LITTAFIN FIQHU (DARASI NA SHA HUƊU.)



BUTAR DA AKE ZUBA RUWAN WANKA KO ALWALA:

Kafin mutum ya fara alwala ya duba abin da aka zuba ruwan a ciki tukunna,
Jakar fata ce, kamar salka, 
ko butar qarfe, 
ko ta roba 
ko ta gwal
ko ta azurfa
ko wacce aka yi da gashi
ko ƙashin wata dabba.
Domin Shari'ah ta hana alwala a cikin butar zinare, da azurfa da kuma fatar mushe wacce ba a jeme ta ba kamar yadda ya tabbata a hadisi.

ABUBUWA GOMA SHA ƊAYA DA AKE SO A YI ALWALA KAFIN A YI SU. 
1.Idan za a ambaci Allah ﷻ a yi alwala.
2. Idan za a yi bacci an so a kwanta da alwala. 
3. Lokacin da za a yi karatun Alkur`ani Mai Girma.
4. Idan mai janaba zai ci abinci ko zai sha ruwa ko zai yi bacci an so ya yi alwala.
5. Idan mutum zai yi wankan janaba ya fara yin alwala domin an so haka.
6. Duk sanda mutum zai yi sallah, yana da alwala an so ya jaddada don samun haske a kan haske. Allah ﷻ Ya yi umarni da yin alwala idan za a yi sallah, kuma hadisai masu dama sun zo da bayani a kan falalar yin alwala.
7. Sunnah ne ya zamo kullum mutum yana cikin alwala, idan ta warware ya yi wata.
 8. Idan mutum ya yi amai ko kumallo ana so ya yi alwala.
9. An so wanda zai ɗauki gawa zuwa maƙabarta ya yi alwala.
10. An so mai karanta Alkur`ani ya zama yana da alwala, saboda idan ya zo wajen yin sujjada sai ya yi da alwala.
11. Idan matum ya sadu da iyalansa kuma yana sha'awar komawa ya yi alwala, domin hakan yana ƙara nisaɗi.

ABUBUWAN DA SUKA HALATTA A YI ANA CIKIN ALWALA
Idan mutum yana cikin yin alwala ya halatta ya yi magana idan buƙatar haka ta taso babu laifi.
Idan mutum ya gama alwala babu laifi ya goge danshin ruwa da tawul ko tissue.
Idan mutum yana alwala wani zai iya taimaka masa da zuba ruwa .
ABUBUWAN DA AKE YIWA ALWALA
Alwala tana wajaba saboda yin abubuwa guda biyu: sallah ta farilla ko nafila, da yin ɗawafi na farilla da nafila da Ɗakin Allah mai tsarki wato Ka'abah. Da ɗaukar Alkurnani mai girma, a mafi rinjayan magana.

FATAWOWI 28,KAN ABUBUWAN DA SUKE WARWARE ALWALA GUDA. 
Abubuwan da suke warware alwala suna da yawa. Wasu daga ciki malamai sun haɗu a kan cewa suna warware alwala, saboda ƙarfin dalilansu, wasu abubuwa kuma sun yi saɓani a kansu. Daga cikinsu akwai:
1.Duk wanda ya yi kashi alwalarsa ta warware, dole ya sake wata kafin ya yi sallah saboda Allah ﷻ ba zai karɓi sallar wanda ya yi kari ba, har sai ya yi alwala.
2. Duk wanda ya yi fitsari alwalarsa ta warware sai ya sake wata kafin ya yi sallah.
3. Duk wanda ya yi tusa, alwalarsa ta warware. Wajibi ya yi wata kafin ya yi sallah.
4. Duk wanda maziyyi ya fito masa yana da alwala, sai ya sake alwala kafin ya yi sallah. Maziyyi yana fitowa ne saboda dalilai masu dama, kamar shafar mace da sha'awa, tunanin jima'i, kallon sha'awa, kallon finafinan batsa, maganganun batsa masu tayar da sha'awa da makamantansu. Duk lokacin da maziyyi ya fita alwala ta warware, sai an sake wata kafin a yi sallah, sai idan mutum ba shi da lafiya, maziyyi yana fita kodayaushe. Wannan zai dinga yin alwala duk lokacin da zai yi sallah, amma idan yana cikin sallah maziyyin ya fito ba zai yanke sallar ba .
5. Fitar wadiyyi yana warware alwala. Shi wadiyyi yana fita ne a ƙarshen fitsari kuma yana da kauri.
Wani ruwa da yake fitowa mata ta gabansu, a wasu lokuta, suna kiransa ruwan ni'ima, shi ma ba ya ɓata alwala a mafi rinjayen dalili.
6. Idan aka yiwa mutum aiki a mafitsararsa aka saka masa roba, fitsarin yana fita ta roba, shi ma alwalarsa ta warware, sai idan ba ya tsayawa, ya zama mai yoyon fitsari, sai ya dinga yin alwala duk sanda zai yi sallah.
7.Matar da take da larura ta yoyon fitsari ita ma za ta dinga yin alwala duk lokacin da za ta yi sallah.
8. Wanda jini yake fito masa ta dubura, saboda basir ko tsutsa, tsakuwa da makamamtansu, saboda larura, zai dinga yin alwala a duk lokacin da zai yi sallah, amma idan ya fito masa yana cikin sallah zai ci gaba da sallarsa.
 9. Fitar jini ko yin kumallo ba ya ƙarya alwala. Don haka wanda ya ji rauni yana da alwala ba ta warware ba, sai ya yi sallah abin sa, amma ya tabbatar ya wanke jinin da kuma kumallon.
10. Bacci mai nauyi yana warware alwala, ko ya yi tsawo ko bai yi tsawo ba, matuƙar ya yi nauyi. Ana gane nauyin bacci ne, idan mutum yana bacci ba ya jin abin da ake yi a kusa da shi. Amma bacci mara nauyi ba ya warware alwala.
Bacci gajere mai nauyi yana warware alwala.
Bacci dogo mai nauyi yana warware alwala.
Bacci dogo mara nauyi ba ya warware alwala, amma an so a sake alwala domin a shiga sallah da nishaɗi.
Bacci gajere mara nauyi baya karya alwala.
 11. Alwala tana warwarewa da gushewar hankali, domin idan mutum ya sha kwaya, ko giya ya bugu zai iya yin tusa ko fitsari ko kashi ba tare da ya sani ba.
12. Haka idan mutum ya yi alwala sai ya sami larurar farfaɗiya ko ciwon hauka, duka wannan sababi ne na warware alwala. Idan ya dawo cikin hankalinsa sai ya sake alwala .
 31 Alwala tana warwarewa da shafar mace, domin jin daɗi, da sha'awa kamar:
Wanda ya shafi mace domin ya ji daɗi, kuma ya ji daɗin alwala ta warware.
Wanda ya shafi mace ba domin ya ji daɗi ba, amma bayan ya shafe ta sai ya ji daɗin, alwala ta warware.
Wanda ya shafi mace ba domin ya ji daɗi ba, kuma bai ji daɗin ba, alwala ba ta warware ba.
Wanda ya shafa jikin mace domin ya ji daɗi, amma kuma bai ji daɗin ba alwala ta warware. Abin da ake lura da shi wajen shafar mace shi ne jin daɗi ko kuma niyyar jin dadin. Idan an sami ɗaya daga cikin biyun, alwala ta warware.
14. Shafar gaba, Idan mutum ya shafa gabansa da niyar biyan buqatarsa kuma ya ji daɗi kamar masu yin istimna'i wato fitar da maniyyi ta hanyar mulmula gaba ko wani ɓarin jiki, wannan laifi ne, kuma alwala ta warware. 15. Haka idan mace ta shafa gabanta har maziyyi ya fito alwala ta warware. Idan kuma ba da niyyar haka ba ne alwala tana nan. 16.Shafar dubura da matsematsin tsakanin cinyoyi da shafar marena da shafar gaban wani ba da niyar sha'awa ba, ba ya warware alwala.
17. Idan namiji ya shafi jikin namiji da niyyar sha'awa wannan ya zama fasiƙi, amma alwala ba ta warware ba, a mafi rinjayen dalilai, amma wanda yake yin haka fasikanci ya yi, Sai ya yi gaggawar nadama da tuba.
18. Idan mutum ya shafi wani ɓangare a jikinsa, ko ya shafi gabansa ta kan tsari, kamar wando ko riga, alwala tana nan, zai iya yin sallah idan babu abin da ya fito.
 19. Wanda ya ci naman raƙumi sai ya sake alwala, saboda hadisi ya inganta a kan haka, () amma idan ya sha nononsa ko ya ci kayan cikinsa kamar hanta, hanji, huhu da saifa ko kuma ya ci kitsen rakumin, waɗannan duka akwai saɓani. Abin da ya fi rinjayen dalili shi ne alwala ba ta warware ba, () sai ga wanda ya ci naman raƙumin kawai domin hadisin iya nama kawai ya kawo.
20. Idan mutum yana sallah sai ya yi dariya, sallarsa ta ɓaci, amma alwalarsa tana nan.
 21. Wanda ya yiwa mamaci wanka shi ma an so ya yi wanka, amma idan yana da alwala tana nan ba ta warware ba.
22. Wanda ya fita daga Musulunci bayan ya yi alwala, ma'ana ya yi ridda to ina maganar alwala ma tun da ya fice daga Musuluncin? Idan ya tuna nan take, sai ya sake alwala, ko kuma tana nan? Magana mafi rinjayen dalili, sai ya sake alwala bayan ya tuba.
 23. Mutumin da yake da larura ta fitar fitsari ko kashi ko maziyyi ko wadiyy ko tusa, kullum a cikin haka yake ya zama cuta, irin wannan abin da zai yi shi ne sake alwala duk sanda zai yi sallah. Ko da yana cikin sallah sai ya ji abin yana fita ba zai yanke sallah ba sai ya gama.
24. Idan mutum ya yi alwala sai yake kokwanto a kan karyewar alwalar, ya ci gaba da sallarsa, alwalarsa tana nan, domin kokwanto ba ya kawar da sakankancewa (yaƙini).
25. Idan mutum ba shi da alwala sai kuma yake zaton kamar ya yi, wannan dole ya sake alwala, domin ba shi da yaƙini a kan samuwar alwala a tare da shi.
26. Wanda ya tabbatar ya yi fitsari kuma ya tabbatar ya yi alwala, amma ya manta wanda ya fara gabatarwa, wannan shi ma dole ya sake alwala, saboda rashin tabbas a kan samuwar alwala ko rashin ta.
 27. Wanda yana cikin sallah sai ya ji kamar wani abu ya fito masa, ko ya ji kamar ya yi tusa, amma bai ji warinta ko sautinta ba, ya ci gaba da sallarsa, waswasi ne kawai yake samun sa.
 28. Wanda yake sallah sai ya ji fitsari ko kashi yana matsa masa, ya je ya fara gabatar da fitsarin tukunna domin ya sami nutsuwa, amma idan ya ci gaba da sallah a haka, sallarsa ta ɓaci, idan ba ya iya cika ruku'u da sujjada da rashin nutsuwa saboda ya matsu.
A duba waɗannan littafai, don ƙarin bayani
مختصر خليل
الرسالة
ملخص الفقه الإسلامي
صحيح فقه السنة
فقه السنة للسيد سابق

Post a Comment

0 Comments