Maza Ga Wasu Hanyoyin Da Zaka Tinkari Macen Da Kaganta Kana So A Hanya:



 

Yiwa macen da ka gani kana so a hanya magana ba sauki bane gareshi ba. Wannan yasa wasu maza da dama suke rasa macen da suka gani a hanya sukaji ta musu suna sonta.

Wasu mazan kuwa sukan yi karfin hali su tinkari matan, amma bada sigar da ya dace ba, don haka kodai taki saurarensu ko kuma ta saurarensu amma su kasa samun shiga.

A darusan mu na baya mun kawo wasu hanyoyi da dabarun tinkaren mace, a wannan karon ma ga wasu dabarun nan domin shawo kan macen da ka ganta kana so kuma bakasan Inda take ba.

 

1:Hanya na farko da zaka yi saurin jawo hankalin mace ta saurareka kuma bata sanka ba shine ta hanyar mata sallama.

Ganin yadda sallama yake da karfi kuma da mahimmanci a tsakanin Musulmai, da Kuma wajabcin amsawa wanda aka yi masa idan yaji kuma yana cikin natsuwa yasa duk macen da ka yiwa sallama muddin tana da tarbiya na addini zata amsa maka wannan sallamar taka, da zaran kuma ta fahimci magana kake son yi da ita zata tsaya.

 

2: Fara'a da murmushi sune abunda ya kamata ka yiwa macen da kayi mata sallama kuma ta amsa maka a daidai lokacin da kake gaiswa da ita.

Wannan fara'ar da murmushin tunin sun aika mata sakon abunda kake da niyar yi idan mace mai wayoce ita. Don haka daga wannan lokacin zaka fahimci idan zata saurareka ko kuma zata baka uzuri.

 

3: Idan zaka mata magana bayan sallama da Kuma gaisuwa, ka rika hadawa da abunda bature yake cewa (pleasant request) duk magana sai kace mata (Don Allah ko zan iya samun lokacinki na mintuna 2 ko 3 tunda naga kina saurin) wannan zai sa ta fahimci cewa da mutum mai mutunci take tsaye ba dan tasha ba.

 

4:Ka saukar da muryarka kasa kasa, a lokacin da kake mata magana kuma cikin girmamawa.

 

5: Kamin ka tinkari macen da bata sanka ba ka tabbatar kayi shiga mai kyau yadda bazata raina ganinka ba. Tunda ba sanin ka tayi ba ko kai wanene ko Dan wanene, don haka shigar mutuncin da zaka yi shine zai karfafa mata gwaiwar tsayawa ta saurareka.

 

6: Kada kace zaka tsaya gaf da gaf da ita a lokacin da kuke magana, ka bata tazara tamkar kana kyamar kusantar ta. Hakan yakan tabbatar mata cewa da gaske ne kake magana bada wata manufa ta daban ka zo ba.

 

7: Idan kana magana da macen da baka santa ba batasanka ba a karon farko ka guji saka idanuwanka akan halittunta irinsu nonuwanta idan mai yalwan kirjice, ko kuma kugunta idan mai girman kuturice ita.
Kana magana ne kana hada Idanuwa da ita sannan kuma kana maida kanka kasa bayan kun hada Idanuwa, a hakan za a yi hira.

 

8: Kada ka kuskura ka jata da hira mai tsawo yadda har zata gaji tace maka zata tafi. Kayi magana da ita a takaice koda kuwa ka fahimci tana jin dadin hiran taka ka katsai ka sallameta.

 

9:Kada ka dameta da yawan tambayoyin da kasan bazata so amsasu nan take ba. Saurin tambayar lambar waya ga macen da bata sanka ba yanada hadari. Haka kuma kokarin sani ko tana da manema a wannan tsayuwan duk ba tambayoyi bane da suka dace.

Abu mafi dacewa shine neman izzinin ganinta a mutunce a gidansu ko kuma inda take ganin zata baka dama tunda wannan shine farkon haduwar taku. Tare da kokarin sanin inda take son ku hadun.

Wadannan sune abu masu mahimmanci a haduwarku ta farko da macen da bakusan juna ba.

 

10: Kada ka sake ku rabu da mace ko wacce iri ce ba ka yaba da kyaunta da kwalliyar ta ba. Haka nan idan wani salon daurin dankwali ko dinki tayi ka kambamasu ka yabamusu ka nuna mata wannan shine karon farkon da ka taba ganin wata mace da shi.

Irin wadannan kalaman sunfi komai a wajen mace kuma sune zasu tsaya a kwakwalunta bayan ta tafi duk abunda ka fadamata kamin wannan kalmar duk zata manta dasu sai wannan daga zugata dasu.

#tsagayarmalamtonga 
#sirrinrikemiji   
Allah bada sa'a.

Post a Comment

0 Comments