SUNNONIN SALLAH GUDA 35.
Sunnoni a sallah su ne abubuwan da idan mutum ya yi su a sallah akwai ƙarin lada, amma idan an bar su sallah ba ta ɓaci ba.
1. Ɗaga hannaye yayin kabarbari daidai da kafaɗa ko daidai da kunnuwa.Yin su sunna ne a sallah, saboda hadisin Malik Ɗan Huwairis (رضي الله عنه) cewa Annabi ﷺ yana ɗaga hannayensa a cikin sallah. ()
2. Ɗora hannun dama a kan na hagu a kan ƙirji saboda hadisin Wa’il Bn Hujrin (رضي الله عنه) da hadisin Sahal (رضي الله عنه) da sauran hadisan Annabi ﷺ. Wannan dalilin ne ya sa malamai suka sa shi a cikin sunnoni saboda ko da mutum bai yi ba, sallarsa ta yi amma idan ya yi, ya sami lada.
3. Kallon inda mutum zai yi sujjada. An ruwaito wannan daga sama da mutum (10) kamar yadda ya zo a Sunanul Kubra na Imamul Baihaqi da Almustadrak na Imamul Hakim.
4. Addu’ar buɗe sallah (du’aul istiftahi) kamar yadda ya zo a hadisin Abu Hurairah (رضي الله عنه). Kamar haka:
((اللَّهُمَّ بَاعِدْ بَيْنِي وَبَيْنَ خَطَايَايَ كَمَا بَاعَدْتَ بَيْنَ الْمَشْرِقِ وَالْمَغْرِبِ، اللَّهُمَّ نَقِّنِي مِنْ خَطَايَايَ كَمَا يُنَقَّى الثَّوْبُ الْأَبْيَضُ مِنَ الدَّنَسِ، اللَّهُمَّ اغْسِلْني مِنْ خَطَايَايَ، بِالثَّلْجِ وَالْماءِ وَالْبَرَدِ )) ().
5 Neman tsarin Allah ﷻ daga shaiɗan saboda hadisin Abi Sa’idil Khudri (رضي الله عنه) wanda Abu Dawud da Tirmizi suka rawaito.
6. Yin Basmalah saboda hadisin Anas (رضي الله عنه) da Imamu Ahmad da Nasa’i suka ruwaito.
7. Faɗar Amin bayan karatun Fatiha wanda mutum zai bayyana a inda ake karatu a fili, ya ɓoye a inda ake ɓoyewa, kamar yadda ya zo a hadisin Abi Huraira (رضي الله عنه) wanda idan liman ya ce, Amin shi ma ya ce amin, za a gafarta masa abin da ya wuce a rayuwarsa na laifuka. ()
8.Karatun sura bayan Fatiha a raka’o’in farko saboda hadisin Samuratu Bn Jundubin (رضي الله عنه). ()
9. Bayyana karatu a wurin da ake bayyanawa, wanda ya zo a hadisin Zubairu Bin Muɗ’im (رضي الله عنه).
10. Asirtawa a cikin sallar da ake asirta karatu wanda ya zo a hadisin Kabbab Bn Aratti (رضي الله عنه) cewa sun kasance suna gane karatun sallar Annabi ﷺ a Azahar da La’asar ta hanyar yadda gemunsa yake motsi. ()
11. Ɗan tsayawa bayan an gama Fatiha ko kuma kafin a yi ruku’u, saboda hadisin da aka ruwaito daga Samura.
12. Buɗa hannaye a kan gwiwoyi yayin ruku’u, domin kammala ruku’u, da daidaita gadon bayansa saboda hadisin Rifa’ata Bin Rafi’i (رضي الله عنه) da hadisin Wabisa Bin Ma’abad (رضي الله عنه).. ()
13. Nisanta hannaye daga kwiɓi lokacin da mutum ya yi ruku’u, saboda hadisin Abu Humaid Assa’idy (رضي الله عنه). ()
14. Abin da mutum zai ƙara na tasbihi a cikin ruku’u ko sujjada, kamar yadda ya zo a hadisin Huzaifatul Yamani (رضي الله عنه).
15. Abin da za a ƙara na neman gafarar Allah ﷻ a cikin sujjada, kamar yadda ya zo a hadisin Huzaifa (رضي الله عنه). ()
16. Sauke gwiwoyi kafin hannaye a cikin sujjada da kuma ɗaga hannaye kafin gwiwoyi a cikin tsayuwa saboda hadisin Wa’il Bin Hajir (رضي الله عنه).
17. Haɗe ‘yanyatsun hannaye yayin kabbara.
18. Buɗe ‘yanyatsun ƙafa a cikin sujjada kamar yadda ya zo a hadisin Abu Humaid (رضي الله عنه).
19. Fuskantar gabas da ‘yanyatsun hannu da na ƙafa kafin sujjada, kamar yadda ya zo a hadisin Abu Humaid Assa’idy (رضي الله عنه).
20. Nisanta damatsa daga kwiɓi lokacin sujjada kamar yadda ya zo a hadisin Abdullahi Ɗan Buhaina (رضي الله عنه).
21. Nisanta ciki daga cinya da cinya daga ƙwauri kamar yadda ya zo a hadisin Abu Humaid (رضي الله عنه).
22. Sanya hannaye daidai da kafaɗa ko kunne, lokacin sujjada kamar yadda ya zo a hadisin Abu Humaid (رضي الله عنه) da hadisin Wa’il (رضي الله عنه) da na Barra’u (رضي الله عنه).
23. Matse duga-dugai na ƙafa da kafe su yayin sujjada kamar yadda ya zo a hadisin Nana A’ishah (رضي الله عنها).
24. Yawaita addu’a a cikin sujjada, kamar yadda ya zo a hadisin Abu Huraira (رضي الله عنه) da hadisin Abdullahi Ɗan Abbas (رضي الله عنه). ()
25. Shimfiɗa ƙafar hagu da kafe ta dama yayin zama tsakanin sujjada da sujjada, kamar yadda ya zo a hadisin Nana A’ishah (رضي الله عنها).
26. Ɗora hannun dama a ƙafar dama da hannun hagu a ƙafar hagu a lokacin zaman tahiya.
27. Sanya damatsa a kan cinya lokacin tahiya kamar yadda ya zo a hadisin Wa’il Ɗan Hujir (رضي الله عنه).
28. Damƙe ‘yanyatsu da kuma miƙe ɗanyatsan nuni a yi nuni da shi.
29. Yin zaman hutu (Jalsatul Istiraha) bayan sujjada ta biyu kafin shiga raka’a ta biyu, da kuma sujjada ta uku kafin shiga raka’a ta huɗu.
30. Zama a kan mazaunai a tahiyar ƙarshe kamar yadda ya zo a hadisin Abu Humaid Assa’idy (رضي الله عنه). ()
31. Yin salati a tahiyar farko.
32. Addua’ar neman tsari da abubuwa guda huɗu kamar haka:
a. Azabar qabari.
b. Azabar Jahannama.
c. Fitinar rayuwa da mutuwa.
d. Fitinar Dujal. Kamar haka:
((اللَّهُــمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنْ عَذَابِ الْقَبْرِ، وَمِنْ عَذَابِ جَهَنَّمَ، وَمِنْ فِتْنَةِ الْمَحْيَا وَالْمَمَاتِ، وَمِنْ شَرِّ فِتْنَةِ الْمَسِيحِ الدَّجَّالِ)) ()
33. Damantawa da kuma haguntawa lokacin sallama, kamar yadda ya zo a hadisin Amr Ɗan Sa’ad (رضي الله عنه) () daga mahaifinsa Sa’ad (رضي الله عنه).
Idan an yi sallama a tsaya sai an yi astagfirullah sau uku ga kowa,
34. Sannan a juya a kalli jama’a.
35. Y azkar na bayan salla,
Za mu ci gaba insha Allah.
0 Comments