MAHIMMANCI KULA DA SALLAH AKAN LOKACI.
SALLOLI BIYAR.
Allah ﷻ Ya wajabta mana salloli biyar safe da yamma: Asubahi raka’a biyu, Azahar raka'a huɗu, La'asar raka'a huɗu, Magariba raka'a uku da Isha raka'a huɗu, gaba ɗaya raka'a goma sha bakwai.
A tsawon shekara ɗaya, ana sallah raka'a dubu shida da ɗari daya da ashirin (6,120).
A cikin kowacce raka'a akwai sujjada guda biyu, kuma a kowacce rana mutum yana yin sujjada (34).
Sallah tana da rai, da gangar jiki. Gangar jikinta shi ne tsayuwa da ruku'u da sujjada da karatu. Ranta kuma girmama Allah ﷻ da tsoron Allah ﷻ, yabonSa, rokonSa, neman gafararSa, salati ga Annabi ﷺ da yi masa sallama da sauran bayin Allah na gari.
Sallah tana da ciki da waje. Wajen sallah shi ne tsayuwa da zama da ruku'u da sujjada da sauran zikirori da addu'o'i. Cikin sallah shi ne girmama Allah ﷻ da tsoronSa da ƙaunarSa da yabonSa da ƙanƙan da kai gare Shi. Idan tauhidi da imani suka tsaya a cikin zuciya, sai biyayya da aiki su biyo baya.
Ita sallah kamar abinci ce ga zuciya da ruhi. Kamar yadda ake cin abinci kullum, ake shan ruwa kullum, ake shaƙar numfashi kullum, domin gangar jiki ta rayu, haka ma sallah ake yin ta kullum domin tana daɗa ƙarfin imani da ciyar da ruhi abinci. Da haka mutum zai ƙara sanin Allah ﷻ, ta hanyoyi shida, sanin Allah ﷻ ta hanyar sunayenSa, siffofinSa, ni'imominSa, addininSa da abin da Yake so da abin da ba Ya so da girmama Shi da gode maSa da yabonSa.
An tambayi Manzon Allah ﷺ “Wane aiki ya fi soyuwa zuwa ga Allah ﷻ?” Sai ya ce, “Yin sallah a kan lokacinta.” Sai aka ce, Sai kuma me? “Sai ya ce, biyayya ga iyaye.” Sai kuma me? Sai ya ce, “Yin jihadi saboda Allah (a tafarkin Allah ﷻ).
Allah ﷻ Ya wajabtawa bayi yin sallah a kan lokaci. Duk ibadar da aka saka mata lokaci wajibi ne a yi ta a kan lokacin.
Allah ﷻ Ya umarce mu da yin biyayya gare Shi da ManzonSa ﷺ. Abubuwan da aka umarce mu kashi huɗu ne:
1. Akwai ibadar da take da wuri da kuma lokaci, kamar aikin Hajji.
2. Akwai ibadar da take da wuri amma ba ta da lokaci. Ana iya yin ta a kowanne lokaci kamar Umra.
3. Akwai ibadar da ba ta da wuri kuma ba ta da lokaci kamar sadaƙa da kyauta da sada zumunci da makamantansu.
4. Akwai ibadar da take da zamani da lokaci kamar salloli biyar. Muna da salloli biyar a kullum: Azahar, La'asar, Magriba, Isha`i da Asubah.
Yanzu mafi yawa ana amfani da kalanda wajen tantance shigar lokacin sallah da fitarsa. Wannan ya sa za ka ga dukkan masallatai suna maƙale irin wannan kalandar domin sanar da masallata lokacin sallah. Duk da cewa masu yin kalandun suna da yawa, amma za ka ga kusan duk sun haɗu a kan lokaci ɗaya. Ko an sami bambamci ba mai yawa ba ne. Kuma yanzu kusan kowa yana amfani da wayar hannu kuma a cikinta akwai (application) da mutum zai sauke a wayarsa na sanin lokacin sallah. Don haka, wannan ya isa a kan maganar lokutan sallah. Amma kowacce sallah tana da farkon lokaci da ƙarshen lokaci. A kula da kyau kada a yi sallah kafin lokacinta, kuma kada a yi sakaci har lokaci ya fita ba tare da an yi sallah ba. Akwai kuma sallar da an fi so a yi ta a farkon lokaci, kamar sallar Asuba da Azahar da La'asar da Magriba, amma sallar Isha`i an fi so idan za a yi ta a ɗan yi jinkiri har zuwa tsakiyar lokaci, ta yadda idan aka gama ta sai a tafi gida babu maganar zaman majalisar hira bayan sallar Isha`i. Kamar yadda ya tabbata a hadisi, Manzon Allah ﷺ ya hana zaman hira bayan Isha`i da kuma yin bacci kafin a yi sallar Isha`i.” () Haka sallar Azahar, idan ana tsananin zafin rana an so a ɗan jinkirta ta har gari ya yi sanyi, kamar yadda ya zo a hadisi na Abu Zarrin (رضي الله عنه). () Waɗanda ƙasashen su dare kawai ake yi, ko rana kawai suke gani, ko kuma dare ya fi yawa sosai, ko rana tafi yawa sosai, sai su yi amfani da yanayin ƙasashen da suka fi kusa da su wajen tantance lokutan sallarsu, kamar yadda majalisar fatawa ta Qasar Saudiyya ta faɗa.
HUKUNCIN YIN SALLOLI BIYAR A KAN LOKACI.
Wajibi ne yin salloli biyar a kan dukkan baligi, mai hankali a halin zaman gida, halin tafiya da yaƙi a kan namiji da mace, sai mace mai yin jinin haila, da mai jinin biƙi har sai ya ɗauke.
Ana umartar yaro da yin sallah tun yana ɗan shekara bakwai domin ya saba, saboda faɗin Allah ﷻ a cikin Suratul Nisa`i:
﴿ إِنَّ الصَّلَوةَ كَانَتْ عَلَى المُؤْمِنِينَ كِتَابًا مَوْقُوتًا ﴾ ()
Ma’ana: “Haƙiƙa sallah ta kasance wajibi ce a kan muminai kuma an saka mata lokaci.” Da kuma faɗinSa a cikin Suratul Baqarah:
﴿ حَافِظُواْ عَلَى الصَّلَوَتِ وَالصَّلَوةِ الْوُسْطَى ﴾ ()
Ma’ana: “Ku kiyaye salloli da kuma sallar tsakiya.” ()
Hadisin da Bukhari da Muslim suka ruwaito daga Abdullahi Ɗan Umar (رضي الله عنه) cewa Manzon Allah ﷺ ya ce, “An gina Musulunci a kan ginshaƙai guda biyar: Shaidawa babu abin bauta bisa cancanta da gaskiya sai Allah ﷻ, kuma Annabi Muhammad ﷺ ManzonSa ne, da tsayar da sallah da bayar da zakka da hajji da azumin watan Ramadan.” ()
Da hadisin Abdullahi ɗan Abbas (رضي الله عنه) ya ce, “Lokacin da Annabi ﷺ ya tura Mu'azu zuwa Qasar Yamen ya ce masa, “Ka kirawo su zuwa ga shaidawa babu Abin bauta bisa cancanta da gaskiya sai Allah ﷻ kuma su shaida ni ManzonSa ne. Idan sun yi biyayya ga haka, ka ce musu: Haqiqa Allah ﷻ Ya wajabta musu yin salloli biyar dare da rana.” ()
Haka kuma hadisin Amri Bn Shu’aib wanda Al'Imam Ahmad da Abu Dawud suka ruwaito, Manzon Allah ﷺ ya ce, “Ku umarci ‘ya’yanku da yin sallah, tun suna ‘yan shekara bakwai, ku yi musu ladabi a kan sallah idan suka kai shekara goma, kuma ku raba musu shimfiɗa a wajan bacci.” () (Wato ya zama kowa wajen kwanansa daban).
Alamomin da za a gane yaro ko yarinya sun balaga na farko idan suka cika shekara goma sha biyar, na biyu idan gashin hammata ko gashin gaba ya tsiro musu, ko kuma suka kwanta bacci suka yi mafarki maniyyi ya fito. Idan kuma namiji aka ga ya fara gemu da gashin baki, ko kuma mace aka ga ta fara yin jinin haila, ko ta ɗauki ciki, duk waɗannan su ne alamomin balaga. Idan suka bayyana alqalamin Shari'a ya hau kan mutum, mace ko namiji.
Za mu ci gaba insha Allah
0 Comments