Fason kafa ya kan zamewa mutane karfen kafa musamman ma a lokacin sanyi, ko a yankunan da suka fi bushewa fiye da wasu.
Wannan ya na faruwa ne saboda fatar kafa ta fi ta sauran sassan jiki bushewa kuma tana bukatar kulawa ta musamman wanda yawancin lokuta ba ta samu.
Rashin kula da faso ka iya ta’azzara shi ta yadda zai iya fara jini, ko ciwo ko kuma kwayoyin cuta su shiga ciki.
Ga wasu hanyoyi biyu masu sauki da za’a iya magance wannan matsala.
1. Hanya ta daya: Amfani da Ruwan Kal (Farin Vinegar ko Apple Cider Vinger)
i. Za a zuba ruwa a cikin babbar roba,
ii. Sanna a zuba ruwan kal kamar 1/4 na Kofi daya.
iii. Sai a jika kafar a ciki na tsahon minti 10 zuwa 15.
iv. A yi amfani da Dutsen kaushi wajen gurje fatar da ta jiku.
v. Sai a yi amfani da farin ruwa wajen dauraye kafar.
vi. Bayan a goge ta da tawul mai tsafta, sai a shafa man kwakwa, ko Zaitun ko kuma man Kadanya.
vii. Za a maimata sau uku a sati
Hanya ta Biyu: Amfani da baking soda
i. Za a zuba ruwa a roba mai fadi, Sannan a zuba cokali uku na baking Soda a ciki.
ii. A saka kafar a ciki na tsahon minti 15 sannan ayi amfani da sutsen kaushi wajen gurje ta.
iii. A dauraye da farin ruwa a goge ta da Tawul mai tsafta.
vi. A shafa mai.
v. Shima ana maimatawa kamar sau uku a sati.
Za a iya samun baking Soda a guraren da ake sayar da kayan hada Cake ko kuma Manyan shaguna ko Supermarket, Shi kuma ruwan Kal an fi samun shi a Supermarket.
0 Comments