wani kamfanin Blockstack shima yace sai da ya $250,000 — Mafi yawanci fees din da ake biya ya danganta da yanayin project din amma dai ranging din Bai wuce $0.5 Million Dollars Zuwa $3 Million Dollars.
Wadannan Sune matakan da Coin ko Token yake bi, ya shiga kasuwa inda kowa daga ko ina za'a iya saye da sayarwar shi. Kai mai saye A duk lokacin da ka samu Project kayi dukkanin DYOR din da zakai akansa kuma ka samu peace of mind akai to Siya ne ya rage maka. Domin matakin samun ribar ka mai yawa shine saurin shigar ka da wuri. Kuma ka sani cewa Idan za'a sayar dashi a ₦5 a Stages din Presale Nashi to da ya Shigo ICO Kuma Farashin sa karuwa zai yi ya koma ₦30, shima da zaran an gama na lokacin da aka diba to da anfara Listing Nashi a Exchange Application to nan ma farashin sa kara Haw-hawa yake yi.
Wannan shine Bayanin da ya kamata ka Sani, domin har yanzu wasu basa bambanta tsakanin yaushe ake yin su, ko kuma menene ma'anonin wadannan abubuwan (Presale, ICO, lunching da Listing) idan ana Magana akan Token ko Coin... والله اعلم....
Mustapha Gfatu ✍️
June 16, 2021
0 Comments