Nazari A Kan Cutar Kansar Mahaifa (Fibroid):






Fibroid

Fibroid; wata matsalace da take samuwa a cikin mahaifar mace, wato wani yanayi ne da wani curin nama yake fitowa kuma yana girma a mahaifar mace. Shi qululun naman mai cutar da lafiya yana danfare da wani sashen mahaifar (uterus) da wasu igiyoyinsa (tubes).

“Fibroid” wata kalmar ce ta turanci, domin sauqin furuci da Hausa, zamu cigaba da amfani da lafazin FAIBIROD. A cikin bayanin mu anan.

An kuma yi qiyasin cewa daga cikin mata 100, kashi 20 zuwa 50 na matan suna da cutar fibroid, musamman a shekarunsu na samun haihuwa – wato daga shekara 16 zuwa 50. Wani qiyasin kuma ya nuna cewar mata 30 zuwa 77 suna samun matsalar fibroid a lokacin da shekarunsu na samun haihuwa, wato lokacin quruciyar su ta balaga zuwa lokacin tsayawar al’adar mace saboda manyanta ko kuma tsufanta (menopause). Mafi yawan nau’in faibirod da ake samu baya da wata alaqa da ciwon-daji. Qululun ko qwallon irin wanda baya da nasaba da ciwon-daji ne. Yana iya fitiwo fiye da daya a mahaifa, kamar guda uku, hudu koma fiye da haka a wurare daban-daban cikin mahaifar.


 

 Alamomin cutar fabroid 

 

Wasu daga cikin alamomin na cutar sun hada da;

 
Zubar jinin al’ada mai yawa, ko na tsawon wani lokaci wanda bashi da alaqa da matsalar shafa na Jinnu, kamar yadda ya tabbata a cikin hadisi wanda fiyayyen halitta yayi mana bayani da cewa “wani bugu ne na shaidan.”
 
Zubar jini a baqin lokutta ko kuma tsakanin lokuttan haila
Ciwon qugu, saboda qululun yana danne wani sashen jiki cikin mahaifa
yawan fitsari
Ciwon baya daga qasan baya
Jin zafi /ciwo lokacin yin jima’i
Rashin jini saboda yawan zubar jini
Rashin jin dadi a mara, musamman saboda girman shi qululun a ciki
Basur maisa tsugunni a bayi saboda rashin fitar bahaya
Ciwon qafa
Girman ciki kamar mace tana da juna biyu amma ba juna biyu bane, musamman idan ita cutar faibirod din ta girma
Koma rashin ganin wasu ko daya daga cikin alamamomin da aka yi bayani
 

 Matsalolin da cutar fibroid take haifarwa 

 
1- Matsala wajen haihuwa/lokacin naquda

2- Matsala yayin fama da juna biyu

3- Matsalar rashin samun juna biyu / rashin daukar ciki ga mace saboda qululun ya toshe/taushe ko danne wani bangare na mahaifa

4-Yawan bari ko kuma zubewar CIKI.
 

Yana da matuqar muhimmanci mai jin daya ko fiye daga cikin wadannan matsalolin da taje asibiti domin bincike (test) ko tana da matsalar faibirod ko akasin haka. Idan kuma ta riga ta san ta kuma da cutar to sai ta nemi magani.

 
  Dalilan da ke haifar da matsalolin fabroid 

 
Har yanzu dai masana ilimi a fannin lafiya na ta yin qoqarin fahimtar cikakken dalilin daya sa ake samun fibroid. Sai dai kuma an gano cewa yawan sinadarin Estrogen (estarojin) a lokacin shekarun da mace ke iya samun haihuwa yana da nasaba da lokacin da mata ke samun matsalar faibirod. Daga shekara 16 zuwa 50 wannan shi ne lokacin da sinadarin yafi yawa a cikin jinin mace. Estrogen daya ne daga cikin manyan sinadaran jikin mace, wato Estrogen wani sinadari ne na jinsin mace dake tafiyar da girman jikin mace, rayuwar mahaifarta, da kuma yanayin halittarta daya shafi jima’i.

A lokacin balaga sinadarin yana taimakawa yasa nonuwa da gashin mara da hammata su fito, kuma shi ne yake sa sha’awa ko yawan sha’awa ga mace idan yayi yawa. A lokacin balaga qwayoyin mahaifa (obaries) za su fara samar da sinadarin. Za’a iya kiran shi Estrogen da suna “wani maqerin ‘yanmata ne ” , domin kuwa shi ne yake taimakawa wajen sauye-sauyen halittar jikin mace lokacin da take girma. A taqaice dai shi Estrogen shi ne sinadarin da faibirod suka dogara da shi domin samun qara yin girma a mahaifa, wato makamashin faibirod ne. Faibirod zai ci gaba da yin girma har sai lokacin da mace ta bar yin al’ada saboda girma (menopause), daga nan kuma sai ya fara qanqancewa.

 

Wasu daga cikin dalilan da za su iya sa mace ta kamu da cutar fabroid

 

1.Gado idan mahaifiya ko ƴar uwar ta taba samun fibroid zai iya yiwuwa mace ta samu, saboda gadon jini.

 

2.Jinsin baqar fata; Mutanen Afirka ko qasashen baqar fata, wato jinsin baqar fata su suka fi kowanne jinsin mata a duniya samun matsalar faibirod. Kuma matasa mata baqar fata sune suka fi samun matsalar a shekarunsu na matasa. A qasashen turawa, Indiya da China da sauran wasu qasashen, ba kasafaim ko kuma ba a cika samun matansu da ita matsalar ba.

 

3.Amfani da hanyoyin tsaida haihuwa qwayoyin tsaida haihuwa wani lokacin za su iya sa faibirod ta girma), qiba, qarancin sindarin bitamin D, yawan cin jan-nama, rashin cin abincin ganye da ‘ya’yan itatuwa, shan-giya da dai sauransu.

Hanyoyin asibiti na magance matsalar ta qunshi; aikin tiyata (surgery) domin cire shi qululun tare da cire wani bangare na mahaifa “uterus” [Hysterectomy] wanda zai hana samun haihuwa, hakanan ma wani nau’in aikin tiyatar [Myomectomy] wanda baya hana haihuwa a gaba, qwayoyin magani da wasu hanyoyin. Musamman ma idan ta girma aikin tiyata ne aka fi yi domin rabuwa da matsalar girman faibirod na iya kasancewa kamar girman wani dutse qarami ko qasa da haka, ko girman lemun tsami ko na zaqi, ko girman qwallo, girman jariri koma fiye da girman jariri, musamman idan ba’a cire shi ba ko magance sa. Wasu likitocin naganin idan faibirod ta kai girman inci 4 (4 inches/9-10 cm) to akwai buqatar ayi aikin tiyata domin a cire ta.

……………..

Post a Comment

0 Comments