Daga Dakta Jamil Nasir Bebeji,
Ita dai wannan kwayar cutar ta sanyi wato Gonoriya tana shiga jikin mutum ne ta hanyar mafitsara inda daga nan ne sai ta shiga jijiyoyin jini, shi ke nan sai mamaye duk jiki, wato yayin da mace lafiyayyiya ta sadu da namiji mai ciwon wanda jininsa gaba daya cike yake da ciwon, amma a fatar jikinsa ba dole a gane ba, don haka yayin da maniyyinsa ko maziyyinsa ya shiga jikinta, to ciwon sai ya makale a gabanta, amma ba zai yi mata wani tasiri ba, har sai yah aura ya shiga mafitasarata inda daga nan sai ya mamaye jikinta ta hanyar jini, to sannan sai ya biyo jini ya shigo mararta inda zai zama farjinta shi ne mazaunarsa.
Wanda shi kuma namiji lafiyayye yayin da ya sadu da mai wannan ciwo na sanyi wanda dama yana jininta kuma yayi ka-ka-gida a gabanta, to nan da nan zai hauro mafitsararsa, wanda kuma ita ce hanyar maniyyinsa, sai dai daga ciki sun rabu, inda shi ma daga baya zai duk jikinsa musamman zakarinsa. Shi ne likitoci suke cewa shi wannan ciwo Gonoriya, yana iya kama duk nau’in shekaru na mace, tun daga mafitsara yake bi don haka ko yayin da ta je yin fitsari a wuri mara kyau, wanda yake akwai ciwon, to zai iya biyo fitsarinta ya shiga jikinta, kuma zai iya yin tasiri a ganshi ya bayyanar da matsala a farjinta.
Amma namiji kuwa, amma namiji ko ya shiga jikinsa baya bayyana har sai ya balaga. Idan mun fahimci babbar hanyar da ake daukar wannan ciwo na sanyi shi ne jima’i, ta gaba ne ko ta dubura, mace da mace ko mace da namiji, ko namji da namiji, ko mutum ne da wata dabba da take dauke da ciwon, amma ba sosai ake dauka a bndaki ko ta karin jini ba.
Kuma shi wannan nau’in na ciwon sanyi in ya shiga jiki ba a take ake sani, don alamarsa ba ta bayyana sai bayan kwana biyu ko uku, wani lokacin ma yak an haura wadannan kwanakin har ya kai sati biyu, ya danganta da yadda karfin jinin jikin mutum yake.
Shi wannan ciwo akwai shi ako ina cikin duniya, har da nan Nijeriya sosai, kullum kuma ana samun adadi yana karuwa, amma ya fi yawa a kasashen turai musamman Amurka, da Sweden, da Sipaniya. Kamar yadda mai littafin Health & Education for the Family ya kawo cikin littafin nasa, ya cigaba da cewa, kuma ya fi awannan yankin ne saboda abubuwa uku, na farko:- Permisikiness, na biyu Promiscuity, na uku Pill.
Permisikiness shi ne, idan ka duba Odford Dictionary, shi ne ba da ‘yanci yin zina, wanda an fi samunsa wadancan kasashen. Na biyun kuma Promiscuity, shi ne yin jima’i da mutane barkatai ga mace ko namiji. Na uku shi ne Pill, kwayoyim hana haihuwa wanda ya ce suna yawanta sha don kar su samu haifuwa.
Anan gurin wata kila yana nufin akwai wasu kalar irin wadannan kwayoyi na hana haifuwa da sylke haifar da wannan ciwo na sanyi a duniya, saboda wata cutar akan samu wasu kungiyoyi ko wasu mutane suna ra’ayi akanta. Wata kila saboda yanayin kasuwancinsu.
Daga cikin alamomin wannan cutar sanyi ta Gonoriya, akwai zafi ko kuna musamman a karshen yin fitsarin, da ganin farin ruwa ta gaba a farkon al’amari, wanda daga baya in yayi tsanani sai ya juya zuwa ruwan kasa har ya kai kore-kore.
Wani lokacin ma har da bayyanar kananan kuraje akan zakari ko farjin mace tae da jin kaikayi, kuma ya kan sa ciwon jiki, da jin motsi, da rashin haihuwa, da rashin sha’awa, da makanta musamman ga jarirai idan sun samu a wurin iyayensu.
Ingantaccen maganin wannan cuta mujarrabi shi ne, ‘Sihhatuzzaujaini’ a hada da Aulama, da Yusjam, da na fata da ake shafawa.
Bayin Allah idan ba a manta ba mun fadi maguna da suke da tasiri a kan kowane irin ciwon sanyi, kamar yadda babban likita kuma Malami wato Dawudul’andaki ya fada. To in sha Allahu da yake shi ciwon sanyi ya kasu ya kasu da dama kamar yadda muka yi bayani a baya, to a kowane kala za mu fadi irin maganin da ya kebanta da shi.
Mun samu bayanai gamsassu daga likitocinmu na musulunci na da da na da yanzu, game da shi wannan ciwon sanyi ,ai matukar cutar da jiki,. To kuma daga cikin bayanan likitocin yamma game da shi wannan ciwo na sanyi akwai likita mai suna Isidro Aguilar babban likitan mata a asibitin Faransa, kuma Lakcara a Jami’a ta Madrid a kasar Sipaniya (Andulus), tun a shekarar 2000 yayi littafi mai suna ‘Encyclopedia of Health and Education for the Family’. Littafi mai Mujalladi 4, wanda a Mujalladi na 2 babi na 28 shafi 168, ya sa masa suna wato (STD) wato Sedual Tranmitted Deseases, ana nufin cututtukan da ake dauka ta hanyar jima’i.
Yake cewa kuma ana kiransa ‘Benral deseases’ wannan kuma tsohon yare ne na kasar Girka (Greek) da Italiya (Rome). Ya ce shi wannan ciwo na sanyi ana daukarsa ne ta hanayar jima’i, duk cewa akwai ‘yan kadan da ake dauka ba ta wata hanyar. Kuma duk da cigaba da aka samu na gwaje-gwajen zamani da magunguna masu karfi, amma bai hana cutar yaduwa ba kamar wutar daji.
Ya ci gaba da cewa shi wannan ciwo yana da matukar hadari da barazana ga rayuwar wanda ya kama, don yana iya hana haihuwa ta hana karfin da namiji, da hanawa mace sha’awa, ko in ana saduwa ta dinga jin zafi, da haira da makanta, da haifar da matsolin zuciya, da matsala a kwakwalwa, da raunin jiki, da idan ya kasance Gonoriya ko Slifils, ya kan iya kai mutum ga samun jijjiga ko bugun zuciya, ko shanyewar jiki, don har ya kan sa mutum ya daina ji, da zubewar ciki ga mai cikin da hauka mai tsanani.
Ya cigaba da cewa, su wadannan cututtuka na sanyi su suka fi yaduwa acikin jama’a, kamar yadda Mujallar Jounal ta bugo bayanai game da lafiya ko wane yanki a duniya. Ta buga cewa kungiyar lafiya ta duniya dake Majalisar Dinkin Duniya, ta ce bincike ya tabbatar cewa a ko wace shekara ana samun kwata na mutanen duniya da suke kamuwa da shi wannan ciwon na sanyi, wadanda sababbi ne ba a san su ba.
Sai kuma likita wanda asalinsa mutumin Ingila ne, da yake koyarwa a wata Jami’a ta Faransa, kwararre ne akan cutukan mata (Hamiya Galbas) yake cewa, cutuka da yawa suna faruwa a duniya, amma ciwon sanyi da ake dauka jima’i yana da ban tsoro, saboda hadarinsa da saurin yaduwarsa na kasa gane dalili. Ya ci gaba da cewa, wannan ciwon sanyi bincike ya tabbatar da cewa, ya fi yawa a tsallaken turai, musamman kasar Amurka da ake samun kusan mutane miliyan uku sababbi da suke kamuwa da ciwon a duk shekara, sai kuma kasar Sipaniya da ciwon ya iilata kusan kasha talatin da biyar na mutanen garin, duk da wayar da kai da ake yi da magunguna masu.
Daga nan kuma sai kasashen Afirka, wanda ya fi karanci a kasashen Larabawa.” Ya ce, “Duniya na ba da shawara da karfi akan wanda zai jima’i haramtacce to yayi amfani da (Condom) to amma fa mun lura gaskiya bai da tabbas sosai wurin hana daukar cutar sanyi.”
To ya ‘yan uwa idan muka ce za mu yi cikakken sharhi akan bayanan wadan nan likitoci, to lokaci ba zai ba mu dama ba, sai dai za mu dan yi a taikaice, sannan babban jin dadin shi ne, Allah Ta’alah mai rahma ne shi mai jinkai y ace, “Kul ya ibadiyallazina asrafu ala amfusikum La taknadu mirrahmatillah, innallaha yag firuuzzunuuba jami’a, innallaha huwal gafuururrahim.”
Wato Allah Ta’alah ya ke fada wa Manzon tsira cewa “Ka gaya wa bayi na wadanda suka wulakanta kansu wajen saba wa Allah, to ka da su yanke kauna daga rahmar Allah, domin an tuba kuma aka nemi gafararsa, to shi fa yana gafarta zunubai baki daya.
0 Comments