LITTAFIN FIQHU DARASI NA 24



WAJIBAN SALLAH

Wajiban sallah guda takwas ne waɗanda sallah take ɓaci idan an bar su, amma idan da mantuwa aka bar su, mutum zai iya yin sujjada a maimakon su.
1. Dukkan kabbarar da ba kabbarar harama ba. Ko da mutum ya bar dukkan kabarbari zai iya yin sujjada a maimakon su, saboda hadisin Anas (رضي الله عنه) da yake cewa, “An sanya limami domin a yi koyi da shi. Idan ya yi kabbara, ku yi kabbara.” ()

2. Faɗar (سُبْحَانَ رَبِّيَ العَظِيمِ) sau uku a cikin ruku’u, saboda hadisin Huzaifa (رضي الله عنه) da yake cewa, Annabi ﷺ yana cewa, (سُبْحَانَ رَبِّيَ العَظِيمِ) a cikin ruku’u. Kuma ya zo a cikin hadisin da Imamu Muslim ya ruwaito.
Shi ruku’u, ku girmama Allah ﷻ a cikinsa . ()
3.Faɗar Sami Allahu liman Hamidahu ga liman da mai sallah shi kaɗai. Saboda hadisin Abu Huraira (رضي الله عنه) Manzon Allah ﷺ idan ya ɗago daga ruku’u gadon bayansa ya tsaya cak sai ya ce, (سمع الله لمن حمده). () 

4.Faɗin Rabbana Walakal Hamdu ga mamu da mai sallah shi kaɗai. Shi ma liman zai faɗa saboda hadisin Abu Hurairah (رضي الله عنه) ya ce, Annabi ﷺ yana cewa: “Rabbana walakal hamdu.” Bayan ya ɗago ya tsaya (yayin ɗagowa) sai ya ce, “Sami’allahu liman hamidahu.” Idan ya tsaya sai ya ce, “Rabbana walakal hamdu.” Su kuma mamu saboda hadisin Anas (رضي الله عنه) inda yake cewa idan liman ya ce, Sami’allahu liman hamidahu, ku ce: Rabbana Walakal hamdu.

5.Faɗar Subhana Rabbiyal A’ala, sau uku a cikin sujjada. Shi ma saboda hadisin Huzaifa (رضي الله عنه) Sannan ya yi sujjada ya ce, (سُبْحَانَ رَبِّيَ الْأَعْلَى). () 

6. Faɗar Rabbig gifirliy (sau 2). Saboda hadisin Huzaifa da yake cewa Annabi ﷺ yana cewa: 
((رَبِّ اغْفِرْ لِي، رَبِّ اغْفِرْ لِي)) ()  
 Ma’ana: “Ya Ubangiji ka gafarta min (sau 2) tsakanin sujjada da sujjada.

7. Yin tahiya ta farko, saboda hadisin Abdullahi Ɗan Mas’ud (رضي الله عنه) da yake cewa: Manzon Allah ﷺ ya koya mana idan mun zauna a raka’a ta biyu mu ce:

((التَّحِيَّاتُ لِلَّهِ، وَالصَّلَواتُ، وَالطَّيِّباتُ، السَّلاَمُ عَلَيْكَ أَيُّهَا النَّبِيُّ وَرَحْمَةُ اللَّهِ وَبَرَكَاتُهُ، السَّلاَمُ عَلَيْنَا وَعَلَى عِبَادِ اللَّهِ الصَّالِحِينَ. أَشْهَدُ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلاَّاللَّهُ وَأَشْهَدُ أَنَّ مُحَمَّداًعَبْدُهُ وَرَسولُهُ)) () 
Da kuma hadisin Abdullahi Xan Buhaina (رضي الله عنه) da yake cewa Manzon Allah ﷺ ya yi sallah raka’a biyu sai ya miƙe bai zauna ba, mutane suka miƙe tare da shi da ya ƙare sallar muna jiran sallamarsa, sai ya yi sujjada guda biyu daga zaune sannan ya yi sallama. () Wannan sujjadar ita ce ta zama abakacin wannan zaman da bai yi ba.
8. Zama domin yin tahiyar farko saboda hadisin Abdullahi Ɗan Buhaina (رضي الله عنه) yake cewa ya tashi daga raka’a ta biyu akwai zama a kansa. Lokacin da ya cika sallarsa, sai ya yi sujjada guda biyu kafin ya yi sallama. () 
Waɗannan abubuwa guda takwas su ne waɗanda idan an bar su ake yin sujjada ƙab’li ko sujjada ba’adi. Kamar yadda muka ce, waɗancan guda goma sha biyu su ƙab’li ko ba’adi ba ta tsayawa a matsayinsu. Dole sai an zo da su.
Za muci gaba insha Allah.

Post a Comment

0 Comments