SHIN DOLE NE NA YI WA MIJINA HIDIMA?


(From the Archives)


Ɗaukacin malaman Musulunci sun tafi akan cewa mustahabbi ne mace ta kula da mijinta wajen yi masa hidima kamar dafa abincinsa da sharar ɗakinsa da gyara masa makwancinsa da banɗakinsa da wankewa da goge masa tufafinsa da sauran abubuwan da a al’adance za a fassara su da sunan kulawa da miji.

Malamai suna ganin za ta yi hidimar koda kuwa ta kasance mace ce mai muƙami wacce a al’adance irinta, ba ta yin sauran ayyukan gidanta da kanta.

Sai dai akwai saɓani a tsakanin malamai ta fuskar tantance shin dole ne ta yi masa hidima ɗin ko kuwa ba dole ba ne?

Ɗaukacin malaman mazhabobin Shafi’iyyah da Hanbaliyyah da wasu cikin Malikiyyah sun tafi akan cewa ba dole ba ne mace ta yi wa mijinta hidima, amma ba laifi in ta yi abin da aka saba a al’adance cewa mace na yi wa mijinta.

Su kuwa malaman mazhabar Hanafiyyah sun doge ne akan cewa, aikin gidan miji dole ne akan matar aure.

Yayin da ɗaukacin malaman mazhabar Malikiyyah da Abu Thaurin da Ibn Abi Shaibah da wasunsu suka tafi izuwa ga cewa, mace za ta yi wa mijinta hidima ne game da buƙatarsa ta cikin gida kawai. Amma duk abin da ya kama sai an fita wajen gida, kamar zuwa kasuwa da debo ruwa ko zuwa kai wanki da guga ko wani aiki makamancin haka ko kai sako da amsowa, to wannan ya fita daga abin da ake sa ran mace ta yi na kulawa da mijinta.

Malikiyyah sun ƙara da cewa, in mace ta kasance daga cikin 
mata masu ɗaukaka waɗanda matsayinsu ya ɗara wa aikin gida, kamar ‘ya’yan sarakuna da attajirai da duk wacce ta taso a gidansu cikin wadatar da take da masu yi mata aikace-aikace ko wacce ta sami wani matsayi a rayuwa kamar babbar malama ko attajira ko makamancin haka. To, irin wannan miji bai da halin ya sa ta aikin gida sai in ta ga dama, ko kuma in ya kasance matalauci ne ba shi da halin samar mata da masu aiki.

Ibn Taimiyah yana daga cikin malaman da suka zaɓi ra’ayin cewa dole ne matar aure ta yi wa mijinta hidima bisa abin da yake sananne a al’adar mutane. Sai ya ce: “Kuma ya wajaba a kan macce ta yi wa mijinta irin hidimar da aka san cewa irinta za ta iya yi ga irinsa. Kuma yanayin wannan hidima ya kan bambamta daga wuri zuwa wuri. [Alal misali] irin hidimar macen dake rayuwa a ƙauye ga mijinta ta bambamta da macen dake birni, irin hidimar da mace ƙaƙƙarfa za ta iya yi ta bambamta da wacce maras ƙarfi za ta iya yi”.

Haka shima Ibnul Ƙayyim ya tafi akai. A inda ya kawo hadisai da ke nuni izuwa ga haka, kamar hadisin Fadima ‘yar Ma’aikin Allah (RA) wanda aka ba da labarin cewa ta kasance tana niƙa a gidan mijinta Aliyu (RA) har hannunta ya yi kanta da hadisin Asma’u matar Zubair (RA) wadda ta kasance tana yi wa mijinta hidima, har da kulawa da dokinsa; Ita ke yanko masa ciyawa ta ba shi ruwan sha sannan ta share ma dokin makwancinsa. 

Sannan sai Ibnul Ƙayyim ya kwararo mazhabobin malamai da hujjojinsu, kafin a ƙarshe ya tiƙe izuwa ga cewa hidimar miji wajibi ce akan kowace matar aure, ba bambamci tsakanin ‘yar manya da ‘yar talaka, ko ‘yar sarki da ‘yar bawa, ko ‘yar masu kuɗi da ɗiyar matalauta ko malama da jahila da sauransu.

Uthaimin yana cewa: “dangane da aikin mace a gidan mijinta, wannan wani abu ne da ke komawa zuwa ga al’ada. Duk abin da a al’adance an saba mata suna yi wa mazajensu to shine abin da ya wajaba ta yi wa mijinta. Amma miji bai da ‘yancin ya tursasa wa matarsa yi wa mahaifansa hidima ko kuma ya yi fushi in ta ƙi yin hakan. Kuma ya wajaba akan miji ya ji tsoron Allah a cikin al’amuransa”.

A ƙarshe, abin da za a iya cewa shine, aikin gidan miji da mata suka saba yi wani abu ne sananne a cikin al’adar Musulmi tun zamanin Manzon Allah (SAW) har zuwa yanzun da muke rayuwa. Matan aure sun kasance suna hidima wa mazajensu, suna dafa abinci suna wankin tufafin maigida da na yara, suna wanke-wanke da shara da kai ruwan wanka banɗaki da kula da yara da sauransu. Kuma wannan al’adar ba a taɓa samun wani zamani da al’ummar Musulmi ta yi inkarin ta ko ta yi tawaye gare ta ba. 

Sannan kuma aikin gida da mata ke yi hanya ce ta samun lada da neman aljannar Allah (SWT). Amma kuma, bai kamata miji ya ƙuntata wa matarsa ba ko ya sanya ta ayyuka masu wahala waɗanda ba za ta iya ba. Sannan kuma yana daga cikin hanyoyin kyautatawa, maigida ya dinga taya uwargida yana kama mata aikin kamar yadda Manzon Allah (SAW) yake yi. In kuma yana da hali da buƙata to ba laifi a ɗaukar mata mai aiki.

Allah shine mafi sani.  

Kabir Asgar 
26/03/2020

Post a Comment

0 Comments