BAYANI A KAN WANKA.
Wanka shi ne game dukkan jiki da ruwa tare da cuɗawa da niyya .
Musulunci addinin tsarki da tsafta da ado da kwalliya ne, Allah ﷻ Ya ce:
﴿ أِنَّ الله يُحِبُّ التَّوَّابِينَ وَيُحِبُّ المُتَطَهِّرِينَ ﴾ ()
Ma’ana: “Lallai Allah Yana son masu tuba da masu tsarki.”
Haka kuma Manzon Allah ﷺ ya ce: “Tsarki shi ne rabin imani.”
Ya ce, Allah ﷻ mai kyau ne, Yana son kyau.
Don haka, babu ƙazanta da dauɗa da datti a Musulunci. Kada wani ya ɗauka zama cikin najasa ko datti alama ce ta imani da son Allah ﷻ. Manzon Allah ﷺ Ya ce, “Haƙiƙa Allah ﷻ ba Ya duba zuwa ga surorinku da kamanninku, Yana duba ne zuwa ga zuciyoyinku da ayyukanku.” ()
Ana alwala da wanka idan za a gabatar da ibadar da ba a yin ta sai da tsarki. Mun gabatar da inda ake yin alwala.
SHARUDDAN WANKA
Sharuɗɗan wanka guda takwas ne. Su ne:
Musulunci.
Niyya.
Hankali.
Tantancewa.
Ruwa mai tsarki.
Gusar da duk abin da zai hana ruwa tava fatar mai wanka.
Ɗaukewar jinin haila.
Ɗaukewar jinin biqi kafin a yi wanka.
FARILLAN WANKA
Farillan wanka su ne:
Niyya a farkon wanka.
Game jiki da ruwa.
Gusar da dukkan abin da zai hana ruwa shiga jiki.
Wasu malamai suna saka shaƙa ruwa da facewa a cikin farillan wanka, kuma wajibi.
Idan mutum zai yi wanka ya nemi wajen da babu wanda zai ga al'aurarsa ko tsiraicinsa, in ba iyalinsa ba.
YADDA AKE WANKA
Yadda ake yin wankan janaba da ɗaukewar jinin haila da jinin biƙi, duka iri ɗaya ne, sai a niyya suka bambamta. Yadda ake wanka ya kasu kashi biyu:
Idan mutum zai yi wankan ibada ya sami ruwa mai tsarki mai tsarkakewa, kamar yadda ya gabata, sai ya yi bas’mala (ya ce, bismillahi) a farko. Sai ya wanke hannunsa sau uku, sai ya wanke gabansa, sai ya kuma ya wanke hannunsa, saboda da ƙazantar da ya taɓa, sai ya yi alwala yadda yake yin alwalar sallah, sai ya wanke kansa sau uku, ya zuba ruwa ya cuɗa ko’ina, ya tabbatar ruwa ya ratsa gashinsa ya tarar da fatar kansa. Daga nan sai ya wanke kafaɗarsa ta dama zuwa ƙafa, ya dawo ya wanke ta hagu zuwa ƙafarsa. Ya tabbatar ya wanke duk wasu wurare masu loko, kamar hammata da cibiya da matsematsi da bayan gwiwa da ƙarƙashin ƙafa da dunduniya da tsakanin `yanyatsun ƙafa da baya da wajen kaushi da faso, domin abin da ake buƙata a wajen wanka shi ne game jiki da ruwa. A tabbatar ko’ina ya sami ruwa tare da niyyar wanka. Idan wannan ya samu, wanka ya cika yadda ake buƙata.
Kalar wanka na biyu shi ne, mutum ya yi niyyar wanka kawai, ya dulmiya a cikin ruwa, ko ya shiga cikin kwamin wanka, ko ƙarƙashin shaya ko ruwan sama ko cikin kogi da dai sauransu. Ya cuɗa jikinsa, ko’ina ya sami ruwa shi kenan ya gama wanka domin an sami muhimman abubuwa guda biyu da suke tabbatar da ingancin wanka; su ne, niyya da kuma game jiki da ruwa.
* * * *
ABUBUWAN DA SUKE JAWO WANKA
Abubuwan da suke jawo a yi wankan ibada su ne:
1. Fitar maniyyi a cikin bacci, ko a farke, daga namiji ko mace, ta hanyar lafiya da jin daɗi, saboda hadisin da ya ce, “Idan ruwa ya fita a yi wanka.”() Wato idan ruwan maniyyi ya fita, a yi wankan janaba.
Idan mutum ya yi mafarki yana saduwa da mace, amma da ya farka babu alamar fitar maniyyi, babu wanka a kansa.
Idan mutum ya yi mafarki yana saduwa da mace, bayan ya farka sai ya ga maniyyi a jikinsa, wajibi ya yi wanka.
Idan ya tashi daga barci sai ya ga maniyyi a jikinsa, amma bai yi mafarkin saduwa ba, wajibi ya yi wanka, saboda samuwar maniyyi a tare da shi, wanda fitarsa ne yake jawo wanka.
Idan mutum ya ga maniyyi a jikin kayansa, amma bai tuna lokacin da ya yi mafarki ba, sai ya yi wanka ya rama sallar da ya yi daga lokacin da ya kwanta wannan baccin da ya yi mafarkin.
Saduwa tsakanin mace da namiji, ya shigar da gabansa a cikin gaban mace, wajibi su yi wanka ko da maniyyi bai fito ba, domin Manzon Allah ﷺ Ya ce, “Idan kaciya biyu suka haɗu wanka ya wajaba” () ko da maniyyi bai fito ba.
Idan mutum ya rungumi matarsa suka yi wasa kawai babu saduwa, kuma maniyyi bai fito ba, babu wanka a kansu, saboda rashin samun dalilan da suke jawowa a yi wanka guda biyu: fitar maniyyi ko shigar kaciyar namiji cikin farjin mace. Idan ba a sami xayan biyun ba, babu wanka.
Idan maniyyi ya fitowa mutum bayan ya yi wanka, wasu malamai suna ga babu buƙatar ya sake wanka, wankansa na farko ya isa. An ruwaito daga Zuhriy da Hasanul Basriy sun yi fatawa ga wanda maniyyi ya fito masa bayan ya gama wanka cewa babu buƙatar ya sake wanka. ()
Idan maniyyi ya fitowa mutum ta hanyar rashin lafiya, ko wata larura, ko aka yi masa wata allura domin a ɗauki maniyyi a jikinsa, duka wannan babu buqatar yin wanka, saboda rashin fitar maniyyi ta hanyar sha'awa.
Idan mutum ya ga wani abu a jikinsa, amma yana shakka maniyyi ne ko ba maniyyi ba ne sai ya shinshina. Idan ya sami yaqini ko zato mai qarfi cewa maniyyi ne, sai ya yi wanka domin ya fita daga kokwanto.
Haramun ne mutum ya sadu da matarsa tana cikin jinin al'ada ko jinin biqi, ko ya sadu da ita ta dubura, amma idan ya keta Shari'a ya yi, sai ya yi wanka, kuma ya yi nadama, ya yi kaffara, ya tuba.
Abin da yake jawo wanka shi ne ɗaukewar jinin al'ada. Idan mace ta gama jinin al'ada ta tabbatar ya ɗauke har ta ga alamar ɗaukewarsa, sai ta yi wanka kamar yadda ya gabata a baya a wankan ibada.
Shi ne jinin biƙi. Idan mace ta haihu, jinin da yake biyo baya ya ɗauke, sai ta yi wanka, kamar yadda ya gabata a wankan ibada.
Idan Allah ﷻ Ya arzuta mutum da shiga addinin Musulunci, ya wajaba ya yi wanka na ibada, kamar yadda ya gabata da niyyar ya shigo Musulunci. Saboda wani mutum () Ya musulunta, Manzon Allah ﷺ ya umarce shi ya yi wanka.()
Wankan ranar Juma'a, domin ya je sallah cikin tsarki da tsafta.
Idan mutum ya mutu a yi masa wanka kafin a binne shi, sai wanda Shari'a ta ce ba a yi musu wanka, kamar wanda ya yi shahada a filin daga fi sabil
Zamu ci gaba insha Allah
0 Comments