LITTAFIN FIQHU DARASI NA 29/30




ƊAGA HANNU
Daga nan sai ɗaga hannu wanda yake da mahalli biyu.
Na ɗaya, za ka iya ɗaga hannu ‘yanyatsunka su zo dai-dai kunnenka.
Na biyu, za ka iya yin ƙasa-ƙasa da hannun ‘yanyatsun su zo dai-dai da kafaɗarka kamar ka yi saranda. ‘Yanyatsunka su kasance a haɗe su kalli gabas (alƙibla) wato alamar saranda.Wannan shi ake kira ɗaga hannu.

YADDA AKE ƊAGA HANNU
Ka haxa faɗar Allahu Akbar tare da ɗaga hannun. Wannan shi ne hanya ta ɗaya.
Za ka iya faɗar Allahu Akbar sannan ka ɗaga hannun.
Wato kenan ɗaga hannu yana da mahalli uku:
1. A yi shi kafin kabbara.
2. A haɗa shi tare da kabbara.
3. Ko kuma a yi kabbara sannan a ɗaga hannu.
Idan mutum ya yi wannan, ya shiga sallah kenan, kuma an sami abubuwa guda uku:
na ɗaya, a zuciya yake wato niyya,
na biyu da baki ake yin kabbara,
na uku kuma da hannu ake yi wato ɗaga hannu. Kenan a wajen shiga sallah an sami i’itiƙad ita ce niyya da ƙaulu, shi ne faɗin Allahu Akbar, da kuma fi’ilu, wato ɗaga hannu. Don haka malamai suka ce ana shiga sallah ne, bil’ƙauli, wal’i’itiƙadi, a cikin zuciya an ƙulla niyya, a baki an ce Allahu Akbar, an ɗaga hannu ma’ana an yi saranda (miƙa wuya) ga Allah ﷻ.


LITTAFIN FIQHU DARASI NA 30

TSAYUWA DA SHARUƊƊANTA
Tsayuwa tana da sharuɗɗa domin malamai sun ce da kabbarar harama da yin tsayuwa domin kabbarar harama. Ana tsaye ake kabbarar harama da kuma karatun Fatiha domin karatun Fatiha da tsayuwa duka farilla ne. Akwai wanda idan ka hango shi sai ka ga ba tsayuwa yake ba, kuma ba wata lalura ce ta sa ya yi doro, goho, banƙare ko kuma ya karkace dama ko hagu, ko ya ɗaga kansa sama ko ya miƙe kansa ba. Waɗannan abubuwa guda shida idan mutum ya yi su bai tsaya ba:
1. Duk mutumin da ya noƙe kansa, ma’ana: ya haɗa haɓarsa da ƙirjinsa, bai tsaya ba.
2. Mutumin da ya ɗaga kansa sama, shi ma bai tsaya ba.
3. Wanda ya banɓare baya, shi ma bai tsaya ba.
4. Wanda ya russuno gaba.
5. Wanda ya karkata zuwa hagunsa, bai tsaya ba.
6. Wanda ya karkata jikinsa zuwa dama, shi ma bai tsaya ba.
Sai an sami waɗannan abubuwa guda shida sun koru sannan ake samun fuskantar Alƙibla. Kishiyar waɗannan abubuwa da aka lissafo a sama shi ne tsayuwa, kamar mutum ya tsaya cak, ta inda duk wanda ya hango shi ba zai ce ya karkata dama ko hagu, ko ya noƙe kansa ko ya ɗaga kansa ba, ko ya yi goho gaba ko ya ɓangare baya ba.
Kuma inda ake so fuskarsa ko idonsa ya kalla shi ne inda zai yi sujjada, wato ya tsayar da kansa tsakiya cak, domin wani idan yana sallah sai ya noƙe kansa, ya haɗa haɓarsa da ƙirjinsa. Wani kuma sai ya ɗaga kansa sama wai sallah yake yi, wani kuma ya dinga rawa yana rangaji. Duk waɗannan abubuwan dariya wani littafi ne majahuli ya zo da su wanda ba a san asalinsa ba, har ma yana faɗar kowacce aya daga cikin ayoyin Fatiha akwai yadda ake yi mata nata rangajin. Na taɓa shiga wani masallaci ina bin wani liman sallah mai yin irin wannan rangajin, sai na ɗauka ko rawar ɗari yake yi ko kuma ba shi da lafiya ne. Sai daga baya na tuno can bayan shekara (22) muna karatu a wajen wani babban malami, Allah ﷻ Ya jiƙansa, yana koya mana Mukhtasar Khalil, sai yake ce mana akwai wani littafi ku kiyaye shi ba shi da asali yana cewa, idan liman zai yi sallah ya rangaza gabas da yamma ya yi kaza da kansa. Ka san shi ɗalibi idan aka ce abu babu kyau to sai ka ga ya yi ƙoƙarin samun littafin. Shi ya sa muka je kasuwa muka sayo littafin, har muka tashi muna kwatantawa muna yin dariya. Har ma wasu limaman suna ganin ƙwarewa ce da iya limanci mutum ya karanta wannan littafin ya zo yana yiwa mutane rangaji. Kai liman da aka ce ka tsaya cak, me ya haɗa ka da wani rangaji? Saboda haka mutum ya tsaya cak!
Akwai wani abu muhimmi, shi ne yadda ya kamata ƙafar mutum ta tsaya. Wani yakan buɗe ƙafafuwansa ta inda ta tsakanin ƙafafuwansa ma akuya za ta iya wucewa.Wani kuma zai tsuke ƙafafuwansa ya haɗe su.Wani kuma zai buɗa su daidai gwargwado wanda shi ne Shari’a ta ce a yi.
Wani ‘yanyatsunsa sukan kalli gabas, ko kusurwa, ko hagu ko dama yayin da wani ƙafarsa ɗaya ta juya ta kalli hagu ɗayar kuma ta kalli dama. Ita tsayuwa wadda malamai suka yi bayani ita ce ‘yanyatsunka su ma su kalli gabas, muddin ba wata lalura ko rashin lafiya mutum yake da ita ba ta yadda ƙafar ba za ta murɗa ta juyu zuwa gabas ɗin ba. So ake a buɗa ƙafa matsakaiciyar buɗawa yadda dai muka saba tsayuwa ba ware ko buɗa ƙafarmu muke yi ba sosai. Wani ma sai ya dinga tutture jama’a, yana kakkanewa sai ka ce yana kokawa ko yana filin daga. A wurin da ake so a sami tawadhi’u da ƙanƙan da kai, bai kamata mutum ya dinga bobboƙarewa ba.
Bayan mutum ya ɗaga hannayensa daidai kafaɗa ko daidai kunnuwa, idan ya dawo da su sakin su zai yi ko kuwa riƙe su zai yi a ƙirji? Ya tabbata a hadisin Manzon Allah ﷺ ya ɗaga hannayensa dai-dai kafaɗa kuma ya ɗaga su daidai kunne. Daga nan ya ɗora su a kan ƙirjinsa: ya ɗora hannun dama a kan ƙirjinsa ya ɗauki kuma hannun hagu ya ɗora a kan na dama. Shi ma akwai siffa biyu da aka ruwaito: siffatul qabdhu da kuma siffatul wadh’u

ZA mu ci gaba insha Allah.

Post a Comment

0 Comments