DANGER SIGNS DURING PREGNANCY
- ZUBAR JINI:- Lokacin da mace keda JUNA BIYU ba a bukatan ganin jini a tattare da ita matukar ba an haihu ba, duk Lokacin da aka ga jini ko aka fara ganin jini kafin haihuwa Yana tabbatar da akwai Matsala, Ana bukatan zuwa asibiti Dan ceto uwar da Dan da kecikin cikin.
- JIJJIGA:- Jijjiga yayin ciki, da lokacin haihuwa ko bayan haihuwa na daga cikin ababe mafi Hatsri, Jijjiga ga mace Mai ciki tana alamta lallai akwai Matsala boyayya, akwai Abunda ya dace ayi Dan taimakon Rai dama ceto ran Uwar.
- CIWON KAI MAI TSANANI:- Ciwon kai Mai TSANANI ga dukkan Mata masu juna, lokacin haihuwa ko Bayan haihuwa na daga cikin MANYAN MATSALOLI Daya dace a kula a Kuma dauki Mataki ga Mata uwayenmu, Mata bayin Allah.
- ZAZZABI DA YAWAN KWANCIYA:- Zazzabi da yawan kwanciya kowane lokaci ga mata masu ciki na Daya daga cikin matsalolin ciki, hadduran dake tattare ga Mata masu ciki masu bukatan agaji, Yawan kwanciya, kasa tashi daga Kan gado na tabbatar da Mai juna biyu na cikin matsala ko HATSARI.
- CIWON CIKI KO MARA MAI TSANANI:- Ciwon Mara lokacin da mace keda JUNA BIYU mai tsanani na Daya daga cikin matsalolin ciki ko hadduran dake tattare ga Mata masu ciki sai ayi bincike ta yanda za a ceto uwar da Dan ta.
- SHASHSHEKA, NUNFASHI DA SAURI KO SUMA DAMA RASHIN NUMFASHIN:- Duk lokacin da aka samu Mata masu ciki cikin wannan yanayin lallai suna tabbatar da akwai Matsala kuma ire iren wadannan Matan na bukatan taimako Dan gudun Wahala dama Rasa Rai Allah ya Kyauta yaji kanmu, yajikan iyayenmu Amen.
Fatan Haihuwa lafiya, Ya Allah ka saukar da matanyenmu lafiya, Kayi masu albarka, kasa matanmu aljanna sanadiyar wannan ibada ta daukan ciki, Renon ciki da Haihuwa Amen, Allah damu mazan masu kokari duk kajefa mu cikin aljanna babba 😄😄😄🙏🙏🙏
(Kabir Danwuri)
0 Comments