✅Babu shakka lallai tunawa da Allah da komawa zuwa gareshi da yawan tuba da Istighfari lokacin da bawa yake rashin lafiya yana ciki hanya mafi girma na samun warakar bawa daga dukkan cutukan da ke damunsa.Yana cikin matakan samun waraka ga marar lafiya,bawa ya fara da rokon Allah da komawa zuwa gareshi da neman gafararsa,wannan itace mafi girman hanyar waraka ga wanda bashi da lafiya,domin ya nemi waraka awajan mai ita kuma wanda yake warkarwa.
✅Yana kuma cikin hanyar samun waraka karanta Alqurani mai girma,kamar yadda ya tabbata acikin saheehul Bukhari na yin Rukqa da karanta Suratul fatiha sau bakwai ga marar lafiya,da kuma guarantee sauran surori da ayoyi na neman waraka,kamar Qulhuwa da falaqi da Nasi da Ayatul Qursiyyu, da ayoyi guda biyu na karshen Baqara da dukkan wani bangare na alqurani mai girma,domin Alqurani dukkansa warakane kamar yadda Allah yake fada:
*(ﻭﻧﻨﺰﻝ ﻣﻦ ﺍﻟﻘﺮﺁﻥ ﻣﺎ ﻫﻮ ﺷﻔﺎﺀ ﻭﺭﺣﻤﺔ ﻟﻠﻤﺆﻣﻨﻴﻦ)*
@ﺍ ﺍﻹﺳﺮﺍﺀ 82
ADDU’O’IN NEMAN WARAKA DA SUKA TABBATA ACIKIN SUNNA
1-ﻻ ﺑﺄﺱ ﻃﻬﻮﺭ ﺇﻥ ﺷﺎﺀ ﺍﻟﻠﻪ.
*(LAA BA’AWA DHAHURUN INSHA ALLAH)*
@Bukari ya fitar da wannan hadisi daga Sahabi ﺍﺑﻦ ﻋﺒﺎﺱ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﻤﺎ ”
2-Annabi s.a.w ya kasance idan baya da lafiya,yana karanta qulhuwa da falaqi da nasi sai ya yi tufi a hannunsa sai ya shafe dukkan jikinsa.
@Bukhari da Muslim
3-ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺭﺏ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺃﺫﻫﺐ ﺍﻟﺒﺄﺱ ﻭﺍﺷﻔﻪ ﺃﻧﺖ ﺍﻟﺸﺎﻓﻲ ﻻ ﺷﻔﺎﺀ ﺇﻻ ﺷﻔﺎﺀﻙ ﺷﻔﺎﺀ ﻻ ﻳﻐﺎﺩﺭ ﺳﻘﻤﺎ.
*(ALLAHUMMA RABBIN NASI,AZHIBAL BA’ASA WASHFAHU ANTASH SHAFI LAA SHIFAA’AN ILLA SHIFAA’AKA,SHIFA’AN LAA YUGHAADIRU SAQMA)*.
@Bukhari da Muslim.
Annabi s.a.w idan yaje duba marar lafiya yana taba jikinsa sai ya karanta wannan adduar.
4-ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﺮﺑﺔ ﺃﺭﺿﻨﺎ ﺑﺮﻳﻘﺔ ﺑﻌﻀﻨﺎ ﻳﺸﻔﻰ ﺳﻘﻴﻤﻨﺎ ﺑﺈﺫﻥ ﺭﺑﻨﺎ ”
*(BISMILLAHI TURBATI ARDHINAA BAREEQATU BA’ADHUNAA YASHFAA SAQEEMANA BI’IZNI RABBINA)*.
@Bukhari da Muslim
Manzon Allah yana sanya yatsansa manuniya a kasa sannan ya dagata sai ya karanta wannan adduar ga marar lafia.
5-ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﺭﻗﻴﻚ ﻣﻦ ﻛﻞ ﺷﻲﺀ ﻳﺆﺫﻳﻚ ، ﻭﻣﻦ ﺷﺮ ﻛﻞ ﻧﻔﺲ ﺃﻭ ﻋﻴﻦ ﺣﺎﺳﺪ ، ﺍﻟﻠﻪ ﻳﺸﻔﻴﻚ ، ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﺭﻗﻴﻚ.
*(BISMILLAHI ARQEEKA MIN KULLI SHAI’IN YU’UZIKA,MIN SHARRI KULLI NAFSIN AU AINU HAASIDIN,ALLAHU YASHFEEKA BISMILLAHI ARQEEKA)*.
@Muslim
6-ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ.
*(BISMILLAH)* sau ukku
Sannan sai a karanta wannan adduar ta kasa sau bakwai:
“ﺃﻋﻮﺫ ﺑﻌﺰﺓ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻗﺪﺭﺗﻪ ﻣﻦ ﺷﺮ ﻣﺎ ﺃﺟﺪ ﻭﺃﺣﺎﺫﺭ”.
*(A’UZU BI’IZZATILLAHI WA QUDRATIHI MIN SHARRI MAA UJIDU WA UHAAZIR)*.
@Muslim
7-ﺃﺳﺄﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﻌﻈﻴﻢ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺮﺵ ﺍﻟﻌﻈﻴﻢ ﺃﻥ ﻳﺸﻔﻴﻚ .
*(AS’ALUL LAHAL AZEEMA RABBIL ARSHIL AZEEMI AN YASHFIYAKA)*.
@Abu Dauda da Tirmizy
Ana karantawane sau bakwai,Annabi ﷺ yana cewa:
*(Babu wani marar lafiya da ajalinsa bai zoba da za’a karanta masa wannan addua face Allah ya bashi lafiya)*
@Duba Riyadus Saliheena
8-ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺍﺷﻒ ﺳﻌﺪﺍ ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺍﺷﻒ ﺳﻌﺪﺍ ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺍﺷﻒ ﺳﻌﺪﺍ.
*(ALLAHUMMA ISHFI SA’ADAN,ALLAHUM
MA ISHFISA’ADAN,ALLAHUMMA ISHFI SA’ADAN)*.
@Bukhari da Muslim.
Amma wajan sa’a sai ka sanya sunan marar lafiyar misali:
ALLAHUMMA ISHFI Mustapha sau ukku.
Sunane ga wanda yaje wajan marar lafiya ya yi masa addua da daya daga cikin wadannan addu’o’in da suka tabbata daga Annabi ﷺ kuma Ummuna Aisha R.A tana babu labarin Mala’ika Jibril ﷺ yayiwa Manzon Allah ﷺ Ruqya lokacin da yaje dubashi.
*Allah ka warkar da marar lafiyarmu baki daya*.
Share this:
0 Comments