LITTAFIN FIQHU (DARASI NA TARA)



MENENE YA HARAMTA GA MACEN DA TAKE YIN JININ HAILA?:

Malamai sun ƙirga abubuwa guda takwas, waɗanda suka haramta ga macen da take yin jinin haila, kamar haka:

1. Ba a saduwa da ita saduwar aure . Idan mutum yana da mata tana yin jinin al’ada, haramun ne ya sadu da ita tana yin wannan jinin, amma zai iya rungumar ta, ko ya yi mata sumba (kiss) ko kuma ya saka gabansa a matse-matsin cinyarta domin biyan buqatarsa. Amma ta saka wando ko siket domin kada abin ya wuce zuwa ga saduwa da ita. Saboda Allah ﷻ Ya ce: “Kar ku kusance su har sai sun yi tsarki.” Kuma Annabi ﷺ, a hadisin Anas (رضي الله عنه), ya ce, “Ku aikata komai ga iyalanku sai dai saduwa.” Don haka, mutum yana iya jin daɗi da matarsa idan tana jinin al’ada, amma fa ya kiyaye kada ya sadu da ita. Saboda hadisin Nana A’ishah (رضي الله عنها) ta ce, Manzon Allah ﷺ “Idan yana so ya rungume ta tana jinin al’ada, sai ya ce ta ɗaura zani, ta ɗaura gyauton ta.” ()
Haka a wani hadisin ya ce: “Idan yana son ya yi wani abu da matarsa, kuma tana jinin haila.” (ma’ana, yana so ya rungume ta ko sumba) to sai ya ce "ta rufe gabanta.”

MENENE HUKUNCIN WANDA YA SADU DA MATARSA TANA CIKIN JININ HAILA?:

Babu saɓani tsakanin malamai cewa haramun ne mutum ya sadu da matarsa tana al’ada. Idan kuwa mutum ya sadu da matarsa tana haila, to ɗayan abu huɗu ne ya faru. Ko dai jahili ne bai sani ba ya sadu da ita da jahilci,
ko kuma kuskure ya yi, ya ɗauka jinin bai zo ba sai da ya sadu da ita ya ga jini,
ko kuma ganganci ya yi, ya san tana jinin ya je ya sadu da ita,
ko kuma dole aka yi masa ya sadu da matarsa alhali tana cikin al’ada ɗin,
ko kuma ita matar ce ta ɓoye masa cewa tana jinin haila, bai sani ba sai da ya sadu da ita, sannan ya gano.
To in dai ya sadu da ita da gangan, wannan shi ne ya aikata laifi , domin ya keta dokar da Allah ﷻ Ya shimfiɗa masa cewa:
﴿ وَلاَتَقْرَبُوهُنَّ حَتَّى يَطْهُرْنَ ﴾ ()
Ma’ana, “Kar ku kusanci mata har sai sun yi tsarki.”

ME YA KAMATA WANDA YA AIKATA HAKAN YA YI?:

Ya yi nadama, ya tuba, ya yi alqawarin ba zai sake komawa ba. Wato, sai an sami abu uku: nadama, ya daina, ya yi alƙawarin ba zai sake ba. Shin akwai kaffara a kansa? Akwai hadisin da ya zo cewa, “Wanda ya sadu da matarsa tana cikin jinin al’ada, sai ya yi sadaka da dinare ko rabin dinare, shi ne kaffararsa.” Kuma ya tabbata daga ruwayar Abdullahi ɗan Abbas (رضي الله عنه) cewa ya yi fatawa da haka kuma ba wai Annabi ﷺ ne ya faɗa ba, shi ya yi fatawa da hakan. 

Don haka abin da ake biya gwargwadon wannan kaffara dinare ko rabin dinare, dinare shi yake dai-dai da gram huɗu da ɗigo biyar, wanda kuɗinsa yake dai-dai da naira dubu sittin, (6o,ooo) da aka ƙiyasta a yanzu. Saboda dubu sittin sau dubu ɗaya, shi ne miliyan sittin, wanda shi yake ba da diyyar rai a wannan lokaci. Sai mutum ya ba da wannan bayan ya tuba ya yi kaffara.

2. Ba a sakin mace idan tana yin jinin al’ada, domin Allah ﷻ Ya ce: “Ku sake su a lokacin da za su fuskanci iddarsu.” Don haka haramun ne mutum ya saki matarsa tana cikin haila. Saboda hadisin Abdullahi bin Umar (رضي الله عنه) ya saki matarsa tana jinin al’ada. Manzon Allah ﷺ ya ce: “Maza ka umarce shi da ya mayar da ita, sai ta yi tsarki ta kuma yin jinin al’ada, sannan ta kuma yin tsarki, ta kuma yin jinin al’ada, sannan ta yi tsarki. Idan ya ga dama ya riƙe ta, idan ya ga dama ya sake ta, kafin ya sadu da ita.” Wannan ita ce iddar da Allah ﷻ Ya yi umarni a saki mata a cikinta.
Don haka idan mutum zai saki matarsa kada ya sake ta tana cikin jinin al’ada ko jinin jego, kada ya sake ta saki uku a kalma ɗaya, kada ya sake ta bayan ta yi tsarki, kuma ya sadu da ita a cikin wannan tsarkin.

3. Ya haramta mace ta yi sallah idan tana cikin jinin al’ada. Saboda hadisin Nana A’ishah (رضي الله عنها) da take cewa, “Mun kasance idan mun gama al’ada, ana umartar mu da mu rama azumi amma ba a umartar mu da mu rama sallah.”

4. Yin azumi: Idan mace tana yin jinin al’ada haramun ne ta yi azumi. Malamai sun haxu a kan haka. Saboda hadisin da aka ruwaito daga Abu Sa’idul Khudhri (رضي الله عنه) cewa, Manzon Allah ﷺ Ya ce: “Idan mace tana haila ba ta sallah, ba ta azumi.” Da kuma hadisin Nana A’ishah (رضي الله عنها) wanda ta ce, “Mun kasance ana umartar mu da mu rama azumi amma ba a umartar mu da mu rama sallah.” 

5. Karatun Alqur’ani: Shin mace za ta karanta Alqur’ani idan tana cikin haila ko ba za ta karanta ba? An yarda ta karanta ayoyi daga cikin Alqur’ani domin neman tsari, amma ba karatu irin wanda aka saba ba. Amma ƙaulin da ya fi rinjaye shi ne, mace tana iya karanta Alqur’ani idan tana cikin haila ta hanyar yin tilawa.

6. Ɗaukar Alqur’ani: Akwai maganganu guda uku da malamai suka yi a game da ɗaukan Alqur’ani ga mace idan tana jinin haila:

Malamai na farko suka ce ba za ta ɗauki Alqur’ani ba kwata-kwata, sai dai ta dinga karantawa da ka. Saboda hadisin da ya zo cewar, mutum ba zai ɗauki Alqur’ani ba sai yana da tsarki. Sai suka fassara tsarkin da cewa, ana nufin tsarki daga jinin al’ada da janaba.

Wasu suka ce za ta iya ɗaukan wani sashi ko wata sura, amma ba Alqur’anin dukkansa ba.
Waɗannsu kuma suka ce za ta iya ɗaukan Alqur’ani, matuqar dai ta wanke hannunta, domin dama abin da ake gudu shi ne, kada ƙazanta ta taɓa Alqur’ani.

Waɗannan su ne maganganu guda uku na malamai wanda su ne suke yawo a duniya kuma kowa daga cikin ɗalibai yana rinjayar da ɗaya daga cikin ukun nan. Wanda ya ɗauki ra’ayin farko, sai ya ce kwata-kwata mace ba za ta taɓa Alqur’ani ba sai dai ta yi tilawa da ka. Wanda ya ɗauki ra’ayin malamai na biyu sai ya ce mace za ta iya ɗaukan Alqur’ani, amma ba duka ba sai dai wani ɓangare. Wanda ya ɗauki maganar malamai na uku sai ya ce za ta iya ɗaukan Alqur’anin dukkansa, matuqar dai hannunta yana wanke, domin dama abin da ake gudu kada qazanta ta taɓa Alqur’ani. Idan ta wanke hannunta za ta iya ɗaukan Al’qur’ani izifi sittin musamman ga ɗaliba mai neman ilimi, da wadda za a saka ta ta yi rantsuwa da Al’qur’ani, da makamantansu. Wanda dama a Shari’a idan za a yi rantsuwa ba sai an riƙe Alqur’anin ba, domin a tsorata mutane su ga girman Alqur’ani wajen yin rantsuwa.

7. Ɗawafi: Ba ya halatta ga mai jinin al’ada ta yi ɗawafi da ɗakin Allah ﷻ. Saboda hadisin da ya zo, Annabi ﷺ yake cewa Nana A’ishah (رضي الله عنها) “Ki aikata duk abin da mai aikin Hajji yake yi, sai dai ba za ki yi ɗawafi da ɗakin Allah ba, har sai kin sami tsarki” () 
Haka nan Annabi ﷺ ya gayawa Safiyyah (رضي الله عنها) lokacin da take jinin al’ada, ya ce: “Za ki tsare mu ne?” Sai aka ce ai ta riga ta yi ɗawafin ifadha. Sai ya ce: “To ta shirya mu tafi.” ()  

8. Zama a cikin masallaci: Haka kawai mace ta shiga cikin masallaci ta zauna tana jinin al’ada ba tare da wata lalura ba, shi ma ba a so. Saboda dalilai kamar haka:

Na farko, hadisin da ya zo cewa Annabi ﷺ ya cewa Nana A’ishah (رضي الله عنها): “Ki aikata dukkan abin da mai aikin Hajji yake aikatawa, sai dai ba za ki yi ɗawafi da ɗakin Allah ﷻ ba, ba za ki shiga ɗakin Allah ba wanda masallaci ne har sai ta yi tsarki.” 

Hadisi na biyu, Annabi ﷺ yana cikin masallaci ya cewa Nana A’ishah (رضي الله عنها) “Miƙo min mayafi.” Sai ta ce, ai ina haila. Sai ya ce, “Ai hailarki ba a hannunki take ba.” Ma’ana, kenan ta san mai haila ba ta shiga masallaci, shi ya sa da ya ce miƙo min, ta ce ina haila.

Sannan akwai hadisi na Safiyya (رضي الله عنها) wanda Annabi ﷺ ya ce: “Tsare mu za ta yi? (Ma’ana, sai mun jira ta ta gama jinin al’adarta ta je ta yi ɗawafi?” Sai aka ce ai ta riga ta yi ɗawafi. Sai ya ce, “To shi kenan ta shirya mu tafi.” 
Da kuma hadisin da Nana A’ishah (رضي الله عنها) take cewa, “Suna cikin i`ttikafi mata masu i`ttikafi, idan suka yi jinin haila, Annabi ﷺ yakan yi umarni da su fita daga cikin masallaci.”

Da kuma hadisin Ummu Aɗiyyah (رضي الله عنها) wanda ya zo cewa, “An umarci mata da su dinga zuwa sallar idi, amma masu jinin al’ada su koma gefe, kada su shigo cikin masallaci, kada su yi sallah.” Saboda su halarci addu’ar da Musulmi suke yi.
Allah ne masani 

Za mu ci gaba insha Allah.

Post a Comment

0 Comments