Wasu Abubuwa Guda 25 Da Suka Kamata Kiyi Kamin Ki Kai Shekaru 25 Idan Bakiyi Aure Ba:




Rayuwan mace da take da aure, da Kuma wacce ta taba aure, sun bambamta da rayuwan macen da bata taba aure ba komai yawan shekarunta. 

Wasu matan tun sunada shekaru kasa da ashirin a duniya suke yin aure. Wasu kuwa sukan haura shekaru 20 lokacin aurensu bai zo ba. 
Shekaru 25 na haihuwa ga 'ya mace sune shekarun da suka fi dacewa ace tana gidan mijinta idan son samu ne. Daga lokacin da mace ta soma haura wadannan shekaru ta soma fita da rukunin 'yan mata a shekaru ta soma zama mace koda kuwa bata yi auren ba.
Matan da suka yi aure da wuri mata ne da basa samun damar yin wasu abubuwan da zai taimaka musu a zaman aurensu ba. Domin kamin su samu gogayya na rayuwa tuni sun shiga gidan miji. Matan da kuma aka samu jinkiri wajen aurensu, suna da damar da zasu koyi wasu abubuwa na rayuwa kamin lokacin auren nasu yayi.
Ga wasu abubuwa guda ashirin da biyar da suka dace duk macen da bata taba aure ba zata yisu kamin ta cika shekaru ashirin da biyar da haihuwa.


 
1: Ki siffantu da kyawawan dabi'u.
2: Ki nemi illimin addini.
3: Ki nemi illimin zamani.
4: Ki koyi sana'ar hannu.
5: Ki kasance tare da kawaye na gari.
6: Kiyi kokarin gano baiwa ko basiran da kike da shi. 
7: Ki koyi iya zama da mutane
8: Ki koyi kyauta
9: Ki koyi tarbar mutane
10: Ki kwarai wajen iya aiyukan gida. 
11: Kada ki sa zakuwan yin aure ya tsaya Miki a rai.
12: Ki yawaita karance karance akan sanin wacece mace.
13: Ki fahimci darajar mace
14: Ki nunawa iyayenki da 'yan uwanki kauna.
15: Ki koyi tantali da adana.
16: Ki koyi rike sirri
17: Ki koyi hakuri da yafiya
18: Ki koyi bayarwa
19: Ki koyi kula da jikinki
20: Ki koyi girke girke 
21: Ki kiyaye mutuncinki
22: Ki tantance samarin da zaki kula.
23: Ki guji yin makauniyar soyaya.
24: Ki canza unguwa, gari, jihar ko kasa idan kika kasa samun manema a inda kike.
25: Kada kiyi wasa da addininki 
Wadannan sune wasu daga cikin abubuwan da macen da barayi aure ba kuma ta doshi shekaru 25 da haihuwa. Da fatan za a kiyaye.

Post a Comment

0 Comments