🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍
Saurin inzali ko saurin release yaren da wasu suka fi fahimta matsalace da mutane masu yawa ke fama da ita cikin Maza, illa iyaka kurum mutane kanji nauyi ko kunyar bayyanata ko zuwa asibiti don neman magani wanda hakan kuskure ne.... Hasali ma wasu kanga kamar wannan ba matsalar da za'a jewa asibiti bace wanda kuma matsalar hakika ta asibiti ce.
________________________________________
MATASHIYA KAFIN MU SHIGA CIKIN BAYANIN LARURAR
Kamar ko yaushe nakan jaddada cewa inaso mutanen mu Mata da Maza ku cire wani gurbataccen tunani da finafinai na batsa, rubuce-rubuce na batsa da littattafan Novels da suka kunshi batsa suka riga suka dasa muku a kwakwale da zuciyoyinku da sunan ana koyar da yadda ake Jima'i, Hanyar da za'a bi agamsar da maigida, Salon kwanciya da sauran labarai da hankalin mai hankali bazai daukesu ba saide shasha.
Dole ne nai Magana kansu domin ta irin wadancan hanyoyi ko groups-group da ake tattauna irin wadancan abubuwa faduwar wasu Mazan da rainin wasu Matan ga Mazaje ke samo asali, Domin nan ne arubuce zakaji bayanin wane ya kwanta da wance akalla saida ya shafe minti 30 ko 40 jikin Mace, kuma bayan wai yai release nan da nan ya kuma kamota yaci gaba da kaza da kaza, nan suka kuma release atare, ya kara komata aka cigaba da kaza.... akarshe de sai kaji ana nunawa masu karantun cewa namiji yai release sau 3 zuwa 5, wanda kuma saida suka shafe sama da awa guda ko awoyi 2 suna jima'i.
Wanda a hankalce kuma a gaskiyance sam-wallahi ba irin wannan jima'in cikin jinsin mutane kaf duniya.
Hakama ko videon batsa nasha fadamuku karyans duk ba gaskiya bane wannan jima'in wasa da hankakinku ake, ya kamata kusan haka saboda yanzu yara ne ake aurar dasu cikin Mata wadanda idonsu tuni ya bude da irin wadannan zantuttukan batsar da ganinsu saboda zasu zuba idone suna tsammanin hakan daga Maigida wanda zarar abunda suka haddato suka ga bata faruwa sai'su fara tunanin Miji baida lafiya, Kan aje ko ina sai kaga anfara tura tambayoyi kaza da kaza ana dorawa miji matsalar da baida ita sam, ko neman fara mugun tunanin yin mugun aiki na cin amana wanda a zahirin gaskiya Mazajenku da yawa lafiya kalau suke saide ďan abunda ba'a rasa ba na rashin iya wasa yadda zakuke samun gamsuwa atare.
Babban misali shine ga masu amfani da wayar hannu ta salula shin kun ta6a ganin kun bude waya kurum kai tsaye ta hau aiki daga budewa? Bazai yiwu ba dole saika jira tayi loading ta gama boating wato ta farko tukun sannan sai kaga ta nuna welcome ta zamo ready. Musamman ma in laptop ce ka bude saima kai refresh dinta bayan ta gama boating inkanaso tai aiki yadda ya dace.
To haka ma jikin mutum bazaka taba farkowa bacci ba kurum ka fita da gudu, dole sai ka tashi zaune, wani ma yai miqa, sannan aji jiki ya fara warwarewa.
Toh haka ma jima'i yake bayan anyi release na farko komi lafiyarka akwai abunda ake kira refractory period da saika jira ka jikinka ya qara tattaro sha'awa, bazai yiwu kana gama release ka komawa Mace ba komi lafiyarka dole sai ka jira jikinka ya kara tariya ya tattaro abunda ya rage na daga sauran sha'awarka.
Sannan wannan refractory period ya bambanta wani bai wuce minti 15 zai iya komawa musamman inya tara sha'awa da yawa kila ya dau kwanaki baya gari, wani kuma minti 30, wani sai bayan awa 1, wani awa 3 wani awa 12 wani kuma shikenan sai gobe ko jibi, kuma hakan bai nuna bashi lafiya ya danganta da halittarsa,
Duk da eh akan samu masu larura wadanda kila abaya ba haja suke ba amma yanzu ana ganin matsala musamman idan maigida yana fama da ciwon sugar kuma musamman ace ya fara manyanta dole wannan matansu sai hakuri domin ciwon bai barin su iya rike erection sosai koma jin sha'awar tun ma ace mutum me sake da magani ne dama.
Wannan shine hannunka mai sanda ga kowa, duk labaran nan da kuke karantawa na batsa da kallon finafinan batsa masu tsayi da gajeru karya ce kuma mafi illa domin zai iya sa kirasa Jin dadin aurenki.
________________________________________
SHIN DUK SAURIN KAWOWA NE - SAURIN INZALI ?
Kamar yadda zakuji akasa a ilmance ya kamata kusani ba duk saurin release ke nuna rashin cikakkiyar lafiyar jima'i ba domin zubin halittun mu sun bambanta da juna kuma suna da tasiri Kän haka matukar de mutum ba wata sananniyar matsala yasan yana dauke da ita ba, Musamman a masu sabon aure, yai wuri daga aurenka sati 1 ko 2 ka yankewa kanka hukunci.
________________________________________
SHIN YA JIMA'IN MA YAKE NE A ILMANCE
Yawan jima'i na cutar da jiki, don haka tazarar kwana 3 kan zama abu na daidai, domin matukar ana samun tazarar awa 72 kwana 3 shi kansa sinadarin sperm din zai zamto mai karsashi da lafiyar samar da ciki nan da nan bawai jima'i ace kullum kullum ba.
■ A bisa binkicen masana Jima'i kansa kan fara zama jima'i ne daga zarar ansami sekons talatin da uku gaban Namiji na cikin farjin Mace.
■ Mafi kankantar tsayin jima'i shine wanda yake karewa a iya minti biyu da shigar azzakari farji, banda batun wasanni
■ Hakanan Matsakaicin Jima'i Kuma abun gamsuwa shine bai wuce mintuna 7 da sekons ashirin, wato haďe da wasanni dakan motsa sha'awa wanda basa wuce na mintuna biyu 2.... Saboda haka Inka cire minti 2 cikin 7 kaga saura minti 5 da sekons ashirin wanda wannan shine average na lokacin jima'i. Don haka kuskure ne ko ince ba daidai bane ma ace namijin dake jima'in minti biyar baida lafiya, normal ne.
■ Sai Mafi tsayin zango na Jima'i shine me daukar Minti 10 zuwa 30, hade da wasanni, wanda wannan shiyafi karanci duba da bakowa cikin mutane ke wannan ba hasali wasu hakan wata naqasace akwayoyin halittarsu da suka gada ta zame musu nasara ta fannin jima'i shine Har arika musu laqabi da HARIJIN NAMIJI, kamar yadda naqasa ke zamewa masu dimples abun ado da karin kyau afuska.
Yanzu tunda munji komi wanda yake normal game da jima'i to mu rankaya mu shiga cikin Matsalar da zamu tattauna kai.
___________________¹_____________________
CIKAKKEN BAYANI DANGANE DA SAURIN INZALIN
Saurin inzali larura ce dakan iya faruwa ga kowanne mutum, akuma ko wanñe irin shekaru basai tsoho, dattijo ko wani babban mutum ba, A'a har matasa da sabbin balaga musamman de tsakanin mutane yan shekaru 18 zuwa 59 aduniya, Hakanan kuma yana faruwa ga mutane masu fama da sanyin gaba wato rashin mikewar azzakari mussamman yan shekara 45 zuwa 65 aduniya wato ya zamto matsalar tai musu biyu kenan; ga rashin kuzarin azzakari gashi kuma kota tashin nan da nan mutum ke releasing.
Wato de kawowa batare da mutum yaso hakan ko ya kudurci hakan aransa ba ko batare da shi kansa tare da matar sunso hakan ba.
A zahiri babu wani takamaiman lokaci da dole sai namiji yakai yana jima'i kafin yai release sannan za ace lafiyarsa kalau. Domin lokutan jima'i sun bambanta. Amma de tabbas yana daga larura ua zamto kana inzali tun kafin ma ka shigi mace ko kuma kasa da minti 1 bayan ka fara jima'i. Abune me wuya bayan kai inzali ace ka iya cigaba da jima'i ko tattaba macen ta yadda zata ji dadin jima'in bazai yiwu ba domin tamkar gini ne wanda ginshikinsa ya rushe, wanda hakan zaisa abokiyar rayuwartaka rashin samun jindadin da jikinta ya shirya karba domin ka gaza tun ba'a je ko ina ba.
Hakanan saurin inzalin dake faruwa kafin ma mutum ya gama shigar da azzakarinsa gaban Mace kansa yana jawo rashin haihuwa domin samun ciki ba abune mai yiwuwa ba domin zirar da maniyyin yake a inda bazai iya kaiwa ga abakin mahaifar mace ba ballantana ya shiga ciki, shiko farji kwai acid don haka inka zubar da maniyyi iya nan lalacewa zai ya zubo waje, shyasa ko a wanda suke iya zubawa mace maniyyi can cikin farji abakin mahaifa za'aga ragowar da bai shiga ba ya zama kalar ruwa ya ziraro yana digowa daga farjin macen.
Wannan matsalar ta saurin inzali wasu tun farkon fara jima'in su haka suke samun kansuz wasu kuma.da ba hakan bane sai daga baya ta samesu musamman a mazaje masu larurar ciwon suga, su hatta mikewar azzakarin ma kan zama wahala, shyasa matansu saide hakuri. Amma ga wanda ya tashi ya nemi magani toh ana samun sassauci.
____________________²____________________
ABA-BEN DAKAN JAWO LARURAR SAURIN INZALI
1- Matsalar auratayya (inya zamto magana atsakanin mata da miji ba dadi, bawata jituwa, haka zalika suna da bambancin sha'awa ko yanayin jima'i) domin kila shi akwai yanayin kwanciyar dake sashi saurin kawowa yayi-yayi matar take canza post taki saboda wulakancinta ko taurin kai.
2- Larura agame da aboki ko abokiyar rayuwar musamman intana kuka da zafi yayin saduwa ko kuma kai me jima'in kana fuskantar ciwon kirji, ko ciwon kai adukkan sanda kazo jima'in dom haka kana fargabar kada ka yanke jiki ka fadi ko ka mutu.
3- Halayyar nan ta istimna'i wato masturbation tun ashekarun farkon balaga musamman a wanda yana yinsa kuma yana fargabar cewa za'a iya shigo a kamasa yanayi don haka cin fargaba yakeyi.
4- Tarihin cin zarafi daga iyaye ko wani na kusa da mutum tun baida wayau sosai, domin wani abun saide ai sha'ani ba Mata bane ke fuskantar barna daga iyaye ko yan uwa na jini ko dangi ba
5- Wani binkice da akai na hoton kwakwalwa a mutanen dake fuskantar saurin inzali akai-akai shekara da shekaru ya nuna akwai matsalar tangardar ga signals din kai sakonni na kwakwalwarsu wanda yake baiwa sashin dake sarrafa inzali wato parasympathetic tangardar kasa rike inzalin inya yunkuro.
6- Haka zalika dalilin wani magani da muke sha na wata larurara musamman da ya shafi kwakwalwa wadda kila bai lura ya fahimci hakan kesa masa matsalar ba, ko kuma wanda ya bashin ba wani wanda yasan magani bane don haka shi baya tunanin wannan maganin ne domin yana ganin ai likitane ya basa. Ko kuma ma kila wani maganin gargajiya dake sakar da jiki shima yana iya haddasa hakan.
____________________³____________________
SAI DALILAI MASU MOTSA RAI MA KANYI TASIRI [EMOTIONAL ISSUES]
Kamar;
1. Matsananciyar damuwa dake damun mutum dalilin wasu al'amura na rayuwa ko kasuwanci, ko asara da yayi ko yake hasashen zai iyayi.
2. Halin Matsi da takura wato stress, walau dalilin aiki ba hutu, ko tsananin ayyuka, mutum ne da ko yaushe busy busy busy ba hutu a alamuransa
3. Zargin kai da yawan tunane-tunane akan wani abu da ya riga ya faru dashi, ko ya faru da waninsa, tare da rike abun arai.
4. Matsalar auratayya tsakaninka da matar ya zamto zaman bawani dadi kurum aranka kanajin zaman hakuri kake da ita, ko kuma matan biyune daya can ke cazama kai da rabama kan ýaýa
5. Matsalar kwakwalwa abunda ya kunshi; kamar rashin ganin girman kai tare da raina kai ko raina zubin halittarsa inya kalli matar, wato ya zamto har yana jin kunyar kansa, ko fuskantar al'amari na fyade wato ko wani ya rika masa wasa da azzakari yana yaro wanda hakan har yanzu yake damunsa kuma yake tunawa inyazo jima'i,
6. Fargaba tare da jin cewa ko ya zata kasance shi karon farkonsa kenan saninsa agame da jima'i kadan ne gashi yana yawan jin korafi akan saurin kawowa wannan tunanin ma na haddasa saurin inzali
7. Tunani da sawa rai cewa zanfa iya fuskantar saurin inzali musamman zuwa wajen iyalin da wannan tunanin shima na taka rawa.
____________________⁴____________________
A ILMANCE TAYA LIKITOCI KE TABBATAR DA LALLAI MUTUM NADA MATSALAR
Bawai kurum don kazo ga likita kace likita ina fuskantar matsalar saurin kawowa ba wani bun kafin minti 1 bane kurum likita zai ce ok na fahimta ai kaza da kaza za'ai. A'a akwai wasu ka'idoji da ake dubawa agani sai mutum ya cikasu galibi sannan ta tabbata.
1. Sharradi na farko: Ya zamto akalla cikin adadin saduwarku kimanin kaso 75 zuwa 100% wato kusan ko yaushe cikin minti 1 da fara penetration kake kawowa ko kuwa kana kawowa tun kafin ka kudurci hakan da kanka, kotun kafin ma ka shigeta.
2. Sharadi na biyu ya zamto wancan abunda na fada a sharadi na farko akalla ka dauki watanni shida zuwa sama ahaka yana faruwa akai akai.
3. Sharadi na uku ya zamto wancan sharradin na farko yana matukar sa maka damuwa, kunci ko matsananciyar damuwa kai akaran kanka.
4. Sharadi na hudu shine ya zamto wancan sharadin na farko anrasa gano dalilin dake sanya faruwarsa walau wata cuta ko ciwo irin na sugar, ko kuwa dalilin wani magani, kuma hakan yakai ga fara sanya samun sabani tsakanin Mata da Miji.
_________________________________________
Wadannan sune sharruda 4 da duk wanda yace yana fuskantar matsalar sai anmasa screening kansu. Don haka ka duba kagani shin kana fuskantar dukkansu ko a'ah kafin ka tuhumi kanka da matsalar. Musamman sabbin aure karkuima kanku hukunci tukun ku bari sai kun wuce wata 6 ahaka tukun, domin yanzu farkone shauki da zumudi akai akai kana iya kake kawowa, amma inkukai lebur da juna zuwa wata 2 ko 3 nan gaba toh sannan ne zaka fara fahimtar gaskiyar kanka.
____________________⁵____________________
MATAKAN TSANANIN LARURAR SAURIN INZALI
Tana da matakai uku; walau mild, moderate ko severe wato daga me dama-dama zuwa me tsanani.
■ MAFI SAUKI [MILD]
Shine; wanda ke faruwa tsakanin sekons 30 zuwa Minti 1 na agogo da shigar mutum jikin Macen ya fara jima'i (30 seconds to 1 minute of vaginal penetration)
■ MA TSAKAICI [MODERATE]
Shine; Wanda ke faruwa sekons 15 zuwa sekons 30 da fara jima'i (15-30 seconds of vaginal penetration).
■ MAFI TSANANI [SEVERE]
Shine; wanda ke faruwa kafin ma afara jima'in, kila daga durkusa ya tunkari jikin matar saide kaji wuuuur kawai, ko kuma yakai ga shiga jikin Macen amma cikin sekons 14 da farawa shikenan tsur-tsur yai release komi ya kwanta.
____________________⁶____________________
A KARSHE SHAWARAR DA ZAN BAYAR ITACE
1}- Shi jima'i jiki ne ke yinsa amma zuciya ko ruhi ke sarrafa shi. Tashin farko karka kuskura ya zamto ka tun kari jima'i kana cikin damuwa ko fargaba kowacce iri ce. Daga nan kuma toh karka kuskura yayin da kaje ga iyalin kake hakaltowa cewa gaka kana jima'i aranka, gaka kana shafa guri kaza, ko kana kyawawan surar macen ta guri kaza da kaza... muddin kai haka baza ta6a iya jimawa kana jima'i ba. Sanda ka shigi jikin Macen toh kuma ka kauda hankalinka daga kallonta ko tunanin jima'in kake tunano can wani course ko subject a makaranta, ko kuma gonarka, ko wani kasuwanci daka ta6ayi kaci riba, ko alkhairin wani da ya tabama... kana ahalin jima'in. Muddin ka koyo detachment na ranka daga jima'in toh insha Allah zaka jima.
-------------------------------------------------------------------
2}- Abu na biyu Kamar yadda fiyayyen halitta yai umarni kashe fitila ko rage haskenta ya zamto bakwa iya ganin surar juna babban abune; kwai hikima ahakan, shi zaisa Macen ta rage kunya ta saki jiki dakai, kaima ka saki jiki da ita domin ko kun kalli juna ko kun ta6a juna ba ganin fuskarku ko surarku tar kuke ba, Hakan zai baka damar jimawa kana jima'i saboda wasu lokutan kallon surar kirjin mace kesa wasu mazan saurin inzali domin nono nada tasiri agaresu wasu shine ma ke jawosu ga Macen... Don haka amfani da DIM LIGHT nada matukar amfani hatta ga wanda bai fuskantar wannan matsalar.
-------------------------------------------------------------------
3}- Babu inda yakai kan azzakarin namiji jin ta6i wato sensitivity, duk fadin jikin mutum babu kamar wannan gurin, wasu sensitivity ne kesa su saurin kawowa tun ma ba ace suji hannun Macen akan azzakarinsu ba, don haka kana iya amfani da Latex condom wajen jima'i domin rage sensitvity zaisa ka jima. Ku jaraba kugani.
-------------------------------------------------------------------
4}- Maigida idan kunayin wasanni kafin jima'i wato foreplay kaďan to ka kara tsawon lokacin wasan hakan zaisa matarka ta daina jin cewa kana cutarta musamman ke Macen ki taimaka ki nusar dashi guraren da kikasan ina aka tatta6a ajikinki kinfi saurin rikicewa ki sami INZALI kan kari kinga hakan zai taimakesa ya hada miki da wannan, sai kiji kuna samun gamsuwa tare fiye daki zuba masa ido saidai shi yake taba ki walau kinajin dadin hakan ko bakyaji. In foreplay dinma matsala ne gunka kuna iya farawa alhalin duk da kaya ajikinku har kukai ga ciresu ahankali.
-------------------------------------------------------------------
5}- Galibin Mazaje yanzu cimar su abinci sukafi damuwa dashi, basa kallon kayan marmari matsayin abu na kullum kullum wanda ba haka bane, Ku sanni duk wani fruits ko vegetables da kukasan yana da natural sugar Ku jimanci cinsa hakan nada mahimmanci wajen rage saurin inzali wato kamar su (mangoro, lemon bawo, kankana, ayaba, abarba, Albasa a abinci sosai da sauransu).
-------------------------------------------------------------------
6}- Canza salon kwanciya, idan kan fama da wannan matsala bayan kun kashe hasken dakin toh ka koma kasa ya zamto Kaine akasa kwance ta baya akan gadon ka dora matar a samanka hakan kansa asami karin nisan zango kafin release saboda effect na gravity. Sannan ku lura da tsafta baki dayanku.
-------------------------------------------------------------------
7}- Kuke Motsa jiki, bazai yiwu ka lafke ba, sai gona, tuki in driver ne kai ko office shikenan baka da lokacin motsa jikinka. Kasani motsa jiki musamman abunda ya shafi kugunka zuwa kasa na kara lagiyar jima'i, Ku rika yin stamina boost exercise.
Wato motsa jiki ta hanyar karfafa tsokokin cinyarku da mara zuwa dubura. Ta hanyar zama akasa ka hade kafafunka guri daya ka dogare su saika sa hannuwa ka ruko kafafun kana kwanciya kana dagowa tamkar mai buildin din 6-packs kaita yin hakan har sai kaji ka fara gajiya koda sau 200 kullum kakeyi da Sit up. Hakama inkaje fitsari kake kokarin koyon rike fitsarin kana tsaka dayi, kana yi kana rikesa saika rika sawa ranka cewa kamar haka ya dace inkaji zakai release kakeyi, tph duk sanda kaji zaka kawo saika rika rikewa.
-------------------------------------------------------------------
8}- Idan kana fama da larurar yawan damuwa, tunani ko firgici bai kamata ka zauna ba ka sami lokaci kaje kaga babban likita musamman Psychiatricians zasu baka maganin da zakai amfani dashi na watanni, kuma kasan wani abu? galibi maganin depression din shine zai warkar ma da matsalar saurin inzalin kaji kayi ras tun kafin ma depression ya kau baki daya.
-------------------------------------------------------------------
9} In kaji zaka kawo saika tsaya ka cire tunanin tawohar abun aranka, ka jawo abar waje in kaji abun ya koma bayan ka jima saika koma hakan kansa adan sami Karin time kamar yadda nace inkana jima'i ka dena kawowa aranka cewa jima'i kake.
-------------------------------------------------------------------
10} A dena yawan tsarki da ruwan sanyi, akoma na dumi akai-akai saide inba asami hali ba.
-------------------------------------------------------------------
11} Idan Matsalar ba saurin kawowa bace kurum, harma da sanyi gaba, saikai ta jijjigata tare da bubbugawa kamar tsohuwar cocila, toh wannan matsalar ta erectile dysfunction din za'a magance farko tukun, hasalima ana maganceta galibi za'a anemi saurin inzalin arasa. Musamman anfi samun wannan a madu ciwon suga wajibi ne ku lura ku sanya ido kan sugar dinku saboda tana illata manya da kananun jijiyoyi wanda shiyasa azzakari ma take shafarsa domin bazai mike ba muddin babu isashshen jini hade da healthy nerve stimulation.
-------------------------------------------------------------------
12} Matasa masu kuruciya dake Masturbation kuima kanku fada ku dena, ayanzu zakuga abun kamar bakomi ba, bazakuji ba amma muddin kukaqi bari akace ka shafe shekara ko sama da haka kana aikata wannan halayyar jazaman sai lafiyarka ta ta6u. Zakaji haushin kanka gaba. Tun yanzu kuima tikka hanci don ku fita kunyar kanku.
-------------------------------------------------------------------
13} In duk wannan Matakan anbi abun yaci tira... Toh sai kazo kaga babban likita a bangaren PSYCHIATRIC, Ko Sex therapist. Akwai magunguna da ake ba mutum yake sha minti 30 zuwa awa 1 kafin saduwa zaike amfani dasu. Inbasu amshesa ba acanza masa wasu, har asami daidai shi.
Hakama akan bada topical desensitizing creams wato mai na shafawa a azzakarin da zai rage sensitivity din penis to za'a sami lafiya da ikon Allah.
-------------------------------------------------------------------
14} Muddin akai aiki da wadannan shawarwari toh za adace ballantana kuma in ba'aga canji ba toh in akaje akaba mutum magani yazo ya hada magani da kiyaye wadancan shawarwari, toh kuwa inde abun bai bar mutum ba toh gaskiya alamace ta Haka zaka mutu da larurar babu wani abu kuma da za'a iyama. Babu wani surgery da ayanzu akeyi don matsalar.
_______________________________________
Allah yasa mudace. Sannunku da karatu! Na jinjina muku. Ina alfahari daku baki daya.
✍🏼
[Ibrahim Y. YUSUF]
21062021
0 Comments