🤱🤱🤱🤱🤰🤰👨🍼🧑🍼🧑🍼🤱🤱🤱🤱🤱
Babban hatsarin da haihuwa ke zuwa dashi dake jawo asarar rayukan Mata bayan haihuwa shine zubar jini bayan haihuwar wato Post Partum Hemorrhage a likitance dake faruwa a stage na uku na haihuwa. Wannan shine lokacin da dariya ke rikidewa ta komk kuka, wato murna ta koma ciki, daga murnar haihuwa akoma kukan mutuwa.
____________________1___________________
Sau tari wanda baisani ba zai tunanin fitar yaro shine haihuwa lafiya, shine mafi mahimmanci. Amma wannan bashine haihuwa lafiya ba. Haihuwa lafiya shine aga bayan fitar yaro Mahaifa ta murda ta harba wato contracton ta yadda hakan zai sanadiyar fitowar placenta wato (mabiyiya ko abunda hausa kance uwa ta biya). Kai wani lokacin koda uwa ta biya akwai bukatar sai mahaifa tai wannan harbawar... idan bata harba ba hakan bazaisa jijiyoyin jini su toshe ba don haka mace zata ci gaba da zubar da jini... wanda wannan shike kashe Mace. Wani lokacin hatsarin placenta din ce ma ke manne mahaifar ta yadda in aka jawo saide ta taho hade da mahaifar ta tidota. Shiyasa haihuwa tsallake siradi ce ba karami ba.
________________________________________
Toh abunda ke taimakawa wannan harbawar shine ai maza maza ai stimulating nonon mace, shyasa wani lokacin ma in mace na naquda akan iya bukatar akawo yaron da take shayarwa domin ya kama nonon hakan zai taimaka wajen contraction din mahaifarta, ko kuma inba yaro ace mijinta ya tsaya ya rika kama nononta, inbabu duk daya saide nurses sui mata.
Toh waccan hikimar ta stimulating nipple nada matukar mahimmanci har bayan haihuwa, wannan.tasa game kallon finafinan likitoci na haihuwa zakuga da anciro yaro cikin jininsa da komi za'a dora ma.uwa shi ya kama nono domin ya taimakamata yasa mahaifarta harbawa jinin haihuwa ya tsaya... wannan shine hikimar skin to skin, nan da nan zakuga likitoci sun dorasa a nono.. saboda hatsarin daka iya biyo baya.
Haka zalika wannan jinin haihuwar duk da anfi ganin zubarsa nan da nan bayan haihuwa cikin awa 24 na yini... Haka zalika kananun ma'aikatan lafiya kusani yana iya faruwa tun daga bayan kwana 1 da haihuwa zuwa sati 6.... Matukar Macen da akasan ta haihu kasa da sati 6 tazo asibiti da complaint na zubar jini to kusani yana iya kasancewa Post Partum Hemorrhage har sai In kun gano wani abun daban... don haka a lura dakyau, kar adau zubar jini matsayin ba serious abu ba don kurum kila anyi satuttuka da haihuwa ko kwana 3 uku.
___________________2____________________
Haka zalika koda baki fuskanci matsalar zubar jini ba ki daure ki shayar da babynki hakan zaici gaba da sa mahaifarki harbawa ta taso daga mararki ta koma kasan cikinki cikin sati 2 da haihuwa, hakan zai rage miki tsananin ciwon mara duk da shayarwa kwai zafi wani lokacin.
________________3_______________________
Bayan haihuwa ke ýa mace kisani kazanta ba taki bace, baki daya tsaftarki dole ki nunkata, walau C/s akai miki ko kuwa normal da kanki kika haihu it does'nt matter.
Musamman tsaftar mara, matse-matsi zuwa farji kada ki wasa, saboda kinga a lokacin kina fitar da abunda muke kira Lochia wanda ake kira jinin nifasi... wannan na dada saki vulnerable to infection. Sannan ki guji amfani da kayan matsi da sauransu kasa da sati 12 na haihuwarki, inma bazaki iya bari ba. Saboda in ma kinki muna jiye miki tsoron endometritis ko sepsis.
________________4_______________________
Kina iya yin wankanki koda aranda akai miki C/s ne, saide ya zamto kina d akayan dressings duk sanda kikai wanka gurin ya jike ki zaune ki cire audugar, da bandage din ki wanke gun da iodine ki canza sabon dressing din gun shikenan. Inbaki da kayan yin hakan toh ki guji jiqa gurin ake kebesa in anzo wanka. Sannan duk bayan kwana 3 kya iya zuwa aduba ko anemo ma'aikacin lafiya; ade tabbatar gurin baya fidda ruwa inma yana ruwa toh atabbatar bame jini-jini bane. Saboda gudun samuwar surgical site Infection da yana iya sa kwayoyin cuta suita cin fatarki hankali suna qarawa gurin girma kizo ki shiga masifa. Kinura da duk wani canji da zaki gani agun, karki kasa aguiwa kima likita waya
__________________5_____________________
Galibi bayan haihuwa cikin Mata kan bude, kwai cin abinci... Babu komi hakan bazaisa ki nauyi fiyr da kima ba muddin kina shayarwa, nauyin bazai canza daga yadda yake ba kafin ki ciki abaya.
_________________6______________________
Bayan kwana 3 zuwa 5 da haihuwa galibi nono ke fara cika tsir-tsir ya rika ciwo. Koda sha yaro yake yana zafi... don haka ba matsala bane ki rika matsewa wani kaso saboda ki sami relief. Kda duk sanda kikaji ciwo kice dole dai jariri yasha alhalin ya koshi, wannan kesa su yawan tumbudi. Muddin kikaji jaririnki na gyatsa tare da yawan tsilla fitsara hakan alamace ta kyakkyawar shayarwa don haka in nono na miki ciwo dalilin cika kike matsewa kina ragesa.
_________________7______________________
Wasu kanji ana cewa shayarwa na hana daukar ciki abunda ake kira lactation amenorrhea wanda hakan ke a amatsayin kamar hanyar planning, amma abunda bakusani ba shine sai macen dake shayar da yaro akalla duk bayan awa 4 zuwa 6 ce ke samun wannan benefit din, wato akaikai akalla sau 6 zuwa 7 arana. SANNAN kusani hakan na tasiri ne kurum tsawon watanni 6, wato adadin watanni Exclusive freeding, domin ga wacce ta cika watannin haihuwa cif ovulation dinta na dawowane bayan sati 6, wacce ta haifi bakwaini kuma ovulation dinta na dawo mata bayan sati 4, yayin da wacce tai bari ovulation na dawo mata bayan sati 2.
Don haka daga wata 6 saide ki za6i hanyar planning daban walau magani ko de wata hanyar, inkinga baki sami ciki ba toh bakya ovulating kin taki lucky ne kurum. Amma maganin ma na plannin banda shan COMBINATION PILLS Muddin kina shayarwa saboda zasu kawoma shayarwa matsala, zasu hindering milk production dalilin estrogen, saide ki amfani da magani mai progestin kawai... don haka kananun ma'aikatan lfy fatan zaku kiyaye wannan.
__________________8_____________________
Ciwon nono ba bakon abu bane galibi saboda bacteria din da ake smau asaman fata dakan shiga ta kafar nono ko ta nitsa cikin fata idan akwai karancin tsafta. Shyasa nake cewa ki gama ba yari nono kurum kija sale6ar bra din ki mayar, A'a ki samu tissue ko towel ki dangwali ruwa ki goge kan nonon sannan ki mayar, haka shima jaririn kinsa ruwa ki share masa nasa bakin.
Sannan idan kan nono ya tsage muddin yana miki ciwo karki azabtar da kanki cewa dole sai kinba yaro ya kama ahaka. Ki bashi dayan... shi kuma mai tsaguwar ki rika matse ruwa daidai da wanda ake sha kina zubarwa, Is normal.
___________________9____________________
Koda babu tsaguwa abunda ke jawo muku ciwo yayin shayarwa shine; dorawa jariri iya kan nono ya kama. Inde zaki ke dosana masa nipple dole kiji zafi, Areola wannan sahin duhun baki daya shine zaki tabbatar labbansa na tabawa, shi jariri bada lebe yake jawo nono ba... shyasa mace dake shayarwa koda mijinta zaice zai kama nononta ya tsotsa saide taji zafi bazai ta6a iya zuqowa ba dan besan ya zai ba yazo amma in jariri ya kama sai kaga har biyo kumatunsa yake. Don haka ki samu contact me kyau har gemun jaririnki yake dungurar nonon
___________________10____________________
Zaki iya shayar da jaririnki har shekaru biyu. Hakan zai baki kariya daga ciwon cancer nono data sassan haihuwa, tare da kiyayeki daga hatsarin kamuwa da ciwon jijiyoyin jinin zuciya [coronary artery dx]
Kai kuma megida ka nuna karamci asamo mata kayan marmari da fruits🍌🍋🍊🍉🍇🍏🍓🥬🥒🥭🍍 da nama akai-akai musamman hanta har sati 6 bayan haihuwa.
__________________11_____________________
Kuskure ne baiwa mace maganin dakatar da zubar ruwan nono. Kusani physiologic process ne don haka akoya ma macen dabaru, inciwo yake abada maganin ciwo. Amma banda basu hormonal drugs don Allah akiyaye kwai illa karkuje ku lalata musu pituitary gland ku kashesu da ransu, domin shikenan kurum hakan na faruwa mace ta dena haila, ta den ovulation, ta dena jin sha'awa, ta dena komi irin na mutane rayuwarta ta zama maleji. Akwai abunda ke kira sheehan syndrome abunda ake gudu kenan. Ashir dinku da bawai mace maganin tsaida ruwan nono saide in kasan kai gynecologist ko medical doctor ne.
__________________12____________________
Galibi abunda na kance ga masu zubar ruwan nono shine; suke ragesa ahankali suna shan maganin rage zogi Irinsu ibuprofen.
Inkuwa yaye zatai ko kuwa jaririn ne ya mutu... toh a samo kabeji madaidaici... inda hali asa cikin freedge yadda zai dau sanyi. Ko cikin roba ko randa sai asaka ice block... inkuma duk ba halin ķanqara ko freezer sai ai amfani dashi a yadda ya samu amma de a wankesa tukun.
Daga nan inyai sanyi saiki yagi ganyen daidai girman wanda zai rufe nononki rijif kamar yadda hoton kasa ya nuna...
Saiki dau rigar nononki ki mayar wato kitareshi da ita, musamman adan tsuke number bra din yadda zata kamesa amma ba tsam inde zai dameki da ciwo ba... sai ki barsa kici gaba da harkokinki har zuwa awa 1 koma awa 2 ya zamto de sai kinji ya jike da zufa toh sai acire. Kya iya canza wani a lokacin ko ki bari sai anjima ki kara sa wani. Kar kuma ake takure bra din... abarta saisa-saisa yadda bazata dameki ba.
Kike yin haka sau 3 yini, safe, rana, yammah... kita yi kurum har zuwa lokaci ko kwanakin da kikaga ya tsaya ya dena zubar.
_______________________________________
Fatan bayanin ya ilmantar. Nagode muku bisa yadda bakwa gajiya da bibiyar rubutuna, Allah yai albarka, ya taramu a aljanna baki daya. #Jumat_Mubarak
_______________________________________
"✍🏼
[Ibrahim Y. Yusuf]
𝗜𝗯𝗿𝗮𝗵𝗶𝗺 𝗬. 𝗬𝘂𝘀𝘂𝗳
0 Comments