Yadda Zaki Cusawa Mijinki Kaunarki A Zuciyar Sa:



 

Akwai dabaru da hikimomi, hadi da kissa da kuma kisisinan da mace zata iya amfani dasu domin ganin ta cusawa mijinta kaunarta a zuciyarsa.
Irin wadannan dabaru ba wani wiya ko3 wahalar gudanar wa suke da shi ba. Sai dai mata da dama basa iya aiwatar da irin wadannan dabaru.
Ga wasu3 dabaru na yadda zaki jawo soyaya mijinki cikin Suki.

 

Wanka Tare- ba duk mata sukasan cewa yin wanka tare da miji yana kara dankon soayya ba.
Koda kuwa ke baza kiyi ba, to ki yi kokarin ganin kin cuda shi kin wanken shi kamin shi ya daureye kansa.
Wannan salon dabaran mallakar miji yana da tasiri matuka ga duk macen da zata saba yiwa mijinta hakan

 

Girki na musamman- yiwa namiji girki na nusamman da kikasan yana so shima wani salo ne na mallakar miji cikin sauki.
Kada kiji3 kyashin kashe abunda yafi abunda ya baki na hada wannan abinci.
Duk macen da zata yi amfani da wannan dabaran na girki zata cusawa mijinta kaunarta cikin sauki.

 

Cin abinci Tare- cin abinci Tare- da mijinki shima wani salo ne na mallakar miji. 
Koda miji yana cin abinci da abokai ko 'yan uwane, ki rika samun wani abinci ko kayan kwalama na musamman da zaki rika3 bashi a lokacin da kuke ku biyu kuci tare.

 

Gaisuwa cikin ladabi- ki zamo mace mai gaida mijinta cikin ladabi duk safiya idan kun tashi. Haka kuma ki zama mai masa maraba cikin kauna idan ya dawo daga aiki. Ki kasance mai masa fatan akheri a lokacin da zai fita nema ko aiki.

 

Kada ki zama mai Mita- Yawan mita ga miji nan take kike fita daga zuciyar namiji.
Ki zama mace mai bari magana nan inda aka yita, ba tare da kin ci gaba da mita ba akan abunda ya wuce.

 

Kada ki zama mai zafin kishi- wasu matan na dauka cewan idan suka nunawa namiji zafin kishi zai sa ya sota, sam ba haka bane. Mata masu zafin kishi akasarin su suna rasa aurensu saboda wannan kishin nasu.

Ki zama mai nuna kishinki daidaita gwargwadon da shi miji zai rika gudun yin duk wani abunda zai saki kishi.

Amma idan kin zama mai zafin kishi a kullum zaki rika samun matsala da mijinki. Yadda hakan zai sa ki kasa samun soyayar sa kamar yadda ya kamata.

 

Babu ruwanki da duba wayarsa- mata da dama sun rasa mazansu saboda mugun halinsu na binciken wayar mazajensu.
Rashin daukar wayar miji wani dabara ne na mallakar mijinki cikin sauki amma ba dukannin mata suka san wannan sirrin ba.
 
Ki yi kokarin wajen gamsar da Miji- Kada ki gaza wajen gamsar da mijinki a duk lokacin da yake bukatarki.
Gamsar da miji na sa miji ya kasance yana matukar matarsa yana Kuma fata da burin ganin yayi rayuwarsa da ita.

#Tsangayarmalam
#sirrinrikemiji 
Wadannan wasu ne daga dabarun cusawa miji soyayya cikin sauki ba tare da wahala ba.

Post a Comment

0 Comments