LITTAFIN FIQHU (DARASI NA 23)



SHARUƊƊAN SALLAH

Sallah ba ta tabbata sai an yi ta da ilmi, kuma saboda Allah ﷻ. Akwai sharuɗɗa da malamai suka sanya kafin sallah ta zama ingatacciya, sai an cika su. Guda bakwai ne kamar haka:
1.Yin tsarki, alwala ko wanka ga wanda wankan ya wajaba a kansa kafin ya shiga sallah, domin gusar da babban kari ko ƙarami.
2. Tsarkake tufafi da wuri da jiki daga najasa kafin a shiga sallah.
3. A tabbatar kafin a fara sallah lokaci ya yi.
4. Sanya tufafi wanda za su rufe tsiraici. Mace dukkan jikinta al'aura ne, in banda fuska da tafin hannu. Shi kuma namiji ya yi shiga ta mutunci, yadda za ta rufe masa kafaɗunsa zuwa gwiwa domin zai gana da Allah ﷻ ne. Ya kamata ya zama cikin tsarki da tsafta, kada ya yi shiga wacce babu kamala da mutunci a cikinta.
5. Wajibi mai yin sallah ya tabbatar ya fuskanci Alqibla kafin ya tayar da sallah. Idan bai san inda Alƙibla take ba, sai ya yi tambaya, kuma ya dogara da amsar da aka ba shi. Idan ya yi sallah sai bayan ya gama, sai wani ya ce masa ba ka kalli Alqibla ba, sai ya sake idan lokaci bai fita ba. Wannan shi ne bambamci tsakanin wanda ya kaucewa Alqibla da mantuwa da kuma jahilci da wanda ya kaucewa Alqibla da ijtihadi. Wato mutum ne ya zo zai yi sallah, ga shi kuma bai gane inda Alƙibla take ba, kuma babu wani da zai nuna masa, sai ya yi iya ƙoƙarinsa, wajen gane alƙiblar. Bayan ya kalli inda yake tsammani ya yi sallah, sai daga ba ya ta bayyana a gare shi cewa, bai kalli Alƙiblar ba, babu komai a kansa. Amma idan yana cikin sallah sai wani ya zo ya ce masa ba inda yake kallo ba ne Alƙibla, sai kawai ya juya zuwa ga Alƙiblar ba tare da ya yanke sallarsa ba. Idan kuwa sai bayan ya ƙare sallar aka tunatar da shi, babu laifi a gare shi.
6. Yin niyya a cikin zuciya ta sallar da mutum zai yi. Niyya kala biyu ce: na ɗaya ya yi niyyar aikin da zai gabatar kamar sallah ko alwala: na biyu ya yi abin saboda Allah ﷻ kawai, ba domin yabo, ko neman girma, ko neman wani abun duniya ba. Manzon Allah ﷺ ya ce, “Kowanne aiki yana da niyya, kuma kowa akwai abin da ya niyyata.” Kamar yadda ya zo a hadisin Sayyidina Umar () (رضي الله عنه).
7. Ya yi sallah yadda Annabi ﷺ ya yi sallah da yadda ya koyar da ita, Saboda Manzon Allah ﷺ ya ce, “Ku yi sallah kamar yadda kuka ga ina yi.” () 

RUKUNNAN SALLAH
Rukuni shi ne wanda ba yadda za a yi a ɗauke maka shi; wajibi ne sai ka zo da shi kamar karatun Fatiha. Akwai wajibai waɗanda idan ba da gangan aka bar su ba, sujjada tana tsayawa a maimakonsu. Akwai sunnoni da sallah ba ta ɓaci idan an bar su da gangan ko da mantuwa. Akwai kuma abubuwan da za a yi a gyara su. Rukunai guda goma sha uku ne (12) Su ne:
1. Tsayuwa: Ana yin sallah ne a tsaye sai dai idan mutum ba shi da lafiya sai ya jingina. Idan ba zai iya tsayawa ba, ya jingina ba sai ya zauna ba tare da ya jingina ba. Idan ba zai iya ba sai ya zauna ya jingina. Idan ba zai iya ba sai ya kwanta. Ita kuma kwanciya zai yi ko da idonsa ne sai ya jujjuya shi ya yi nuni saboda faɗin Allah ﷻ:
﴿ حَافِظُواْ عَلَى الصَّلَوَاتِ وّقُومُواْ لِلَّهِ قَانِتِينَ ﴾ ()
Ma’ana: “Ku kiyaye salloli har da sallan nan mafi tsada (sallar la’asar) kuma ku tsayu ga Allah kuna masu yin shiru.”
Da kuma hadisin Manzon Allah ﷺ, ya ziyarci wani mutum da yake da lalurar basir, sai Manzon Allah ﷺ ya ce masa, ka yi sallah a tsaye, idan ba za ka iya ba ka zauna, idan ba za ka iya ba ka yi a kan kwiɓinka.

2. Kabbarar Harama: Saboda faɗin Annabi ﷺ, “Idan ka tashi za ka yi sallah ka yi kabbara.” Kabbarar harama ita ce ta biyu (2) bayan tsayuwa a cikin sallah. Kuma Annabi ﷺ ya ce, “Mabuɗin sallah shi ne tsarki, haramarta shi ne kabbara, fita daga sallah kuma shi ne sallama.” ()

3. Karatun Fatiha: Saboda Annabi ﷺ Ya ce: “Babu sallah ga wanda bai karanta Fatiha ba.”
Yin Ruku’u: Allah ﷻ Ya ce:
﴿ يَأَيُّهَا الَّذِينَ ءَامَنُواْ ارْكَعُواْ وَاسْجُدُواْ وَاعْبُدُواْ رَبَّكُمْ...﴾ ()
Ma’ana: “Ya ku masu imani ku yi ruku’u ku yi sujjada.” Da hadisin Abu Huraira (رضي الله عنه) wanda Annabi ﷺ yake koyawa mai munana sallarsa. Ya ce, “Sannan ka yi ruku’u har sai ka nutsu a cikin ruku’u.” ()

4. Ɗagowa daga ruku’u har sai mutum ya daidaita a tsaye, saboda hadisin mai munana sallarsa Annabi ﷺ ya ce masa, “Ka ɗago har sai ka daidaita a tsaye.”() 
5. Yin sujjada a kan gaɓɓai guda bakwai: Allah ﷻ Ya ce:
﴿ يَأَيُّهَا الَّذِينَ ءَامَنُواْ ارْكَعُواْ وَاسْجُدُواْ وَاعْبُدُواْ رَبَّكُمْ...﴾ ()
 Ma’ana: “Ya ku masu imani ku yi ruku’u ku yi sujjada.” 
Da kuma hadisin mai munana sallah inda Annabi ﷺ ya ce, “Ka yi sujjada har sai ka natsu a sujjada.” () Da hadisin Abdullahi Ɗan Abbas (رضي الله عنهما) Annabi ﷺ yana cewa, “An umarce ni da na yi sujjada a kan gaɓɓai guda bakwai.” () Ya nuna goshi da hanci da tafukan hannaye da gwiwoyi da tafukan ƙafa (dugadugai guda biyu).
6. Ɗagowa daga sujjada ta farko, 
7. Yin sujjada ta biyu kamar yadda aka yi ta farko.
7. Ɗagowa daga sujjada ta ɗaya da ta biyu. Annabi ﷺ ya ce da wanda yake wa gyaran sallah,“Ka ɗago har sai ka tabbata a zaune.” 
Zama a tsakanin sujjada da sujjada Shi ma ya zo a cikin hadisin Abu Huraira (رضي الله عنه), inda Annabi ﷺ ya ce: “Ka zauna har sai ka nutsu ka tabbatar ka zauna.”
8. Nutsuwa a cikin sallah da tara hankali.
9. Jeranta tsakanin rukunai.
10. Tahiyyar qarshe.
 12. Yin sallama daga sallah.

Post a Comment

0 Comments