Hanyoyin Kula Da Lafiyar Jarirai Domin Samar Da Yara Masu Koshin Lafiya:





Jarirai mutane ne masu rauni wato ba su da garkuwar jiki mai karfi da za ta iya yakar cuttukan daka iya kama su, saboda haka ba su cikakkiyar kulawa wajibi ne a kan mu. Abubuwan za mu dunga yi sun hada da sanya musu kayan sanyi da share hancinsu yayin da yake toshewa da kare su daga iskar fanka ko AC daka iya dauko kwayoyin cuta zuwa gare su wanda ke iya shafar hanyoyin numfashisu, sannan kuma iyaye mata su dunga cin musu nau’in abinci masu inganci da zai amfani jikinsu ta hanyar shan nono. Wajibi ne a irin wannan zamani da muke ciki kai yara alluran rigakafi domin kula da lafiyarsu musamman wadanda ake ma yara daga zarar haihuwa na (BCG da HBB) domin kare su daga hatsarin kamuwa da kwayar cutar tarin TB. (Tuberculosis) da ciwon hanta rukunin B.

Hikimar yin hakan a ranar da aka haifi yaro shi ne, ana samun mutane ‘yan barka da ke tururuwar zuwa ganin jariri musamman yankunanmu na karkara, kowacce burinta a ba ta dan ta dauka, wata a jikin tufafinta kuma ba a san me ta debo a hanya ba na kura da iska. Haka wata ita kanta kila tana fama da ciwo irin su tari da sauransu. Kun ga sanda ta rungumi jaririn nan komi na iya faruwa wanda ka iya cutar da yaron, amma karshe sai ka ji uwa na ai baki ne ya kamashi kowa sai ya ce kai wannan yaro katoto haka. Amma azahiri ba wani baki sakaci ne kurum, dan haka ko da an yi wa yaro irin wannan alluran, ki samu net din saka jarirai ki tura danki ciki duk wacce ta shigo an haihu! Eh an haihu ga yaro can yana bacci. To Allah raya amin. Hakan ya wadatar gara aleka a gan shi ya fi kowacce ta zo a ce sai an mika mata duk abu a gaji da yaro. Ba ruwanki da surutun da za a yi, gara surutun kin hana dan da a barku da ciwo kuna kwana ba bacci.

Haka kuma kamar yadda nasha fada a baya, iyaye mata ya kamata su kara kulawa bayan farkowar jariri daga bacci ko yana kuka ko ba ya yi, ba ruwa ya kamata ake dura masa ba, nono yake bukata, a daina ba su ruwa kai tsaye sai bayan sun sha nono.


Ruwan da ake ba su shi ke sa da yawa ba sa girman da kuke so, sai dai ku rika hangen ‘ya’yan wasu kuna sha’awa. Kuma shi ke sa wasu yaran fama da gudawa suna ramewa.

Bayan kin gama ba yaro nono, kar ki abun nan da mata suka jima suna yi wato kurum ki ja salebar nono ki mayar cikin riga. Wannan kuskure ne, hakan na fitar da kwayoyi cututtuka a duk yayin da kika gama ba da nono, an so ki sa ruwa ko tsuma mai lemar ruwa inda hali mai dumi ki goge kan nonon da shacin jikin nonon sannan ki mayar cikin riga, hakan na kare jarirai daga tsotsar dattin daka iya sa su zawo, saboda haka a kula.

Bayan gama shayar da jariri nono kada ki sake ki tintsirar da shi wato ki maida shi gado ki kwantar wannan kuskurene. Ana so ki dora shi a kafada kina jijjiga shi a hankali kina shafa bayansa zuwa can za ki ji ya yi gyatsa alamar ruwan nonon ya tsirga masa, hakan zai sa da kin koma kin kwantar da shi zai ci gaba da baccinsa domin ya koshi. Amma in kin ji bai yi gyatsa ba alama ce ta nono bai ishe shi ba, dan haka ki tashi zaune ki ci gaba da ba shi nono.

Yawancin jira-jirai sabbin haihuwa a kan haife su da nauyin kilograms biyu da digo bakwai (2.7kg) zuwa kilo hudu (4kg), ka dan ke haura hakan. Sannan yaron da ya gaza kilo 2, wannan ya kasance wanda ba a son ganin haka domin yana nuna uwa ba ta samu ingantacciya kulawa ba yayin goyon cikin ko kuma ambar ta ta yi ta fama da cututtuka musamman malariya.

Sai dai ko da an haifi yaro da cikakken nauyi bayan kwana 3 zuwa 4 da haihuwa nauyin yaron kaso 5% zuwa 10% yana raguwa komi kulawar da ake ba shi, wannan ba matsala ba ne dan an ga haka. Sannan tsayin jariri in ya kasance namiji yana zuwa ne tsawon santimita 50, yayin da mace ke zuwa a santimita 49.

Daga lokacin da jariri yakai watanni 6 zuwa 12, ana tsammanin nauyinsa na haihuwa ya rubanya kansa yakai ninki uku. Wato in an haife shi yana da 3kg daga sanna yakai wata 6 har zuwa cikar shekara ana tsammanin yakai 9kg. In ba haka ba, hakan na nuna baya samun cikakkiyar shayarwa da ingantaccen abinci saboda haka sai a kiyaye.

Za ki iya sanin nauyin danki da kanki ta hanyar lissafa yawan watanninsa a duniya ki tara da iya adadin watannin ciki wato wata tara, sai ki raba zuwa gida biyu.

Post a Comment

0 Comments